I

3.8K 271 7
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

I

✍️ Ayshatuuu

Kamar yadda kullum nake fada mishi yau ma haka na Kara maimaitawa cikin kunnuwan shi

" Wallahi! Kaji na rantse Babu wata Mata da zata juya ni a cikin gidannan! Yadda take jin aurar ta kayi Nima haka ka aureni, I've sense of belonging a cikin gidannan..."

Katse ni yayi saboda na lura ya gaji da jin maganganu na, Ina tunanin Bai San Haka nake ba tun asali, kilan da Bai aure ni ba

" Meye matsalar ki ne? Yanzun ni ban Isa nace ki bar Abu ki Bari ba kenan?"

Na kalleshi Ina sassauta abinda nake ji a zuciyata, yayi wani irin, abun tausayi nace

"Kuji wata magana? Me kace na daina ban daina ba? Kafi kowa sanin bani da matsala, ni bani da fitina Amma ni bana Bari, baza ayimin Abu na Bari yayi sliding haka kurum ba! Wallahi se na rama"

Zama yayi yana dafe kanshi, showing me his tiredness akan maganar da nake Yi. saboda Ina son shi, son da nake mishi ba kadan bane, it's immeasurable se naji ban jin dadin yanayin da yake ciki, Amma kuma bazan iya dauke kaina akan abubuwa da dama ba,inada tsoro, tsoron da nake kada Nima ayimin abinda akai yiwa uwata, bazan dauka ba. Shiyasa tun kafin ya aureni na fada Masa a zuciyata inada kullin kishiya, babban tanadi nayi Mata, saboda ni uwata ta Zama UWARGIDAN BAHAUSHE, Bata ji dadi a hannun kishiya ba, haka Nima bazan Bari ta faru akaina ba. Idan ta zauna lafiya Dani I'm a peaceful person idan ta nuna way round ni kuma Zan nuna Mata lallai Nima Yar yau ce.

Ganin har lokacin ina tsaye a kanshi bani da niyyar Zama yasa ya Mike ya Kama hannuna tareda Dan matsawa kadan, hakan yasa na kalleshi cikin idanu, da sauri na sunkuyar da kaina Ina tura baki nace

" Saboda kasan wannan shi ne rauni na shi ne zaka min hakan?"

Se yayi dariya kadan yace

" To ya zanyi? tunda kin koya rigima bani da wani solution kuma, for goodness sake ba Zaki barni na huta ba?"

Zama nayi gefen shi Ina tura mishi baki nace

" Ni na fada maka ka dauke kanka, kayi kamar baka gani ba.."

Bai ma barni na gama maganar ba ya hade bakin mu guri daya, seda muka nutsu na ture shi nace

" This is cheating!"

Ya Mike Yana wani irin murmushi yace

"Ko? Ai nasan idan ba hakan na Miki ba bakin ba zai rufu ba, kuma Naga kema you were submissive!"

Kaina na girgiza na barshi kwance bakin gadon na fita parlona, na Jima tsaye Ina kallon parlon ba tareda nasan tunanin me nake ba, hannun shi naji ya zagaye kuguna hakan yasa nayi firgigit na dube shi, da idanun shi yake tambayata akwai wani Abu se na girgiza kaina kawai.

"Ba wannan Safiyyar na sani ba, Safiyyar da na sani a FGGC was a cool girl, Amma duk kin Zama me hayaniya kema!"

Nayi murmushi, reminscising over the past memories da mukai tare, sure ba Haka nake da ba, Babu Wanda zaiyi tunanin Zan Zama Haka.

Wajen karfe Tara ya shigo part dina, Ina kwance a parlor na kammalla dukkan abinda ya kamata nayi, shi daya nake jira ya shigo mu kwanta, gefena ya zauna tareda Kama hannuna yace

" Sub ya Kare ne?"

Ya fada Yana kallon TV din, Ganin bana kallo, TV dinma a kashe. Kaina na girgiza na tashi na zauna nace

" Ko daya, ka manta I'm not a fan of movies"

Se yayi murmushi Yana gyada Kai tareda fadin

" To tashi muje mu kwanta!"

UWARGIDAN BAHAUSHEOù les histoires vivent. Découvrez maintenant