"Tunda ya fara maganar Baban Aziza yake kallonshi har ya gama, sannan shima yace Bawam Allah ai Aziza da bakintaa tace ni ba ubanta bane, sannan kuma tace man na manta da na taɓa haihuwar wata mai suna Aziza kuka ya fashe dashi ya cigaba da cewa yarinyar nan ta zaɓi wata gurba marar kyau nida yan'uwa ba yanda bamuyi da ita ba akan tabar wannan ƙazamar rayuwa amman tayi kunnan uwar shegu damu, kaga wannna har aure sai da na daura mashi da ita, ranar da aka daura masu aure a ranar ta gudu daga nan bamu sake ganinta ba, koda kuwa labarinta ban sake ji ba sai yau ku da kuka zo mana da labarinta, daman ai haka bariki take angama yayinta shine aka dawoman da ita ko? To wallahi bani ansarta taje ta cigaba da rayuwar da ta ga itace ta dace da ita."

"Dafashi wani police yayi sannan yace hakuri zakayi Alhaji dan yanzun haka Aziza bata bisa doron duniya, Allah S. T.W ya anshi rain Aziza dan kuwa yana hannunshi sai dai mai Aziza ta mutu ta hanyar da mai kyau ba dan kuwa a hotel ta mutu suna aikata *Zina* da wani wanda ba ma addininsu ɗaya ba, a haka rai yayi halinsa da akazo gyara room aka tadda gawarsu sai muka kira wannan bawan Allah ya nunani sanna ya cigaba da cewa munsa matarshi ce dan tayi saving din sunanshi da *Mijina* koda yazo yaga gawarta ya tsorata sosai kuma har yanzun bai daina kuka ba, yace mana baisan tana wannan harkar ba shi dai yana soyayya da ita suna shirin auren juna, sai yace mana ta taɓa ce mashi ita yar majoji ce, amman bai taba zuwa gidansu ba shine muka shigo majoji dan nemo gidansu yanzun haka gawarta ta hanya dan anraba gawar anba ancan nasu kuma mun bada address za'a kawo maku taku."

"Tashi tsaye Babansu yayi sannan yace inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah sarki Aziza tabbas kinyi mutuwar asara sai dai muna rokan Allah ya yafe maki nidai ko na yafe maki ƴata na yafe maki har abada inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah sarki Asiya Allah ya baiyanaman ke cikin aminci tabbas alhaƙin Asiya shine yake biyayarmu a gidan nan, alhakin marainiyar Allah shine yake biyayarmu Allah na tuba, tabbas na kasance uba marar kyautatama iyalansa, kallonshi muka fara yi sannam akace wacece Asiya? Ce mana yayi Asiya ɗiyarshi ce ta cikinshi mahaifiyarta ta rasu ta barta cikin matanshi suka matsa mata bata da gata sai su Aziza da suke da uwa a cikin gida ba soyayyar da bai nuna ma su Aziza ba da iyayensu amman banda Asiya da tazama baiwa a gidansu Aziza dan duk wani aikin bauta Asiya ce take yinshi lokacin da suna zaune a kunya chemist ɓarayi suka shigo gidansu nan sukayi ma Asiya fyaɗe yace mana yayi kuka a lokacin daga baya matanshi suka zugashi akan Asiya ta samu hanya tana bin maza tunda taga ɓarayi sunyi mata hanya, da bani yarda sai daga baya na fara yarda sai kuma ga ciki ya baiyana a jikin Asiya ni kuma ido ya rufe sai nace wajen iskanci ta samaishi dan daga yi mata fyaɗe rana ɗaya ciki ba zai shiga ba, da bakina da kaina na kori Asiya a gidana haka ta tafi tana kuka, ni kuma a lokacin ko a jikina dan gani nike ba zan yarda ba a haifa man shege a gidana ba, haka ta tafi muka cigaba da rayuwar mu cikin gidanmu muka manta da Asiya, bamu damu da wani hali take ciki ba sai ga Aziza ta bullo da halin bin maza na girgiza sosai tana level one a university ba faɗan da banyi mata ba, karshe na aure mata aure da Kamalu gashi nan ɗan ƙanenane amman sai ta gudu, bayan ta gudu kuma ƙanwarta ita kuma take neman mata😭, yanzun haka sana'arta kenan bin mata take dan itama ta tashi ta barman gidan tana zaman kanta, in kaiku karshe yanzun haka baki ɗaya yarana bana maijin magana daga mai shaye shaye sai mai yi ma ciki, yaran Amarya tane kawai masu ji su biyu ne suma ba wani girma sukayi ba sosai balle nasan ya nasu girma zai zo masu, inalillahi wa'inna'alaihirajiun 😭, wallahi Khadija sosai labarin Baban Aziza ya samu kuka muna cikin kukan akazo da gawar Aziza nan kuka ya zama sabo, haka aka gaya ma matan gida kamar anbusa isul haka unguwar ta kaure da rasuwarta haka muka hadu muka sallaci gawar Aziza muka rakata gidanta na gaskiya, bayan mutuwar da kwana uku nabar zuwa gidan su Aziza, kinji yanda karshen Aziza yazo Khadija dan Allah Khadija ki yafema Aziza na rokeki ki yafe mata dan al'farma Annabi Muhammad S. A. W."

Shiru nayi kawai ina hawaye dan har ga Allah naji mutuwar Aziza sosai, duk da ta bada gudumuwa wajen lalacewar rayuwata amman nasan harda laifina ba laifinta bane dan nice na bata fuska har ta sani a hanya, nayi mamaki da naji Aziza ƙanwar Aunty Asiya ce ji yayi shirun yayi yawa naji yace.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 30, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

A SANADIN SOYAYYAR MINTI Where stories live. Discover now