BIYYAYA

1.1K 83 0
                                    

*😥😥BIYAYYA😥😥*


~NA~

*muneera*

😘😘😘😘wowww comment din ku nasani naji ni ontop😂 kuna jijiga ni da comment din ku dan haka ga page guda na baku kuka kadai ☺se wanda kuka damar bawa

*Mmn Abdallah*
*Khadija marafa*
*Fatima st*
*Meelart sani*
*Maman faruq*
*Gimbiya Bilkisu muhmad*
*Aynah*
*Eesha baby*
*Ummu Aliyy*
*Rukayyat*🤣kanwar yusuf
*Sad baby*


*ohh nagode sosai da addu'oin ku gareni Allah ya biya muku bukatun ku Na alheri 💞💞*

*16💞17*

Faruk shi kadai yake ta tunani anya bawani abu ya faru da Ahlam din shi ba addua yayi tare da fadin Allah duk ma damuwar da take damunta ya rabbi ka yaye mata ita sanan ya ajiye hoton ya fada duniyar tunani
Ahlam kuwa ammi ce ta dauke ta tayi part din ta da ita ta kira doctor yazo ya duba ta, bacci me nauyin gasken yayi awon gaba da ita bayan ta farfado a hankali cikin nutsuwa sedai duk wanda yaganta yasan baa hayyacin ta take ba ta bude idon ta ba kowa a dakin tunani ta shigayi anya ba mafarki tayi ba Karewa dakin kallo tayi sanan ta tabbatar ba mafarki tayi ba , gyra kwnciyya tayi cikin kumar rai hawaye ma zubuwa daga idon ta , a fili take fadin lalai Yusuf ka bata min rayuwa tsakanina dakai sedai mu hadu a koton Allah nida ban taba sanin wanin da namiji ba a rayuwata ba Amma ka min wanan sharin lalai kiyayr taka ta wuce yarda nake zato amma akwai Allah ,ze wanki ni daga wanan mumunan zargin Tashi tayi ta shiga toilet ta dora Alwala ta tadda sallah takai kukanta wurin Ubangiji tana haka sega Ammi ta shigo da flaks a hanun ta abinci ne mai rai da lafiya ta mika mata amma ta girgiza kai tare da fadij Ammi na kema kin yarda zan aikata abinda Yusuf ya fada akanta dan tuni ta dena kiran shi da uncle Yusuf, Aa ahlam ko kowa ya yarda ni ban yarda ba kuma bazan taba yarda ba kinji Ahlam dina daure ki damu kici abinci, girgiza kai tayi alamar ta koshi Ammi da kanta ta bude abincin ta fara bata abaki befi chokali biyu tayi ba tace ta koshi



.Kafin wani lokaci kankani gaba daya unguwa ta dauka da abinda Ahlam tayi se cewa akeyi Albasa batayi halin ruwa ba domin duka gidan su itace ta fita zakka Se masu fadin Allah ya kyauta se kuma masu cewa Karyane sun san yarinya bazata aikata ba haka dai zancen ya gama yada unguwa kowa na tofa albarkancin bakinsa harda masu zaginta wanda duk bata san sunayi ba kuma duk wanan abin Yusuf ne Yaya habib kuwa yayi kuka har shidewa ya dingayi saboda kukan da yake gani yake duk rayuwar da Ahlam ta shiga shine sila ya cuci yarinya haka kawai da kanan shekarun ta Amma inshaa Allah shi ze gyra Kuskuren da yayi da kanshi amma tayaya ze gyra wanan mumunan batanci shikadai yaketa sake sake yana warwarewa can wata shawara tazo masa ya tashi ya taho gidan inda yayi dai dai da fitowar Ahlam daga part din Ammi Ameera kanwarta zata wuce ta dawo tace karuwa se sum sum da kai kamar mutuniyar kirki ta fada tana dariya hadeda taffa hannayenta guda biyu Ahlam bata kalle ta ba illa gigida kai da tayi ta wuce dakin maman ta tashiga sallama da tayi kawai ta iya amsa mata gaishe ta tayi ta kauda kanta gefe Kamar bata ganta ba mama ki yarda dani da sauri ta daka mata tsawa wanda Ahlam din seda ta tsorata a hankali hawaye mash zafi suka fara fitowa daga idon ta tana fadin mama ki yarda dani har zuciyar maman take jin yarda Ahlam take kuka amma ba yarda zatai Ahlam ta tafka kuskure dole ta nuna mata kuskuren ta, tashi Ahlam din tayi tana kuka ta fito tayi part din Ammi tana kuka .

Zaune yake gaban mahaifin nasu yana fadin Alhajin mu ka yarda da Ahlam ta koma makaranta dan Allah Alhajin mu bana son sakarci habibullah dake haka yake kiran shi tashi ka bani wuri wato na barta ta karasa lalacewa koo toh ban yarda ba nace, habib kuwa dan dukawa yayi yana fadin Tuba nake Alhajin mu Amma ka yarda dani domin ni zansa a dinga kaita ana dawo da ita habibullah ban yarda ba zaka iya tashi ka tafi, Tuba nake Alhajin mu a huta lafiya ya fadi yana mikewa ya fice Toh tayaya ze gyra kuskuren daya aikata part din Ammi ya shiga inda ya sami Ahlam a zaune ita kadai a palon ta cusa kanta tsakanin cinyoyin ta tana sauke ajiyar zuciya a hankali alamun shigowa taji tana daga kanta taga yaya habib da sauri tayi daki a guje ta barshi yana gigiza kai, duk yanda habib yaso yaga An bar ahlam ta cigaba da karatu Amma ina abu yaci tura gashi har ta gama idda duk da ita tasan batada wata iddar yusuf akanta


Wai faruk bazaka fito da mata kayi aure ba yaran kawayena duk ina kawo maka su Amma ka ki zabar ko daya daga cikin su ina ce nan har mata biyoka gidanan suna sonka Amma kaki ka fitar da mata wanan wace irin rayuwa ce Ahlam ce ka riga da ka rasata kuma bari kaji koda tanan ni bazam yarda ka aure ta ba tun yanzu kana nuna bamu isa dakai ba akanta bale ka aureta toh baze yuyu ba mahaifiyar faruk ce tsaye take ta masa fada kan yaki fitar da mata yayi Aure hakuri kawai ya bata tareda ficewa dai dai nan Asim abokin shi ya shigo yana kiram sunan sa faruk yana tamvayar shi lafiya nan Asim ke sanar dashi Abinda ke faruwa da Ahlam a zabure ya mike yana fadin karya ne karyane wallahi baze taba yuyuwa ba

*muneera*

dont forget to
#vote
#comment
#share

BIYAYYAWhere stories live. Discover now