BIYAYYA

1.1K 91 5
                                    

*😥😥BIYAYYA😥😥*

~NA~

*MUNEERA*

kuna ina ku matso kusa😉 mana yau page din nakune ku kadai se wanda kukaga damar bawa👇🏻

*SA'ADA M BALA*
*SHMMY💞*
*UMMU SUDAIS*
*MAMAN TWINS*
*MRS KAMAL*
*MISS XERKS*
*NUSAIBA*
*maman fukaihat*
*ph@lm@rt*
*momi*
Dama sauran duk kuna raina 💞💞💞

*14💞15*


Gaban ta taji ya kuma wata mumunar faduwa yayinda tasa kafarta cikin gidan tafiya take kanta a duke jikinta a sanyaye , zata shiga dakin kenan yaya habib ta gani yana fitowa daga dakin kallon ta yayi ya girgiza kai kamar kwala ta gani idon yaya habib amma meyasa shiga tayi gaba daya dakin anyi shiru Ammi da mama taga suna kuka tsugunawa tayi ta gaida su duka ba wanda ya amsa mata alhajin su ne ya dago yana fadin Ahlam abinda zaki min kenan tarbiyya da na baki kenan da wanan zaki saka min kwla taga tana fitowa daga idon shi girgiza kai ta farayi tana kallon mutanen palon amma ba wanda ya kaleta cigaba yayi da maganar duk cikin yarana duk yarana bawanda ya taba wulakantani haka da zubda min girma haka seke Ahlam ......Mama ce ta fara magana Ahlam dama barin ki nayi da haihuwar ki...... Da sauri ammi ta toshe mata baki tana fadin kull!!! dukda itama kukan take tari ne ya tsarke Alhajin yayinda yayan Ahlam suka taso suka mika masa ruwa sanan sukayo kan Ahlam da duka, dukan ta suke kamar zasu kashe ta ihuu take tana neman temako amma ba wanda ya musu magana kansu kyle ta Seda suka mata lilis sanan suka kyle ta

Ahlam kin bani kunya ace tun kafin kiyi aure kika zubda mutumcin ki na y'a mace Haba ahlam ace har kina zubar da ciki tun kafin kiyi aure wanda hakan yasa yanzu bazaki kara haihuwa ba Ahlam ya zaki mana haka girgiza kai tayi tana ja da baya gata a jigace saboda dukan da tasha wallahi Alhajin mu shari ne, shari suka min .......yusuf ne yake fadin ai ga takarda nan Ahlam ab duba an gani dan haka nasake ki saki 3 maman yusuf din ce ta fashe da kuka Ahlam muna son zama dake Amma ......Alhajin mu karka yarda dasu wallahi sharri ne 'kazafi ne ban aikata ba wallahi ku yarda dani wai ba wanda ze yardani ne ta kali gefenta yaya Abubakar kai kasan bazan aikata ba wallahi banyi ba ban aikata ba yusuf ka fada musu gaskiya wallahi banyi ba ku temake ni bani vace ni Ahlam ban aikata ba mamana kema kin yarda kenan na rantse sharri ne kama kafar yusuf tayi tana jijigawa ka fada musu ban aikata ba banyi ba ni Ahlam ban taba aikata zina ba bale har na zubda ciki tasss!!!! taji an wanke ta da mari ba kowa bane se Maman ta yi mana shiru ma'karyaciyya in kika cigaba da magana sena tsine miki.......Jiri ne ke dibar ta tunda take mama bata taba sa hannu a jikin ta ba se yau har tana ambaton tsine mata lalai uncle yusuf ya cuci rayuwar ta ashe da gaske yake mata na seya jefata cikin *RAYUWAR KUNCI* lalai duniya *RIGAR ARO* (na ummu nabil) ce yau gareka gobe ga dan uwanka lalai  gwra ta mutu da abunda yusuf ya mata tsakanin ta dashi se hisabi a lahira  ki tsayawa mutane akai *mazinaciyya* kawai ba kowa ke magana ba se hajiya babba kin cuce mu kin yodare mu Ahlam shikenan tana gama fadin haka ta fice a fusace mama ma ta bita su yusuf ma suka fice ya rage daga ita se Ammi se Alhaji girgiza kai take aa alhajin mu kai ka yarda dani sharri ne sharri suka min wallahi banyi zina ba ni ba mazinaciyya bace ban aikata ba  ku yarda dani tana fadin hakan ne murya a dashe

Hanbare ta yayu ta fadi ya tashi ya fice faduwa tayi ta yayinda Ammi ta taso a hankali ta dagota sedai me gani tayi Ahlam bata motsi jijiga ta tayi Amma Ahlam ta kasa motsi

Ji yayi gaba daya jikin shi ba dadi ya rasa dalilin yin hakan meyasa duk abinda yake jiki a sanyaye yake yin shi ba kowa bane se faruk hotunan Ahlam ya dauko yana kallo ganin Ahlam yayi a cikin hotuna tana fadin Faruk ka temake ni ka temake ni

*kow yasan ni yasan bana long typing kuma bana littafi ya wuce 40-50 ni kawai ina rubuta abu ne da ya kunshi book din gaba daya bana tsayawa kakale kakale da karyar arziki sakona kawai nake isarwa direct*

*dont forget to*

#vote
#comment
#share

BIYAYYAWhere stories live. Discover now