Part 21

54 3 0
                                    




And'au tsawon lokaci kafin dajin yadena girgiza hakana kogon junoor,yareema irfan d gimbeeya jawahir da suka zuba ido suga jaririn randa da mamakinsu se suka ga abu d'an tsurut alullub'e azani se sheqa uwar dariya yake,ahankali suka matsa kusa dashi yayinda hannunsu Ke sarqe dana juna ai ko taku biyu basiba,su kaga yayi wata iriyar girgiza yakoma wani qaton baqin aljani me qaho guda biyu,se gashi sunzama'yan tsirit kamar kiyashi agabansa, nan danan hankalinsu ya d'ugunzuma ainun ganin yacce yadawo,wata mahaukaciyar dariya yasaki yana "tabbas nasan zaku zo Amma be kamata ku b'uya ajikin bil'adama ba saboda bakuda tasirin iya shigowa nan gurin shiyasa zaku fake da qananun halittu wajen d'aukar fansa hhhhhh inada shu'umin iko da qarfin izzah zab'i biyu gareku ko kwantar dakai kuyi mubaya'a ko ku fuskanci azaba mara yankewa,kamar yadda magabatanku suka d'and'ana ahannun nuwairah "

"Qarya kake shu'umi !!!! Munfi qarfin mu fake ajikin bil'adama sedai kai sani da cewa gimbeeyarmu da yareema zasu wanzu domin zuwan wannan ranar ?!!"da amsa kuwa yaji muryar jawahir tana fad'i yayinda idonta ya sauya kala.

Afusace yasa hanunsa ya wartota segata'yar tsirit ahanunsa wata shu'umar dariya ya kyakyace da ita kana ya wurgar da ita gefe guda aikan kace meye kamar iska yareema irfan yatashi fuuuu yahaye gadon bayansa da idanuwa yakalli takobin dake rataye ajikin bangon aikwa segata ahanunnsa daidai Allon bayansa yacakamasa harseda ta lume duk tsayinta aikwa wani girgiza yay had'I da karaji tare da wurgashi gefe guda,,nan danan halittarsa ta sauya yadawo kamar yaro d'an shekara 10 Amma jikinshi duk gashi kamar na akuya ko rago wani irin sufa yayi ya nufi kan jawahir,da hanunta ta watsamai kunfar wuta wacce batasan taya akai tafitoba kawai taga hanunta yanaci da wuta aida gudu yaja baya yana muzurai da idanuwa,tofa !!! Ansoma....

B'angaren ragowar d'aliban da fulaninan sunanan daga bayan kogon junoor gaba d'ayansu sun lab'e suna ganin yadda kogon Ke qara yana fitar da wani irin sauti gashi alokacin gari yafara wayewa, b'angare guda kuma securities sunyi waya domin aturo jami'an tsaro tare da ambulance.


Sun shafe tsahon awa guda suna fafatawa tare da jaririn randa gaba d'ayansu sun galabaita damma sun qara samun wani qarfin ikon da basusan daga ina suka samoshiba,abun dayafi wahalar dasu shine yacce yake b'ace wa b'attt ko kuma yay ta sauya halitta dan yanxu haka yakoma zuwa qadangare irin Jan gwala gwadannan harin d'afewa jikin jawahir yake kuma yasamu nasarar d'afewa wani irin zafi taji domin cin namanta na gurin yake , aikwa nan take irfan yazo yay yay ya b'anb'arosa yakasa idan ya matsama shime seya gutsurammasa nama ita kad'ai tasan azabar datakeji,wani irin qara take  aduk lokacin daya gutsiri namanta. "Wayyo Allah Jawahir meke faruwa??? Nashiga uku??? "Muryar aunty hibba sukaji yayinda take qoqarin shigowa gurin ,idanun jawahir dayafara sauya kala alamun ba iya namanta yake ciba har guba yake samata tafara d'agamata hannu da karta sake tashigo ta juya duk da bata gane wace ma ita agurintaba.

Amma ina aunty hibba takasa juyawa da gudu ta qaraso, wannan wuqar data tsinta agarin neman jawahir ita taciro tacakamasa aciki kana tai wurgi dashi,Innalillahi gaba d'aya fatar gurin ta d'auke har wani rami gurin yay saboda tsabar azaba yacce Kasan qonuwa ,kallon wuqar tai jawahir da sauri ta d'auka kana tashafata akan gurin da yahau nan take wani Koren hayaki yafara fita, d'aukewar hayakin kuma keda wuya gurin yadawo kamar bakomi daya samu gurin,wata mahaukaciyar dariya tayi kafin takalli hibba tace " ina godiya yarinya kinyi qoqari da kika kawon wannan wuqar hatimin."

Mamaki tsoro razani firgici sungama shiga jikin aunty hibba Shikkenan an sauyamata'yar uwatta,jaririn randa ganin yagalabaita sosai yasashi neman mutane domin yasha jini Dan qarfinsa yadawo,kogon da su beelal adam Ke ciki ya nufa Dan yana jiyo qanshin jini tindaga inda yake ,yayinda b'angaren jawahir kuwa qarfinta yaqaru ,cikin zafin nama suka miqe kana daga bisani suka shiga Dubé Dubé ...Amma idanunsu ya rasa shu'umin aljanin.....

Tunda yakafa kai awuyan beelal adam be sakeshiba seda yashanyemasa jini tasss ,wnai irin dariya yayi kana ya kuma had'a ido da sauran d'aliban yayinda dukansu ba wanda be fitsari ba Dan tsoro,tabaya yaji andamqoshi yareema irfanne ai suna had'a ido yasakarmasa wani irin shu'umin murmushi sannna ya b'ace b'atttt nan take wata BAQAR guguwa ta gauraye kogon wanda baka iya ganin komi  jitai ayanketa ahannu,hakana irfan ma agefen damtsensa yaji anyakeshi afusace y d'aga hannunsa ya daki qasar gurin yana fad'in "yaku shu'uman aljanu ku dakata da zirga zirgar da kuke !!!!"aikwa tsiiitttt kogon yayin guguwar ta d'auke kamar bata tab'a wanzuwaba.

Zaune take akan kujerar kwanrangwal d'innan  ta hard'e qafa d'aya kan d'aya idanunta se hayaqi suke (aunty hibbace) tana facing d'insu yareema irfan ,cikin wata iriyar murya tafara magana "ayauma kinada zab'i guda biyu jawahir hhhhh inmade kikashe'yar uwarki ko kibarta nikuma danake jikinta nakasheki!!!!! Hhhhh"

Zaman dirshan tayi aqasa yayinda irfan kuma ya zauna tare d kwantar da cinyarsa akan qafarta wata wawiyar dariya sukeyi wanda su kad'ai su Kasan ma'anarta kafin dg bisani si shiru irfan yakalleta yace "yake nuwairah tare da shu'umin jaririn randa kusani cewa tarihi maimaita kansa yake!!!! Kuma yauma ze maimaita duka yaran bil'adammanan damuke jikinsu tabbas be kamata mucutar dasuba wannan tsuhuwar gabace wacce mu aljanu bazamu iya kawo qarshentaba dole se cikin qanannan halittu tabbas Ke shu'umace dakike so ki had'a qanwa da 'yarta fad'a d'aya takashe d'aya to ni sarkine hakan baze faruba....."

""Hhhhhh kusani cewa tinfarko ku kuka kawo bil'adama cikin rigimarnan,domin ku samu tasirin shigowa kogonanan dan haka dole su cutu dan ku kuka fara cutar dasu nibanada tausayin wani jinsi na mutane " hibba tafad'i tare da wani malqar da wuyanta gefe guda ,had'e hannayenta guri guda tai tafara karantu wasu sunayen manyan aljannun dake kogon kan kace meye halittu daban daban sun bayyana,nuni tamusu gasu jawahir da irfan da agaggauta b'atar dasu sutafi can bayan duniya yayinda take so taga gawar jawahir da malam irfan agurin ......

Nan danan suka yo kansu,cikin zafin nama su yareema irfan Ke kare kansu ,gumurzu yay gumurzu kogon junoor banda qaraji da girgiza ba abinda yake ,sun shafe awa uku ana d'auki ba dad'i daga ganin fad'an tabbas inba aljanu bame iyashi Dan kwata-kwata ba qaqqautawa,hankalin sarauniyan nuwairah ya d'ugunzuma ainun ganin yadda aljannunta keda nakastuwa suna guduwa wanda yarage befi su ukuba........

Afusace ta tashi tashigo gumurzun,inda suka fara zabga azababben fad'a da jawahir da aunty hibba kowa yana neman ran d'an uwansa al'amarin dayatashi hankalin sarkin aljanu wato hayat dake jikin malam irfan matuqar sukawa yarannan hakan basimasu adalciba,dole yasan yacce za ai su fita daga cikin kogon da yarannan daman burinsu na shekaru dubu biyu be wuce su fito da jaririn randaba kuma hakan baze tab'a yiwuba matuqar suna jinsunsu na aljanu Amma yanxu kam burinsu yacika,Dan haka cikin zafin nama yashiga tsakanin gimbeeya jawahir da sarauniya nuwairah yayinda yad'auki jawahir kamar iska suka tashi sama fuuu daidai kogon da suka ajjiye ragowar d'aliban suka Nifa nan take suma suka kwaso su...

Tofa abun al'ajabi be qarewa yayinda jama'a kowa da kowa sun lab'e suna ganin girgizar d kogon junoor yake Dan har'yan jarida sun qaraso gurin ambulance da kuma jami'an tsaro, yau karo na farko atarihi qofar kogon junoor ta bud'e nan take 'yan jarida aka fara d'auka, inda jami'an tsaro keta shiri da dabarar dazasu ceto mutannen dake cikin kogon ,sega malam irfan da jawahir d'auke da ragowar d'aliban mutum biyar inda mutum uku suka ransa ransu wato ablah Kabeer , yusuf bashir,se beelal adam .

Fitowarsu keda wuya mamaki yacika kowa, ganin sun galabaita yasa nurses din da aka d'akko a ambulance d'in saurin qarasawa gunsu da gudu wasu 'yan fulani suka qarasa suna karkuje Jan mutane yake Amma ko kallonsu basiba ganin sun qarasa ba abinda yasamesu yasa kowama ya iya qarasawa gurin ba abinda yafi Jan hankalin mutane ganin yadda shigar malam irfan d jawahir suka sauya zuwa na wasu mutanen da suka shud'e shekara da shekaru.

Had'a ido sukai irfan da jawahir, abad'ini kuma hayat da hayatiy wato sarkin aljanu da matarsa wanda Asali aljanun gimbeeya jawahir ne da yareema irfan ,nan take jikinsu yafara wani irin kaf-kaffffffff aikwa bashiri akayita kansu ...

Read and share

SHU'UMAR IZZAH Where stories live. Discover now