Part 1

368 20 2
                                    

*SHU'UMAR IZZAH*
        
       *written by gimbeeya*
               (Mss 1love❤️)

*part 1*

Har qarfe 12:30 nadare jawahir na falo ita kad'ai tana kallo duk 'yan uwanta sunyi bacci amma idonta k'irrrrrr Mbc 2 take kallo inda ake film d'in silence hill film d'in na horone shiyasa adirirce take kallon film d'in ,ahankali taji andafata da sauri ta zabura ganin mom yasata ajiyar zuciya tace "wayyo mom kinbani tsoro "
Mom tace "badole nabaki tsoroba kin zuba ido kina kallon horror film,kowa yay bacci yabarki "
Lumshe idotai tace "nima fa baccin nakeji mom bara kawai nakwanta "
Zuwa tai ta zare sucket takashe kallon sannna takalli mom tace "seda safe "
Mom tace "Allah yatashemu lapiya karki manta ki kashe kwan d'akin bakyau kwana ahaske "

Jawahir tace "

ok mom have a sweet dream "adaidai lokacin datake kutsa kanta cikin d'akinta "

————————
Dare mahutar bawa kowa yaje yakwanta gari yayi tsiitttt ba abunda kakeji se kukun tsuntsayen dake kan bishiyoyin gidansu,wata iska ke kad'awa saboda yanayin hadari agarin hakan yasata kuma qudundunewa cikin bargo,bajimawa kwa aka fara maka uban ruwa adarenannan,amma hakan besa jawahir farkawaba.qessss taji ankuna lantarkin d'akin daga kwancen datake ta bud'e idonta,muryar mom natace taji tace "jawahirrrr yauma nazone nabaki labari amma wannan yanada tsayi domin kece alabarin bawataba "

Ahankali ta bud'e sleepy eyes d'inta tace "mom wai meyasa bakya zuwa bani labarine se tsakar dare kuma bayan munayin sallama dake ai alokacin dase kibani kuma da safe kitamin fad'a ina makara sallar asuba bayan ke kike hanani bacci "

Shafa kanta mom tai tace "jawahir yanxune nake da lokacin baki labari "
Zumb'uro baki tai tana "gsky ni yau bacci zan mom gobe kyabani "taja blanket dinta takuma rufa,
Kamar anwurgota k'asa taji kanta yadaki bangon gadon datake da sauri tamiqe kanta na mata wani irin zafi,kallonta mom tai tace "lapiya "
Ahankali tace "mom kaina ne "
Tana riqe dakan saboda dakyar tai maganar ,shafa kanta mom tai tace "bara nakamamiki "
Rangwad'ar dakai kawai tayi "tinda mom ta riqe mata kai taji kan yafara daina ciwo gashi baccinma kwata kwata yad'auke,tayi kamar 2mint kamin tasakarmata kan tace "to sannu seki kwanta tinda yadaina "
Jawahir tace "a a mom nifa banajin bacci yatafi kawai bani labarin "
Murmushi mom tayi tace toh amma kirufe idonki domin in inabaki labarin zakidinga gani kamar gaskene saboda zakiga abun a idanunki.
Tace "shikkenan gami da rufe idonta "

———————
Shekaru dubu biyu dasuka wuce
Zaune take akan wani dutse me girman gaske ga fad'i ga wani uban tsayi zaune take kamar yacce uwarta takawota duniya ,hayaqin dayafara fitowa daga idontane yasa dutsen yafara narkewa zuwa ruwan jini,har ya narke gaba d'aya shiga tai tana wanke jikinta da alamu wanka take,bayan tagamane ta tashi fuuuuu kamar iska bata tsaya ko inaba se garin NUWAIRAH daular matsafa da aljanu,wani yankine a acikin dajin dake arewa cin Nigeria wanda ayanxu ake kiransa da falgore,timmm tasauka akan wata bishiyar dabino kamar macijiya haka ta sulale tayo qasa,saukarta daga kan bishiyan keda wuya se bishiyan takama da wuta kamar wacce akasawa fetur,hakana tana dire qafanta aqasa nan danan macizai kunamai giza gizai suka fara hawa jikinta sushiga ta kunne sufita tahanci sunkai tsawon minti 20 suna zagaye jikinta kafin daga bisani su sulale qasa,d'aga murya tai tace "se ni Sarauniya nuwaira!!!!!kuna inahhhh "

Wata irin guguwace ta tunkarota me tsananin duhu qarasowar guguwar ne kusa da ita yasa tafara had'ewa,sega wasu irin mutane masu jela jikinsu duk gashi uwa tumaki tace "ina farautar abincina "

D'aya daga cikinsune yasunkuyar dakai yace "suna kogon junoor "

Wata dariya tai tace "shagalin shekara yakusa zagayowa,kuma jariri yakusa fitowa daga cikin randa,kuma dole awanke shi dajinin wata mad'aukakiya dan haka zamuje mu d'akko gimbeeya 'yar sarki,wacce sukeji da ita ba iya jinin al ummar garinsu zanshaba harda jinin magajiyar karagon sarautarsu,"

Atare sukace "sarauniya nuwairah kiyi komi acikin isarki!!!"

Daganan batace komaiba takuma tashi sama kamar iska fuuuuu se bakin kogon junoor shafa hannunta tai kawai abakin kogon se gashi dutsen dake jiki ya wangame,randace aciki wacce tayi girman dutsen da  sarauniya nuwairah take wanka,wato dutsen jini,se wata kujera wacce aka yita da kwarangwal d'in mutune agefen randar,daidai kujerar tazauna ta wurga hannayeta sega kogon yacika da haske.

Mutanene ajere sunkai su 30 d'aure da sarqa kallonsu tafarayi tace "inaso na samu qoramar jini acikin kogonnan kuma bada jinin kowaba senaku,Dan haka kowa yad'auki wuqa ya caccakawa kansa yacce ko ina nashi ze b'ule naga jini na kwarara!!!"

Gumi ne yafara keto musu na tashin hankali sukafara "sarauniya nuwairah amana afuwa,bama da had'I da gimbeeya jawahir haqiqa zata kawo kanta gareki matuqar kika sakemu "

Afusace sarauniya nuwairah ta miqe tace "banason jin sunanta tabbas kunjawa kanku "bashiri hannayenta sukai fiqai fiqai farcenta yay zaqo zaqo,haqoranta sukai fiqa ta nufi kansu gadan gadan,hannayenta tasa acikinsu tana zaro hanjinsu sekuma takafa kai akansu tana zuqo kwakwalwarsu suna ihu.............

Koda mom tazonan alabarin firgigit jawahir ta bud'e ido tana "wayyo mom wanne wane zalinceni bazan iya jiba saboda wlhy komi kike gayan inaganinsa a idona "

Murmushi mom tai tace "yanxu saura awa d'aya da rabi ai asuba kikwanta kamar kullum karki sake kigayawa kowa kuma karki sake kimin maganar harse nazo gunki "

Tace "shikkenan mom "

Shafa kanta tai bajimawa kuwa bacci yakuma d'ibarta,b'attttt mom tab'ace daga d'akin....

 
Read and share

Comment dinku shizai sa naji gaba
09024410404 for more books

SHU'UMAR IZZAH Where stories live. Discover now