Part 4

70 4 0
                                    

SHU'UMAR IZZAH

       Written by gimbeeya
             (Mss 1love💔)

PART 4!!!

Ahankali mom tafara bud'e idonta tana "Ina annur???dan Allah ku kawominshi,dan Allah inason ganinsa "

Ba iya nurse d'in asibitinba har likitocin seda tabasu tausayi hibbace ta rungumeta tana kuka tace "mom annur yatafi yabarmu ,ummah bazamu sake ganinshiba "setafashe dawani kuka nan suka had'u suna tayi amma jawahir tana gefe d'aya ta sanqame ,ido kawai take wurgawa,doctor ne yazo yasamesu yace "hajiya se haquri dukkan me rai mamacine,tabbas dukanmu zamu mutu in lokaci yayi wanda yakarb'eshi yafimu sanshi dan Allah kuyi haquri yanxu za afito dagawarsa se aje gida domin amai sittira "

Akan wheelbed aka turoshi jawahir na hango gawar annur kawai idonta ya haskomata jiya da daddare lokacin dayabata cupcakes d'innan yana "kici wlhy da dad'i "

Hangon jinin dake fuskarsa jiya da daddare tai "wato danacemai kar yatafi yabarmu ashe tafiya zaiyi shine yabunne kanshi,shin me akai masa zetafi yabarmu"

Itakuwa mom riqeshi tai gam tana jiyo muryarsa shekaran jiya da rana yana"mom dan Allah kije makaranta kice amin jumping so nake na girma nazama lawyer ,mom na dinga tsayawa agaban alqali ,se yamiqe tsaye ya tsaya straight yana "objection my loard !!!"

Dariya sukai gaba d'aya ganin yacce yadage uwa yana gaban alqalin mom tace "ai annur qoqarinka shizai kaika ai"

Yace "aikwa mom zandage sosai "

Maganar doctor da mom taji yadawo da ita daga tinaninta yace "hajiya kisakeshi za asashi amota"

Hibba ce tariqe mom ,se jawahir data riqe hannun siyama mom ce kawai amotar gawa sukuma sukahau motar mom ,uncle fahad ne yk driving ,dan tunda suka taho da asuba hibba takirashi awaya.

Misalin qarfe goma na safe angama had'ashi maqotama duk sunshigo ,daddy ne yakuma kiran mom yajaddamata cewa gobe ze taho daga china inshallah ,saboda mom cewa tai da abari seyazo sannan akaishi makwancinsa,amma dad ya nusasheta cewa anaso agaggauta kai bawa makwancinsa badamuwa gobe zaixo.

To bayan angama had'ashi aka umarci su hibba d mom da jawahir suzo sumai addu' a za atafi kaishi,dakyar mom ta tashi sukaje addu a suka dinga mai.

B'angaren jawahir kuwa jin muryar annur take yana"haba aunty jawahir kina kallo za atafi dani banmutuba dan Allah kice su dawo dani!!"

Da sauri jawahir takalleshi taga ana qoqarin fita dashi ai da sauri tamiqe tabisu tana"dan Allah kudawo dashi wlhy bemutuba dan Allah "binsu tai,nan Gwaggo ta riqeta tana "jawahir haquri zakwi kowa d'an hakane.

Amma ita bata yarda annur yamutuba cewa take "wlhy gwaggo da kunnena yacemin be mutuba "

Dafa kanta gwaggo tai ganin tarikice tafara mata addu'a ahankali tafara samun nutsuwa.

Itama mom jikin gwaggo tazo ta lafe gwaggo ko se aikin rarrashi take tana "haba hauwa 'u tawakkali zaki kika rasa mahaifinkinma kika haqura "

Mom tace "gwaggo ba rashin lpy ba komaifa kawai naje tashinsu sallar asuba naga idonsa aqafe munazuwa asibiti akace yamutu "

Gwaggo tace "aidama mutuwa base da cutaba "

Tofa duniya kenan wanda yamutu shiya mutu,wanda tashafa shi tashafa su aunty bahijja da qannen daddy da cousins d'in mom se hidimar dafa abinci suke harda masu cewa "wai girkin be saukabane "hmmm duniya kenan (kowama kamar hakane kana mutuwa kazama tarihi)

Da yamma 'yan uwa na nesa da maqota suka tafi domin zuwa gobe zasu dawo se gwaggo aka bari mahaifiyar mom da kuma Adda itakuma yayar mom ce se inna kareema matar baban daddy dayake mahaifiyarshi tarasu se abokiyar zamanta duk da bawani son daddy sukeba amma tayi kara tazauna.

SHU'UMAR IZZAH Where stories live. Discover now