Part 6

61 4 0
                                    


Shin kin karanta littafin NAMASTE WAHALA kuwa???ko ko kin karanta AQIDATA??shin kinji labarin littafinanna wai SO MAKAHO NE??Qawata akwai buqatar kisiyi littafin SIRRIN MU ?anbarki abaya wajen sayen littafin GAMO na billygaladanci to tabbas kar ayi baku awannnan littatafan 💔💔💔qawayena 🥰🥰.

Hayaqine kawai ke fitowa daga idon sarauniya nuwairah yana shiga na gimbeeya jawahir,anyi 'yan sekanni ahaka jawahir duhu kawai take gani a idonta,daga bisani kuma ta ganta atsakiyar  daji me wani uban duhu duk da haka littafin yana hannunta amma yanxu an rufeshi ,nan take kuma kanta yafara juyawa saboda irin dogayen bishiyun dake dajin .

B'angaren hibba kuwa atinaninta duk qarar datake ji mafarki take shiyasa ko kad'an bata tashiba ,haka abokan zamansu na gidan kwata kwata basusan meke faruwaba,kamar an mintsineta tafarka kuma taci sa a ankawo wuta ganinta ita kad'ai akan katifa yasata tinanin to ina jawahir tai ,wata zuciyarce tabata hala shiga toilet ne,shiyasa takuma juyawa ta koma bacci abinta.

Kwasss !!kwasss !kwasss !!kwassss yake jiyo takon tafiya inda ake tafiyar da takalmi me tsini ,firgigit ya tashi ta window d'akinsa ya leqo.tsaye take ajikin qarfen benen gidan ,yahangota fara tasss gashinnan har d'uwawa duk da tajuya baya hakan be hanashi gano shape d'in kuguntaba,wani murmushi yasaki aranshi yace "wato yaran da suka kama d'akince ashe 'yan hannune May be takasa baccine shine tafito tasamu d'an tayi hhh yarinya kwa kinsamu daidai dake bakisan waye saif bane "

Ahankali yabud'e qofar d'akinsa daga shi se singlet se boxers ya nufota tindaga nesa yakejin qamshin turare nadukan hancinsa ,cikin rawar jiki yaqaraso yana"hey bae lapia kika fito cikin darennan dawannan kyakkyawar kwalliya me gigita tinani kinganki kuwa wannan kwalliya acikin dare aise aljanuma su taya "

Wani murmushi tai tajuyo takalleshi wow kyau ma yayi mata yawa sannan takashe murya uwa me koyon magana tace "hey dear nakasa baccine cos kasan kwana asabon waje ,gashi inajin sanyi kuma bamu taho da bargoba "

Yace "ayyah ai irin hakan nafaruwa amma d'akina Kafff gidannan yafi ko ina d'umi sannan inada manyan bargona bae kawai kitaho mi squatt "

Cikin shagwabe fuska tace "bazan takuramaba?"

Yashe baki yay ganin ta amince da wuri yace"no ai ba takura bae taho kawai"

Daganan suka nufi d'akinsa,har wani gyaramata katifar yakuma yi yabata wani qaton bargo saboda shi duk yarude dakyan halittarta,bayan yagama bata duk abinda yadace agefen katifar yazauna kashe murya tai tace "kai bazaka kwantabane?"

"To ai ganinai uwa wajen zai mana kad'an "cewar saif

Dan matsawa tai kad'an tace "ga wajenan ka iya kwanciya "

Aikwa hakan akai yakwanta kusa da ita tinda yakwanta hankalinshi yad'auke saboda wani irin feeling dayaji ahankali yafara shafa bayanta numfashinsa na sama sama ,itakuwa gyara kwanciyarta tai takuma juyowa ,tinyanayi cikin saninsa haryafara rikicewa sosai yake shafata yana huramata wata iska akunne gaba d'aya yarikice ganin haka yasata fara kissing dinshi asalo nadaban besan lokacin da wani hawaye yazubomaiba saboda dad'i ,ita ko kissing dinshi take sosai.

Tofa tinyanajin dad'i yanxu numfashinsa yafara fita sama sama saboda tarufemai baki da bakinta gashi gashinta yatushemai hanci,jiyay uwa tana zuqo jininshi ,itako nuwairah tinda takafa kai abakinsa take shan jininshi ,idon saif kuwa tini yakafe domin jininshi datake ta zuqa.......

—————

Jawahir haryanxu bata motsa ko inaba adajinannan saboda bata hango gaba bata hango baya ,littafin ta d'aga taga yana wani haske wanda ya haske wajen datake gaba d'aya,jini taga yana kwarara tacikin littafin daidai page din da hoton sarauniya nuwairah yake,gabantane yace rasss badai jinin yayarta takeshaba da mutanen gidan dasuke ,dama da gaske take cewa seta kashe kowa!!!nan fa maganar mom tadawomata "indai baki d'au matakiba zakirasa nakusa dake harta iyayenki "

Shin wane mataki zata d'auka???dolene ayanxu tayi wani abu domin ceton yar uwarta da bayin Allah dabasu san komiba.

——————
Sautin da akeyine daidai kunnenta yasata farkawa ,ahankali ta bude ido,Bud'e idonta keda wuya taga and'auke nepa ,wayarta takunna ta fara haskawa domin ganin wake wannan sautin abu nafarko datafara lura dashi jinin dake katifar sannan kuma haryanxu jawahir batanan,nan take tsoro yakama hibba badai jinin jawahir bane???aikafin tagama isar da tinanin kwakwalwarta taji an cafki wuyanta,sosai taji damqar har maqogaranta nan take tafara kakari idonta yayo waje.....

Har yanxu jinin baidaina fito waba daga cikin littafin,jawahir cikin fargabar abinda sarauniya nuwairah ke shirin aikatawa yasata saurin bud'e littafin ,nan take kuma taga sarauniya nuwairah kwance akan saif tanajan jininshi,nan kuma hannuntane ke damqe da wuyan hibba ga kuma wata iska dake shirin d'aga gidan gaba d'aya ,arud'e jawahir tafara karanta rubutun qasan hoton.

"Tabbas hakan seyafaru dan ganin hoton sarauniya nuwairah babban abune,hakan ze jawo babban tashin hankali domin qarfin shu'umar izzah datake dashi ko hotonta yanada tasiri aqarfinta,hanya d'ayace yanxu zata kob'utar dake shine wannan dajin dakike ciki tabbas ita takawoki nan kuma anan ruhin gimbeeya jawahir yake anan takasheta kuma kema anan zata kasheki inbaki qoqarin kub'utar da kankiba,tabbas ki qoqarin samo inda takasheta sannan ki d'auki crown din dake kan gimbeeya jawahir kisa akanki ,tabbas anan zaki samu damar cire hotanta alittafinnan sannan ki karantashi cikin nutsuwa asannan kigane wacece ke ,kuma menene yakawoki rayuwar mutanenen dasuka shud'e shekara dubu biyu dasuka wuce !!!""

Tana zuwa nan akaratunta qirjinta yabuga yanxu wannan dajin dayake da uban duhu taya zataga gimbeeya jawahir bare crown d'inta ,gashi tabbas bata da lokaci inba ta dakatar da sarauniya nuwairah yanxuba tabbas zatarasa yar uwarta da mutan gidannan gaba d'aya,amma meyasa tinfarko bata sanarmata dahakan ba dabata bud'e ba wlhy,aranta takuma cewa yanxu ba lokacin wannnan tinaninbane,bashiri tafara tafiya cikin dajin tana lalube.

Dan Allah kumin afuwa da wannan yau banjin typing muhad'u gobe......

Read and share

09024410404 for more novels

SHU'UMAR IZZAH Where stories live. Discover now