Part 10

61 6 0
                                    


  
  "When ur intentions are pure,u don't lose anyone,they lose u!!!!!"

Knocking d'in da ake aqofar d'akinne yasata dawowa daga tinanin datake nasawa malam irfan zobe,cikin kasala ta tashi ta bud'e qofar ,tindaga bakin qofaar hibba tafara mata masifa wai ta batta tana ta knocking tin d'azu taqi bud'e wa .

jawahir kallonta tai tace "kinga dan Allah aunty hibba kirabu dani plx banson damuwa yanxu gsky "

Riqe baki hibba tai tana "lallai komi zaki fad'i wlhy bazan fasa gayawa mom abinda kike aschool ba,sannan kuma kiturawa dad account number yanxu yakirani ina hanya nagayamasa zamu excursion yace mutura account number kuma kinsan nawa yasamu matsala "

"Aunty hibba sedai yaturo naki ke kad'ai ni ba excursion d'in dazani "cewar jawahir

Wani kallo ta watsamata tare da d'akko wayarta tafara saka katin awayarta tana "shikkenan aiba matsalabane karkije bara innakira mom seki gayamata bazaki excursion d'in 30marks ba ,ko 10marks kasamu a exam aika wuce carryover bare,bara inna kirata seki gayamata kinji"daga haka tafara dialing number mom,ko ringing uku bataiba mom tad'aga tana "daughters yanxunannan gwaggo take cewa nakiramata ku ,taji muryarku gama siyama itama wai akiramata aunty hibba "

Hibba daria tai tace "hajiya gwaggo tsohuwa nason jin muryar jikokinta hhhhh mom bawa siyama wayar to "

Nan mom tabawa siyama suka gaisa siyama se shiririta take wai itama tanaso tashiga jami a yarinyar dake nursery 2 itakuma hibba se biyemata take,duk abinda suke jawahir nakwance idonta arufe kawai tinaninta tayama zata doshi malam irfan ,jin ana karamata waya yasata bud'e ido.

Hibbace tace "gashinan zakwi magana gwaggo ce tace abaki "

yatsina fuska tai tana "ke nifa bazan iya magana yanxuba "

"Oh haba shikkenan bara kiga "akunnenta hibba tasa wayar tafara "gwaggo kinajina?"

Tace "eh har uwarkima tanajinki "

Hibba tace"yawwa ,mom gwaggo wlhy jawahir bakaratu tazo ba yau d'innan munyi test batai komiba ,tawa malamin rashin kunya yakoreta waje,kuma zamu excursion tace wai bazata ba mom wlhy excursion d'in nada muhimmanci maki talatinne fa amma wai bazataba kuma hartayi wasu abokai maza Allah gwaggo jawahir ba karatu ke gabantaba ko jiya da mukaje library karatu ita qin zuwatai bata komi se bacci ad'aki "

Gwaggo ce tarafka salati ,mom kuma tace sa wayar ahandsfree,hibba tace nasaka.

Gwaggo ce tafara da "jawahira aure kike sone??seki dawo aimiki tinda bakaratun kike soba"

Mom ta amshe da "ko auren takeso tasan halin daddy ai,to tsaya nagayamiki wlhy jawahir ki kiyayeni malaminku kikewa rashin kunya karatunma be gabanki to tun wuri kije ki bawa malaman da kikawa rashin kunya hakuri inbahakaba wlhy se ranki yab'aci dama gobe daddy ze koma china Allah zamu iya zuwa mu b'atamiki rai wlhy "

Cikin tsananin takaici jawahir tacae "wai mom komi tafad'i se ayarda,shifa malamin da kansa yace bazani excursion d'insaba kuma yace seyabani carryover kawai yatsaneni ne "

"Nidai nagayamiki kuma komi tafad'a nasan zaki aikata ,jawahir ba qarya za amikiba sannan dan Allah karkije excursion d'in nan kiga yacce zan dake koyace bazakiba ke kinfi qarfin kibada haquri "mom ta fadi ranta ab'ace

Tofa jawahir taga takanta haka gwaggo da mom suka had'u sukai tai mata fad'a har seda kanta yafara ciwo uzirin yin sallah tabasu domin tasamu damar daina wayar daganan tabawa hibba wayarta ,yayinda taji 'yar uwartata tabata haushi shiyasa tad'au alwashin fita daga harkarta har abada tadaina mata magana tinda munafukace !!!

——————-

Dare yay dare! Dare mahutar bawa gari yayi shiru babu abinda kakeji kowa ya nausa cikin bacci,jawahir zaune take aranta tama rasa wai meke damun rayuwartane wani irin abu ke damunta Dan Allah miyakawo ta cikin labarin mutanen dasuka shud'e shekara dubu biyu yanxu har wani gardi ma zatasawa zobe kaiiii!!!!!nayi danasanin zuwana kano kai!!!!Innalillahi,daga haka tajanyo littafin aqarqashin akwatinta dan yau bazatai bacciba setaga qarshen uwar daka saboda tasan halin hibba intafara bacci kamar gawa se asuba zata farka.

SHU'UMAR IZZAH Where stories live. Discover now