Part 20!

47 2 0
                                    



Wani ihu jawahir tasaki jin damqar da akamata ta shaqe mata wuya,jin ihunta yasa malam irfan saurin kiran sunanta "jawahir lapiya!!!"yafad'i lokaci guda yana laluba inda yake tinanin zejita ai daga wannan ihun be sake jintaba cigaba da lalube yake acikin duhu.....

B'angaren aunty hibba kuwa ta kasa zaune takasa tsaye harseda tafakin idon securities da kuma su lamrat dan Allah yatemaketa bacci yakwashesu saboda sun gaji kuma aqallah yanxu uku ta wuce na dare ,aikwa tafito tabazama neman jawahir Amma ina ba ita ba labarinta nan take ta nausa kanta cikin dajin saboda bazata iya jurewaba wani abu yashafi'yar uwartaba.

————- ya laluba ya zagaye ko ina bejitaba ya kira sunanta ya kira Amma shiru,wani irin abune yazo ya tsayemasa arai yazeyi da rayuwarsa wannan wace qaddarace ??wacce take tausayamasama itama ya rasata beson lokacin dayasaki wata razananniyar qaraba,wacce harseda kogon ya amsa kafin kace meye kogon ya fara fitar da wani irin sautin me cike da dariya duk da ba'ajin abinda ake cewa Amma yafahimci maganar qarshe "tabbas lokaci yayi hhhhh"abinda ya iya ji kenan kafin daga bisani kogon yakama da wani irin haske wanda ya kusa kashemasa ido daga bisani kuma yadawo normal hasken dazaka iya ganin komi aikafin yagama tinanin hanyar dazebi domin gano d'alibansa tini yaji andamqesa tabaya kamar yacce akawa jawahir nan take yaji ad'auresa da wata iriyar sarqa,iya qarfinsa ya gwada Amma yakasa kwance kansa jiyay kamar iska and'aukeshi timm yaji an ajjiyeshi awani d'akin wanda d'akin duk yashine aciki,se wata qatuwar randa agefe se kwarangwal wanda duk ba qashinma yadawo qasa.

"Yareema irfan!!!"muryar jawahir yaji ta daki dodon qunnensa yayin dayaganta atsaye akansa idonta ya sauya zuwa blue ,cikin mamaki yake kallonta yarinyarnan ya akai ta sauya!

"Wannan lokacin muke jira tsawon shekara da shekaru har shekaru dubu biyu,abaya anrusamana muradi Amma ayau qarshen jaririn randa yazo,munada qarfin dazamu iya ja dashi!!!"

Aikafin ta rufe baki ji sukai ankuma yin wata dariya irinta ta tashin hankalinnan harseda kogon ya amsa!!!

Shikwa malam irfan daya zuba ido yana kallonta cike d mamaki dan yanxu y'a tabbatar batada hankali ko aljanu sun shafeta danshi besan akanme take maganaba,cikin sigar tausayamata yace "jawahir bamuda lokacin wannan shirmen kiyi qoqarin kwanceni mu Nemo'yan uwanki mufita daga gurinann .

Ai wata tsawa tadakamai tace "yareema irfan !!!! Qasaitar gimbeeyar jawahir karkace ka salwantar da ran d'anmu annur !!! Kafahimci ko kai waye "

Aikafin ta ida maganar jitai an wurgi da ita kanta yadaki bangon randar wani qaqyacewa da dariya aka kumayi harseda jini ya zobamata kafin t wad'o qasa sumammiya,nan take hankalin malam irfan y d'ugunzuma ainun ganin abinda yafaru nan danan idonsa yafara masa gizau,bashiri ya rintse idanunsa tare da bud'esu ahankali cike da iko d izzah irin ta yareema irfan,duk sarqar dake jikinsa be hanashi qarasawa wajen jawahir ba,tallafota yay ganin kanta na zubar da jini yana "yake gimbeeya ta me qarfin iko kitashi domin cikar qudurinmu,karki bari tasirin shekaru dubu biyu su shud'e anan "

Amma ina jawahir ko motsi nan take randar nan tafara wani irin girgiza jaririn randa Ke qoqarin fitowa yana kyakyacewa da wata irin dariya,yayinda yareema irfan keta qoqarin tashar da gimbeeyarsa,aikafin ya farga yaga d'aya daga cikin d'alibansa wato ablah kabir tazo ta tsaya daidai saitin randar kana daga bisani ta cakawa kanta wuqa aciki ai firgici da mamakine yasashi saurin miqewa tsaye yana "keeeee ""Amma ina tini ta caccaka wuqa acikinta banda jini ba abinda Ke kwarara Amma da zarar ya sauka qasa sekaga anzuqeshi ,kan gawar tata yazo yana me d'agata Amma ina ta sheqa wata iriyar qara yasaki wacce tafarkar da jawahir daga dogon suman datayi yayinda jaririn randa Ke ta tsala uwar dariya....

Kafin kace me ye sega mansur ayub shima d'auke da sharb'ebiyar wuqa ya tsaya daidai saitin randar aiba shiri yareema irfan ya sufa ya riqo hanunnunsa,yayinda yake qoqarin cakawa kansa wuqar suna cikin wannan kokowarne sega yusif bashir yanata caccakawa kansa wuqa agaban randar kafin gimbeeya jawahir ta qarasa kansa ya wad'i matacce yayinda aka zuqe masa jini,ai da saurin irfan yayo wajenta suna had'a ido gaba d'aya sigarsu da kamaninsu suka canja zuwa na asalin gimbeeya jawahir d yareema irfan,tini idonsu ya bud'e aljanune kala kala agurin suke shanyewa yaran jini ,ga yarannan kuma ajere sunbi layi kowanne da wuqarsa ahannu,kallo d'aya sukaimu su gaba d'aya sihirin jaririn randa ya sauka daga kansu,suna dawowa hayyacinsu sukai wurgi da wuqaqen yayinda sukai wuri-wuri ganin malam irfan awane irin shiga......

Ai aunty hibba tindaga nesa tasan lalle ba makawa wannan shine kogon junoor dan tashafe awa tana bulayi adajinnan bataga komiba se wannan kogon aikwa batare da tinanin komiba ta dunfari gurin ,kogon junoor dake jiran jinin d'an adam aitini ya jata.

Sun kasa cemasa komi shima haka be cemusu komiba sedai kallo da ido dan baze iya tina suwaye su agurinsaba gaba d'aya tinaninsa ya sauya haka jawahir cikin izza da isa tacemusu kobiyone suma da mamaki yasandarar dasu atsaye basu musaba suka bita ai wucewarnan da zasi suka ci karo da gawarwakin'yan uwansu akwance wani ihu suka saki me cike da razani tsawa yareema irfan yadakamusu yana "kumana shiru!!!" Gumm sukai da baki tare dabin bayan Jawahir inda take musu jagora wani d'an kogone aciki me d'an zurfi ta musu nuni dashi tace"kushigane komi ze faru karku sake kufito!!"kunjiko

Alamu dakai kawai sukamata na EH sun gane danyanxu sun tsorata dasu gaba d'ayansu...

——tasssss tassss qarar tsagewar randar kakeji wanda gaba d'ayan dajin falgore amsawa yake bare kogon dayake wani irin girgiza ,Durummmm kamar tashin bomb haka rigar fulaninnan sukaji ba wanda be farkaba haka b'an garen d'aliban da gudu kowa yafito daga tint d'insu dan qarar tayi yawa harta wanda suke nesa da dajin hakan be hanasu jiyo qarar ba.

Aunty hibba dayake kwance ayashe acikin kogon itama qarar ce tadawo d ita hayyacinta,idonsu beelal adam dake cikin kogon da jawahir ta zubasu yay qulu-qulu meke faruwa,gashi ance karsu fito Amma da alamu kogon junoor ze ruso akansu....

Read and share

SHU'UMAR IZZAH Where stories live. Discover now