Sun taso cikin tsananin talauci da azaban rayuwa, sun rasa mahaifinsu a lokacinda sukafi bu'katanshi sun shiga wahalhalun rayuwan inda 'kaddara yayita walagigi dasu. Canjin rayuwan data samu yasa ta manta asalinta da yanda ta fito tayi watsi da daman data samu daga 'karshe ta tsunduma cikin tafkin nadama da dana sanin da bai mata amfani ba.