KAMA DA WANE....(Completed)

بواسطة Seemahwrites

13.2K 1.8K 210

even though they look alike that doesn't mean they should have same goals, their life is filled with regret... المزيد

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 12
chapter 11
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
Apology
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
chapter 46
chapter 47
chapter 48
chapter 49
FINAL
Trailer

chapter 17

233 38 19
بواسطة Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤
👩🏻KAMA DA WANE......
BATA WANE👩🏻‍🦱
💙🖤💙🖤💙🖤💙🖤💙

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*Na*
*UMMU NAJMA*
marubuciyar *HAR ABADA*

*DEDICATED TO*
*AMMYN KHAIRAT(golden girl)*
*AND RUKAYYA IKRA(ummu sultan)*

Wannan shafin naku ne 'yan uwana not related by blood but by a strong bond that cannot be separated 💞

*Fatima batula(Mrs balarabe)*
*Yar Umma*
*Fatima shu'aib*
*Matar Soja*
*Nimcy sarauta*
Jinjina gareku marubutan qwarai 👍🏼

17👯
"Me zakayi dashi?"
Ta tambaya tana binshi da wani irin kallo,

"Na roqe ki Haleesa dan Allah ki bani na gani, dan Allah ki taimake ni ki taimaki rayuwa ta please"

Ganin Yanda ya marairaice yasa tasan akwai wani Abu a qasa, a iya saninta Sa'ood dan fashi ne Kuma shugaba ta fada Mata sarqan su gold ne mai tsada, ta yuyu Yana so ya qwace ya siyar ne kaman Yanda yake yi ma sauran mutane Kuma wannan necklace din shi kadai ne abin da ya rage Mata Wanda zai iya sada ta da iyayen ta na gaskiya,

Cire sarqan tayi daga wuyan ta, ta zare pendant din jiki ta dunqule a hannun ta na hagu sannan ta miqa mishi zallan chain din yayi saurin karba Yana qare Masa kallo,
" Haka sarqan yake babu wani Abu a jikin sa?"

Gyada Kai tayi tace " eh haka uwar goyo na ta bani shi"

Sauqe numfashi yayi ya miqa Mata chain din ta karba sannan ya wuce cikin daki Yana Jin ana kiraye kirayen sallah, ya dauko first aid box ya zauna Yana tunani, Yaya ma za'ayi wannan yarinyar ta kasance Sarwa?

Ya yarda tana Kama da dady aliyyu tun ranar da ya fara ganin ta Kuma shekarun ta daya da Sarwa sannan sunan ta daya da Haleesa, Amman Ai su biyu ne ita Kuma ita daya Kuma bata taba ambatan tana da twin sister ba saidai qanwa, a iya sanin shi mamanmu Bata sake aifan wata yarinya ba Bayan su,

Yana zaune Yana tunani ta shigo ta zauna dan nesa dashi sannan ta dauki cotton wool ta zuba spirit a kai Dan taga haka Mai chemist yake yi idan mutane sunji ciwo, ta Kai hannun ta saitin fuskar shi zata fara goge Masa a dan firgice ya dago Yana kallon ta,

Wai qoqarin taba shi fa take da sauri ya ja baya, ai shi dazu bisa kuskure ya kusan taba ta shine ita kuma zatayi Masa na gangan?
"Ki bari kawai zan iya da kaina" ya fada hade da karban audugan hannun ta Yana goge jinin fuskar shi,

Kaman daga sama yaji muryar ta tana tambayar "Mai yasa dazu ka damu da kaga sarqan wuya na?"

Bai dago ba yace "saboda na dauka na Sarwa ne"

"Wacece Kuma sarwa? Yaya za'ayi sarqan ta yazo wuya na?"

" Qanwata ce da Kuma matata"
" Ban gane ba itan guda nawa ne Haka da har take da matsayi biyu a wurin ka?"

Dan dagowa yayi cikin gajiya da tambayoyin ta yace
"Ai kuwa ba Zaki taba ganewa ba Dan ba abinda ya shafe ki bane, na riga na fada Miki Sarwa qanne na ne twins da Haleesa da Saleeha amman ke ba a cikin Mailafiya family kike ba shiyasa baki San abin da ya faru da su ba kuma ba Zaki sani ba"

Dumm_dumm Haka qirjin Leesa yake bugawa, did he just say their names? Tabbas sunan su ya ambata ita da Salee Kuma yace Suma twins ne and akwai MAILAFIYA a jikin takardan da aka tsince su dashi ga Kuma sarqan ta da ya rikice da gani, what if Sa'ood yasan iyayen su yasan inda suke a halin yanzu?

Tashi yayi zai Shiga toilet tayi saurin Shan gaban shi cikin inda_inda da rasa Yanda zatayi ta tambaye shi ya fada Mata wani Abu a Kan Sarwa tace
"Ttt...to..to su sarwan a Ina suke? Kuma Mai yasa Kai kake zaune Kai Daya baza ka koma cikin 'yan uwan ka ba? Baka zuwa wurin qanin ka Kuma shima ya tafi wani gari Yana zaune shi kadai, Baku da wasu 'yan uwa ne kuke wargaza kanku Kuna wargaza al'umma? Kai kayi destroying rayuwa ta da na sauran mutane shi Kuma yayi destroying na qanwata"

A tsawace yace "shut your mouth up Leesa, duk banzan maganar ki ya tsaya a kaina kada ki kuskura kiyi dragging Sa'eed a ciki, ni nasan ba mutumin kirki bane Amman definitely Sa'eed mutumin kirki ne kawai kuskure yayi Wanda ba zamu iya yafe mishi ba shiyasa Kika ganshi cikin wannan yanayin Amman ya fiki gata wallahi"

" Tabbas na yarda ya fini gata tunda ni iyayena watsar dani sukayi suka tafi, maganar shi mutumin kirki ne Kuma bani da tabbaci a Kan hakan amman Abu daya da na sani shine kaima ba mutumin banza bane, kana daukar bindiga ka cutar da mutane Amman daga qarshe kana finsu Shiga damuwa a dalilin hakan, shiyasa na tabbatar cewa there is a hidden secret about you and your family

Duk wani halin banza bakayi, baka wasa da sallah, baka Shan giya, baka Zina Kai de matsalar ka daya ta'addanci, kuma na dade sosai Ina zaune a gidan Nan Amman baka taba qoqarin cutar Dani ba ko sau daya saima kulawa Dani da kakeyi I feel more safe when I'm with you fiye da lokacin da nake gidan aiki na ko gidan riqo na, meyasa duk hakan suka faru ne? Meye dalilin ka na sato ni ka ajiye ni a nan?? I need to know please"

Kawar da kanshi yayi Yana qoqarin boye yanayin da yake ciki yace "ki bani hanya, jam'i zai wuce ni"

batayi musu ba ta matsa ya Shiga, ba dadewa ya dauro alwala ya fito yadan kalleta a kaikaice yace "ki tabbatar kinci abinci kinsha maganin ki kafin na dawo inaso idan kin warware zanyi Miki bayanin tambayoyin da Kika min"

Yana fita Leesa tayi kaman Yanda yace, ta kintsa jikin ta sannan ta dawo parlor tayi zaman jira Dan ta qagu taji labarin Sa'ood maybe suna da wata alaqa da bata sani ba,

Sai Bayan Isha ya dawo ya zauna a kujeran dake gefen nata ita Kuma ta zuba mishi Ido tana sauraro,

Dan nisawa yayi yace "kafin Nan Mai ya gudo dake daga gidan Habib"

Yamutsa fuska tayi tace " 'dan iska ba, keta min haddi yaso yi shine Nikuma na keta mishi hannu na arce abuna, sunce Wai zaije gidan mu Amman shiru har yau bangan shi ba ko dayake Yama San gidan mu ne? Iyakaci ne idan ya bincika a gwada mishi gidan su Ameerah...... Wait, Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un na tafka babban kuskure yanzu idan yaje gidan su ya cutar da su fa? Wayyo Allah na wallahi na sha'afa ban taba tunani a Kan wa'inda suka taimake ni ba, yanzu idan ya cutar da ita fah? Dan Allah kayi wani Abu a Kai ka taimaka ka kubutar dasu please nasan zaka iya"

" Shikkenan in Allah yarda gobe da safiya zan saka aje a dubo su kada ki damu,

And about Sarwa and my family, bansan dalili ba Amman na tsinci kaina da son sanar dake abinda ya shafe ni Amman inason hakan ya zamo wanke tabo da baqin fentin da kike ma 'dan uwana da ni kaina, maybe idan na cika burina na maida ki gida ba Zaki sake gani na ba HAR ABADA,

________________
*MAILAFIYA FAMILY*

Babban jigon wannan zuri'a shine Baba alhaji Wanda cikakken sunan sa Al-ameen khalifa Mailafiya, duk cikin yaran mahaifiyar su shi kadai ne mahaifin shi daban, Bayan Allah yayi was mijin ta rasuwa tayi aure a cikin Mailafiya family ta aife shi dan haka shi kadai ne magajin arziqin uban shi Kuma tunda ta aifeshi Bata sake aihuwa ba,

Al-ameen ya tashi cikin tsananin gata dukda sauran 'yan uwanshi ma mahaifin shi ya dauke su kaman 'ya'yan cikin sa amman nashi gatan daban yake,

A lokacin da Al-ameen ya girma karatun gaba da primary baiyi qarfi ba hakan yasa baban shi ya tura shi Mexico yaje yayi karatun shi har masters kafin ya dawo aka ya auri kyakkyawqn budurwa Mai suna Maryam (hajiya),

Zaman shi da Maryam yayi kyau alhamdulillah Dan rayuwa sukeyi a waye Bata yarda ta aihu ba ma Saida ta shekara 4, tashin farko Allah ya Bata 'yan biyu kyawawa duka maza saidai kaman su ya banbanta,

Babban yaci sunan baban Baba alhaji wato Khalifa qaramin Kuma yaci sunan baban Maryam Aliyyu hydar, Bayan haihuwar su day dadewa ta sake aifan da namiji Ishaq sai Kuma mace Mai suna Siddiqa,

Su khalifa suna Gama primary Baba alhaji ya tattare su ya tafi dasu Mexico harda Siddiqa da ko makarantar Bata fara ba, Basu dawowa sai anyi hutu,

*MAILAFIYA MANSION*

Gida ne babba da ya qinshi duk wani member na Mailafiya family suna zaman su cikin lumana da kwanciyar hankali domin Basu cika auren Mata sama da 'daya ba saboda tsantsar boko da rayuwar turawa da suka dauka suka daura ma kansu babu lamarin addini cikin lissafin su,

A cikin gidan babu takuri Koda tsakanin uwa da 'da ballantana 'dan uwa da 'dan uwa, a Yanda suke cewa ana bawa kowa 'yancin sane so ya rage naka kayi Mai kyau ko marar kyau su dai kada ka jawo musu abun kunya da zagi Amman Bayan haka kowa yayi komai ba komai (wa iyazubillah),

Saboda tsananin dukiya da suke dashi yasa suna da kadarori masu tarin yawa, tun daga Kan asibitoci makarantu da sauran su sai a qarshe suka kafa babban qungiya ta marayu suka bude musu qaton wurin da zasu dinga rayuwa Wanda ya kusan cinye unguwa guda,

Marayu kusan 500 suka riqewa a lokaci daya su riqe su, su Basu ingantaccen ilimi su koya musu sana'a idan suka Kai munzalin aure a tantance mazajen da suke son aura ayi musu aure, idan Kuma maza ne a nema maka wurin zama a baka aiki shikkenan sun yaye ka, Kuma duk lokacin da wani ya ragu za'ayi replacing dinsa,

*MAILAFIYA ORPHANAGE*

Shi ya zamo kaman gida na biyu ma 'yan familyn dan ko wani weekend Wanda suke qasa, yara da manya zasu tafi wurin tun da safe ba zasu dawo ba sai Bayan sallan Isha, a wurin ne masu niyya suke karatun alqur'ani idan anzo yi ma yara,

Tun Aliyyu nada shekara 22 Allah ya jarabce shi da son wata yarinya a orphanage din Mai suna Hafsat yarinya qarama 'yar shekara 15 Mai tsananin kawaici, alkunya da haquri, gata da tsafta tana da haske Amman Bata da wani tsananin kyau,

Tun Hafsat na Bata San kanta ba tana share Aliyyu har ta fada tarkon sonshi saboda tsananin naci da kyautatawa irin nashi Dan kaf orphanage din saida kowa ya shaida Yana nemanta don bayi kunya a gaban kowa Yana alfahari sosai da ya kasance shine dai mallaki Hafsat,

Duk Yanda akayi da Aliyyu ya koma Mexico haka qememe yaqi, kullum Yana wurin Hafsat haka zasu zauna suyita shiririta ma juna don komawa yake yi kamar yaro sa'an ta yayi ta Mata shirme,

saidai fa duk wannan guguwar love din dake diban su Hafsat Bata yarda Aliyyu Yana tattaba ta dan ko yaushe malama tanayi musu nasiha Mai ban tsoro a Kan haramcin tana matar da ba Muharraman ka ba ballantana har shaidan ya Shiga tsakani kuyi aikin da na sani,

Saida yayi shekara 1 a Nigeria sannan baba alhaji ya 'dan takura da maganar komawan shi, ai kuwa yace shi idan babu Hafsat babu inda zaije indai ana son yaci gaba da karatu to a daura musu aure ya tafi tare da ita,

Bai samu wata matsala ba aka yarda da zancen auren su dukda basuji dadin hakan ba dan ita ba 'yar kowa bane, sunfi son a dinga yin qwarya tabi qwarya gaba da baya yaran su su gaji arziqi,

Ganin haka yasa khalifa ma yace aure yake so ya fitar da budurwan sa Zainab 'yar shekara 19 itama baban ta wani babban qusa ne a qasa, Haka akayi auren rana daya khalifa da Zainab suna zaune a Nigeria saboda shi ya kammala karatun shi zai fara Shiga business dinsu shima ana damawa dashi Aliyyu Kuma ya hada takardun Hafsat suka tafi Mexico ya saka ta a makaranta,

Rayuwa na tafiya a hankali wataran farin ciki wataran akasin haka, amare na zaune lafiya a gidajen su saidai har suka cika shekaru 2 babu Wanda ta aihu, Hafsat Aliyyu ne take Bata maganin hanawa saboda a irin shekarun ta Yana tsoron wani Abu ya same ta, Zainab Kuma har yanzu tana cin amarcin ta ne batayi Shirin aihuwa ba tukunna,

Sosai Hafsat ta dage a karatun ta tana hadawa da koyon yaren Spanish dan shi aka fi yi a nahiyar da suke, a farkon shekara na uku da auren su Bayan ta Shiga aji daya a university ta samu ciki, saidai Allah baiyi ta Mai yawan laulayi ba, Banda kwadayi da tsananin ci sai fitina babu abinda take fama dashi,

Haka take tutturawa ta tafi makaranta da himilin kayan qwalama cikin jakar ta ana karatu tana tauna har ta kusan Shiga watan aihuwar ta kafin suka dawo gida Nigeria har lokacin Zainab babu labari,

Bayan sati 3 da dawowar su Hafsat ta aifi 'da namiji Wanda yaci suna Idris, saidai Kuma ta samu matsala sosai wurin haihuwar don likitoci sunce mahaifar ta bayi da qarfi da sunsan da haka tun wuri ba zasu barta ta aihu da kanta ba, suka shawarcesu da su dakata da haihuwa na wani lokaci idan ba Haka ba za'a iya samun matsala don ba lallai yaran suna zama ba, dukda Haka anyi bidiri a sunan Idris Kuma family sunyi ma Hafsat kayan bajinta na gani na fada,

Bayan sunyi 40 Aliyyu ya tada maganar komawar su suci gaba da karatu tunda jikin ta da qarfi haka kuwa akayi ya dauke ta aka nema musu nanny suka koma Mexico, iya bakin qoqari Hafsat nayi wajen kula da Idris, dan dukda fitinanne kunyar da take dashi haka ta yakice shi ta ajiye a gefe take bawa danta kulawa ta musamman,

Tafiyar su da wata 5 khalifa ya Kira Aliyyu yake shaida Masa Zainab tana da ciki, dukan su suka tayashi murna sukayi Masa Allah ya Sanya alkhairi, saidai Rana daya lokacin cikin Zainab nada wata 7 aka wayi gari babu khalifa Allah yayi mishi rasuwa cikin dare ba tare da sanin su ba.................🧚

#vote
#share
#comment.

واصل القراءة

ستعجبك أيضاً

3.9K 451 18
If there is any part of you that makes you think I will ever fall for you then that part ........"shhhh" he said cutting her shut, pressing his index...
33.6K 2.9K 27
အချစ်ရူးနှင့်တော်၀င်ပန်း
356K 21.8K 37
Let's see how different personalities mends with each other to form a beautifull bond together. Where the Eldest is calm and cold, Second is aggress...
49.6K 1.1K 32
It had been mere months after her eighteen birthday, when she was pulled from the safe haven of her life and forced into the fantasy the women had cr...