SADAUKIN BURHAAN CIGABAN IZZA...

By JameelarhSadiq

198 7 2

Kamar yanda kuka sani Labarin Izzah ko mulki labarine wanda ya kunshi mulki na zalinci, ga cin amana ga kuma... More

5&10
Komai yayi farko yana da karshe

1&15 idan zakuji inda Saudaki zaije da inda shetima zai kai Asma'u

117 4 2
By JameelarhSadiq

⚔️SADAUKIN BURHAAN ⚔️ _(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_

A Kingdom Story👑

    *NA*
*Jameelah Jameey*
 
*Ya'r mutan kankia ce❣️*

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOC*

'''kungiya d'aya tamkar da dubu.🤙'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_____________________

*Marubuciyar👇*
*NANA JAWAHEER*
*GIMBIYA HAKIMA*
*IZZAH KO MULKI*
*SANADIN LINK*
*A GIDAN HAYA*

            
              And know

*SADAUKIN BURHAAN*_(daukar fansa cigaban Izzah ko mulki)_
             

*BISSIMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*
_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI_


_Godiya ta tabba ga Allah dayasake aramana lokaci mai tsada a karo_ _na biyu da muka sake haduwa daku a cikin wannan kayataccen labarin mai_ _dinbin tausayi da ilmi na rayuwa wanda ya kunshi tuggu_ _da zalinci na gidan sarauta......inafatan Allah yahadamu da mafificin_ _alkhairyn dake cikin_ _wannan labarin_


'''Karda ku manta wannan labarin dai kirkiraran labari ne kamar yanda ba fada maku abaya,tun farkon labarin.....'''

*Jinjina da tarin godiya ga masoyana naga adduarku marar iyaka* *Allah yasaka maku da alkhairy, Allah yabar kauna ina tareda ku iya* *wuya muna* 🤝🏻

_Kada kuman wannan book din na kudi, kamar yanda na barmaku wancan a #100 kacal VIP_ _kuma #200,toh wannan karanma duk domin ku masoyana (Daukar fansa) ma a naira #300 kacal zan_ _baku shi yan VIP kuma naira #600,duk mai bukata yaima wa'annan numbobin magana_ _07034464517 ko 08160508316_

Note:- kar yarinyar da sake tayi man magana indai ba saye zatayi ba thanks.

_Free Pages_

_Page 1 to 5_



"Allah yaja da kwanan Gimbiya ta kiranki ya riskeni.....wani irin wulakantaccen kallan da tayimashi saida yasaAdo wani irin mummunar faduwar gaba kamar yai fitsari a tsaye haka yaji baki daya jikin shi ya hau bari baisan sadda ya sake zubewa kasaba yana neman afuwar taba....cike da gadara ga wata irin masifaffiyar izzah da takeji duk a lokacin ta fara magana cike da miskilanci da nuna karfin ikon mulki....."sai yanzun kaga damar zuwa"? Yana ta bari yace." Mai Martaba ne ya tsayar dani dan Allah ki mani aikin rai."cewa tayi. "Dallah karka cika da wadannan munanan maganganun naka masu saka mutun ciwon kai."...."Tuba nike uwar gijiyata kimin aikin rai."cewar Ado... Cigaba da cewa tayi."labari ya sameni ance gobe zakuje kasuwar gobir siyan bayi,in kunje inasan ku dubomani bayi guda biyu masu aminci mace daya namiji daya, karka kuskura ku kawo mani raggon bawa, muddin hakan takasance wallahi kashinka ya bushe, in kunne yaji."?

_Hmmm lallai kam wani aikin saike gimbiya Zubaina kenan itake_ _wannan zancen ko za'a dace da jajir taccen_ _bawan da take bukata....._

"Allah yataimakeki bazaki sameni da sabama umarnin kiba zan jajirce in samu maki bawan da ya dace dake wannan hakkina ne a matsayina na masu kula da bayi masu nagarta da inganci."..cewa tayi."ya rage ruwanka zaka iya tafiya."..Tashi yayi yana cewa."Allah yakara girma da nisan kwana ki huta lfy...."



Gabaki daya wajen kowa ya kama kanshi dan sunga duk takara canza masu sun rasa kanta bata dagawa kowa kafa kaf cikin ZAIRANA labarin Zubaina ya karade kowa shakkunta yakeyi tin gimbiya Amina na kwatan tamata harta kyaleta, saboda Mai Martaba baisan ana takurata ya dauki san duniya ya daura mata kasance war yanzun ita kadai yake yawan gani a cikin ya'yan shi......

               _BURHAAN_

Izuwa yanzun Masarautar Burhaan ta rikice ba abinda ake yi sai mulkin zalinci da kaskanta mutane kamar ba gobe duk abinda bayin Masarautar zasuyi basuyin dai dai daga bugu sai aikin wahala ba sauki hatta masu mukamaima basuyin wani motsin kirki....gimbiya Saude ke ba baiwarta aikin gyaran lambu kasancewar bata san kowa na zuwa lambun ta inba wanda ta aminta da shi ba wannan baiwar na cikin aiki tana rage ciyawo kawai saitaga wasu irin manyan bakaken layu....ba karamin tsorata tayiba har saida ta buga uban ihu.....



Da sauri gimbiya Saude ta shigo ta iske wa'annan layyun sunata hayyaki batasan sadda ta cacimi wuyan baiwar nan ba taita duka kamar zata kasheta wani irin kuka ta fashe dashi mai cin rai tanaji tana gani aikinta ya lalace.....saboda ba'asan kowa ya gansu muddin sukai kwana bakwai a binne Sarki Abduljalaal zai mutu....data gaji da dukan baiwar janta tayi kasa ta ha data da Barde daman yagama fita hayyacin shi takaita ta baro mashi ita yai ta dukanta kamar zai kashe ta can ya afkama baiwar nan yai mata fyade saida yaimata kaca kaca jini kawai ke zuba daga kasanta nan yabarta a ya she kamar zata mutu numfashinta na fita sama sama kuma baifasa bugun baiwar nan ba ranar haka yaita haike mata cikin kankanin lokaci numfashinta ya dauke baki daya....wannan kenan

Fa'da tunda galadima Hamza ya shigo fa'da yaketa kankanci ga wukanta mutane yanayi ya hana kowa magana saidai ido sarkin taska ya kira yace yana bukatar ya fiddo foam dubu dari kawai abubuwan da yakamata ace anyima Masarautar Burhaan.....tunda Sarkin Taska yace kudin dake hannun shi bazasu isaba saboda ya karbi kudade a hannun shi ai ko kulle bakin shi Hamza bai bari yayi ba ya haushi da bugu yace sai ya fiddo ma fa'da kudade shiya cinye kudin Burhaan yanaji yana gani Hamza ya hana shi magana daga karshe yasa akai ram dashi sai gidan yarin gilba......

"Hmmmwallahi kadan kuka gani da sannu sai namayar da kowa cikinku abin tausayi a cikin Masarautar Burhaan koda dan uwa nane Abdullahi da Hamza Muhammad kuke magana matsiyata daku."cewar Hamza a cikin zuciyarshi bayan ya gama cima Sarkin taska mutunci.

_Allah ya kyauta wannan wane kalar zalinci ne anya Masarautar Burhaan akwai Allah a cikin lamuranta_ 🤔

Haka kowa yakama gaban shi hartakai ga yanzun kowa na gudun zuwa fa'da gudun kar Hamza ya wulakanta mutun ko ya janyo wani sharrin yace kai kayi dan yaci mutuncin ka ko Abdullahi shima baicika san zaman fa'da ba saboda ya fahimci ba wanda Hamza bazai iya wulakanta waba baki daya Masarautar Burhaan......



Yau kimamin kwanan su Sadauki ukku suna tafiya kuma duk a kasa suke janshi in sun tsaya to abinci zasuci suma sai sunci sun rage su yammashi ko ruwa diga mashi sukeyi a baki ya hade baki daya yagama galabaita ko bacci aka kwanta shi baida arzikin ko mayafin dazai shimfida haka zai kwanta kasa kamar marar galihu basu suka isa gobir ba sai wajen karfe biyun rana sadda suka isa Sadauki yagama galabaituwa da duka jikin shi duk sahun duka nan suka kama hanyar zuwa kasuwa suna isa suka samu waje daban suka sa igiya suka daure kafar shi kamar wani rago, tunda aka shigo dashi mutane sukai ta ribibin shi kamar sunga nama kowa so yake ya siye shi bare yanda suka ganshi jayant gashi kyakkyawan gaske a kankanin lokaci anfasama masu Sadauki kai akazo akasa gasa ta kudi tashin farko foam saba'in aka taya Sadauki, amma sukace albarka wani yace tamanin nan ma sukaki harda wanda yace foam dari amma sunce albarka  basu taba kawo bawan dayakai darajar foam talatin ba tunda sukaga ana ribibin sayen Sadauki sai suka kara daura guri akan shi kowa yaki yarda ya hakura da cikin shi, kuma sunki sallama shi har dare yayi anki karasa cikin Sadauki aiko cikin kankanin lokaci wajen yayi tamkam da mutane kowa yana son yaga wanene wannan bawan mai farin jini har haka duk wanda yaga Sadauki saiyaji tausayin shi ya kama shi dan daganin shi ba ainahin bawa bane jikin shi yasaba da hutu,shiko sai binsu yake da ido kamar wani gele kamar wasa wajen ya makare da mutane har ankai foam dari da hamsin amma sunki siyarwa......kafin kace me sai aka fara sanar da isowar mutanen Zairana tunda Ado yayi ido hudu da Sadauki yaji ya bala'in shiga ranshi da ganin shi zaiyi juriya da yawa aiko ya shiga fafatawa a cikin masu gasar cikiniki.....tashin farko foam dari biyu yasa Sadauki duk wanda ke wajen nan saida ya tsaya ya kalli Ado wani irin girman kai ya sake hawan mutanen da suka kawo Sadauki nan suka ce albarka Ado yasaka kallan Sadauki da kyau yace aran shi konawa akasai wannan bawan baa fadi ba ya hada komai kyawu da kwarjini bai musaba yace yasa shi foam dari biyu da hamsin baki daya wajen nan yahau ihu dan duk wanda ke wajen yakasa ja da Ado.....koda suka ga kowa ya gaza sunsan bazasu kara samun sama da cinikin Ado ba, nan suka amince ya fiddo kudin su ya basu, suka kwance shi nan ya tambayi sunan shi dayake sun rude saboda sunga kudi suka ce sunan shi UMAR ba karamin dadi Ado yaji ba yakama hannun Sadauki yaje ya saimashi abinci ya bashi kamar tsohon mayunwaci haka Sadauki ke hannu baka hannu kwarya har kwarewa yake kaikace wani zai anshe mashi sannan yaba shi ruwa ya sha.....cikin yan mintoci har Sadauki yayi bacci shidai Ado yarasa dalilin dayasa Sadauki ya shiga cikin zuciyar shi a lokaci daya......nan suka tashi ya ida siyan bayin su da mace guda daya da ya siyeta a foam saba'in sunanta Hafsat, nan suka samu waje suka kwanta shi da mutanan shi kowane bawa na kwance waje amma ya shigo da Sadauki cikin daki a shimfida daya suka kwanta kowa saida yaimamaki amma bata magantuwa sunyi tunanin kodan ya siyeshi da tsadane shiyasa yake bashi kulawa.....nan kowa bacci ya dauke shi tunda sukai asibar fari sukai sallah kowa ya hau dokin shi suko bayi suka daure su a jikin doki da igiya, koda wani babban bawa yazo daure Sadauki hanashi Ado yayi saida kowa yayi mamaki daura shi yayi agaban dokin shi, duk da banisa sosai da Zairana a cikin yini daya suna iya isa take saida hassada ta shiga a tsakanin bawannan da Sadauki nan suka cigaba ta tafiya zuwa ZAIRANA.....


Sarki Abdulbaseet Abdulkarim ne zaune acikin falon shi baki daya yarasa mike mashi dadi yaji Masarautar Burhaan ba amo ba labari tunda akayi bikin su Asma'u ba Mardiyyah bare yasa ran ganin ko Sadauki ne yazo kullun dasu yake kwana a cikin yarasa me ke mashi fadi a rayuwar shi ta duniya hakan yasa ya kira gimbiya Zainab yaimata bayanin komai itama dama ta shiga cikin damuwar jin shiru harhaka nan tace."yaka mata kai  kaje da kanka kaji ko lafiya.....nan yace."zan fara tura dan aike daga bisani zanje da kaina dan ina cikin damuwa marar misaltuwa."..... Itama bangaren Umm Aisha lamarin duniya duk ya tarar mata yaimata yawa ta rasa abinda ke mata dadi a duniya intayi magana sai mijinta yace ta cika san ya'ya Mardiyyah tafita kawaici da sanin ya kamata tanaji tana gani saidai tasa ido amma kullun tana cikin damuwa gashi ya hanata zuwa Burhaan yace sai Asma'u ta haihu sannan zataje baki daya.....



A bangaren Mabaruka kuwa kwance take da katoton cikin ta saiga Haidar ya shigo cikin dakin ya dauke ta kamar wata jaririya ba inda ya direta sai toilet yaimata wanka kasan cewar bata lafiya ya dauki san duniya ya daura akan cikin ta komai nashi ya kwallafawa cikin nan itako sai lemewa take tana shagwabar ta san ranta,saman gado ya direta ya dauko mai ya shafeta da shi sai shafa cikin yake kamar kwai da tayi motsi sai yafara riritata baki daya batasan yaimata nisa da kanshi ya saka mata kaya sai wasa yake da cikin sa jiyake kamar ya hade dan cikin ta zaunar da ita yayi a cinyarsa ya bata abinci sai kukan shagwaba take baki daya ya sussuce ba shiri ya hade bakin su sai kiss dinta yake itako ta lafe jikin mijinta kamar zaa kwace mata shi sannn ya dinga bata a binci tana ci a hankali harta koshi nan sukaci gaba da wasanni cikin so da kaunar juna.......su Ado ne basu isa Zairana ba sai karfe biyar na yamma ba inda suka wuce sai sansnin bayi wani katon wajene Sarkin gida ya damka ma bayin da kanshi ya basu masauki amma ya ware ya Sadauki da Hafsat ba inda ya wuce dasu sai wajen Zubaina kasan cewar tana cikin daki nan ya tsaya dasu falo,Fadila taimashi iso wajen Zubaina bayan minti shabiyar ta fito ta iske su tsugun ne, shiko Sadauki sai kalln falon yake tayi, kowa ya kawo gaisuwa ga gimbiya Zubaina amma banda Sadauk itako ta shafaa da kallan tsarin hallittar Sadauki da kyawun shi raban da taga kwakkyawan mutun kamar Sadauki bata iya fadar lokaci batasan sadda ta furta tubarakallahu masha Allah ba, hatta Ado saida ya kalli Zubaina saboda yasan halinta ba komaine ke birgetaba amma yai gashi tayi santin Umar....koda yake dole a yabada kalar hallittar shi saida Ado yakara magana a karo na ukku sannan Zubaina ta dawo hayyacin ta.....dayake sarauta jinintace take ta wayance ta fara masifa....."Ado wannan wani sakaran bawane da zaka kawomani amma bazai iya kawo gaisuwar shiba bayan kowa ya kawo tashi gaisuwa, uban wa yafi."? Cike da fargaba Ado yafara ma Sadauki fada sannan ya gaisheta da muryar shi mai karade zuciyar maza dik  da yana cikin ganiyar sihiri hakan bai hana muryar Sadauki fitaba kamar tada, wanda dole mai sauraro ya shiga taitayin shi,koda zaigadata iyani yace atakaice daman shi ba mai yawan san magana bane bare yanzun da baida control.....tunda ya furta kalmar inayi gimbiya Zubaina tayi mutuwar tsaye duniya tanasan jarumin namiji jajirtacce....koda kasan cewar Sadauki bawa,amma saida taji ya birgeta a karan farkon da da'namiji yafara birge Zubaina......saita basar tace ma Ado "daganin bawan nan akwai shi da girman kai kuma bazamu shiryaba amma inasan hudda da mutane masu nuna izzah kodan in gyara masu zama, menene sunan bawan."? da har Ado zaibata ansa amma ta dakatar dashi da alamu tafisan taji daga bakin Sadauki, amma kamar tana magana da dutse saidata ta daka mashi tsawa sannan ta maimaita tambayar ta..... Baki daya kwakwalwar Sadauki ta daure ya kasa tina komai amma unexpected yace "UMAR" yanda ya furta kalmanne cike da kasaita yasata rudewa.....tunda take bata taba ganin bawa mai nuna isaba kamar Sadauki saidai kace dan Sarkin Burhaan da yaya Ammar keta bada labarin shi......

_Af zancen kikeso Zubaina ance rashin sani yafi dare duhu kuma_ _karamin sani kunkumine....Sadauki ne yazama bawa......haka_ _rayuwa take_

Tunda ya fadi kalmar Umar ta rikinka maimai tawa amma saitaji da yafada tafi dadin sauraro....shi kanshi kallan kanshi yakeyi yanda yaji ta kara kiran shi da Umar alamun dashi take daman yaji kalmar ne a wajen Ado da haka yake kiranshi shima yake amsawa, dan haduwar Sadauki da Ado harya saki jikin shi da shi, ganin shike kautata mashi, itadai Zubaina saikara gayama Allah takeyi tsabar yanda kyawun shi ke fusgarta.....saita fahimci kamar tunda Umar yazo bai tsaya ya kalleta da wahala da hadu da mutane basu yaba kyawunta ba amma ta lura banda Umar kallan tama baiba bare ya yaba kyawunta, saima ita data bige tana yaban kyawunsa abunda bata taba yiba a rayuwar ta ta duniya ba sai yau.....kiran da tasake yima Umar ne yasa shi daga ido ya aza akanta, duk Sadauki nafama da halin mantuwa saida yaji faduwar gaba sake kallan Zubaina yayi amma sai ya samu kanshi da mulmushi....ba karamin shagaltuwa Zubaina tayiba da kallan Sadauki wani irin kayataccen kyaun sa yakara bayyana ga kwarjini da haibarsa duk sunkara bayyana.....ta rasa meke damun ta, saida tayi karfin zuciya sannan tacema Ado yabama Umar mai yimata aikin wanki, sannan ta tambayi sunan dayar baiwar tace Hafsat ita kuma tace ita zata dinga gyaramata daki, da kawo mata abinci, sai hada ruwan wanka.....sannan ta kalli Fadila wadda mamaki ya gama kamata ganin uwar dakin ta ta rude daganin Umar saikace wani mutun mai daraja gashi bata dauki bawa da kima ba....."ke kuma Fadila zaki cigaba da kula da lamurana na yau da gobe dani Kaina ya kamata ace iyanzun kin huta."....taimata godiya mai yawa, koda Ado zai tashi fada mata yayi yanda ya siyo Sadauki saida tayi mamaki, amma da takara kallan shi tasan yafi karfin foam dari biyu da hamsin koba komai Umar akwai kyau da tsari.....sannn ya fada mata  kudin da yasayi Hafsat tace ba laifi ai itama tanda kyau nan taimasu izzini suje su huta gobe sun cigaba da aikin su.......haka suka tashi kowa ya kama gaban  shi.....amma daki daya da Sadauki suka zauna shidai ya nasan Sadauki..... Ranar gimbiya Zubaina yini tayi da tunanin Sadauki a zuciyarta




Ba abinda kema sarki Abduljalaal dadi a duniya dan shi zuwa yanzun kaf lalurar shi bata damun shi irin bakin cikin bacewar dan shi Sadauki yasan yayi rashin jajir taccen da' gashi baida lafiya bare yabi hanya ko Allah yasa ya dace da shi a cikin duniya wannan lamarin shike sa Sarki Abduljalaal kuka da idanun shi, harya kai fagen da Saminu ya fahimci damuwar shi shikan shi lokaci zuwa lokaci inyatuna da uban gidan shi ya bata sai yayi kuka a boye gudun karyama Mai Martaba zuciya saidai yaita bashi hakuri akowane lokaci.....tunda Barde yagama haikema baiwar nan ashe rai yayi halinsa saboda azabar da tashi gimbiya Saude da Masau'da suka shigo wajen shi da niyar su saakaita gidan yari aikau suka tadda ta a ya she su kansu duk rashin imanin su saida suka kauda kai, bako daya jikinta jini ne sannan ya gama wulakanta tata, da sauri Masau'da ta isa ta dago baiwar nan kamar ta zubda mata hawaye dan kuwa Saude kasa isa tayi.....budewar bedroom din shi keda wuya yaga su Saude a falan shi amma ko kunyar su baiji bare nauyin su, haka yaimasu sannu sannan ya karkace su zai wuce aiko Saude ta rike shi...."haka nayi dakai?  bana ce ka ladabtamin itaba shine zaka haikema yar mutane."?kallonta yayi yana mata kallon banza yace."Dallah Goggo ki sakeni ko inshara maki mari harkin isa kitisani a gaba kina cewa na haikema yar mutane daman iman inda zan huta nike dole in shana da ita agabanki ma zan iya aikatawa bare bayan idonki, kuma wannan wulakanta tarbaiwar zakicema yar mutane, daga ita har iyayen ta wahalallu ne."..tunda Masau'da ta  fahimci Barde ya kashe yarinyar nan amma yake tada jijiyoyin wuya batasan sadda tazo ta wasga mashi mari ba saida ya gigice, cikin masifa Saude tace."dan mi zaki  mare shi? ba jika na bane?,dan yaimani rashin kunya ke yaimawa."? .... Tsaki Masa'uda tayi sannan tace."tafican sakarai dake, angaya maki danke na mare shi?  karewar rashin kunya koda zai maki yanda yaima wannan baiwar sai dai in kalla ko dungurin shi bazan yiba, na mareshi ne dan yasan abinda ya aikata ya munana tunda yarinyar nan ta rasa ranta ta sanadiyar  keta mata haddi da jikanki yayi.".. baki daya Goggo ta rude in wannan abin ya fita waje lallai zai taba darajar mulkin da dan'ta keyi, itama sake sama shi tafi tayi amma ko ajikin Barde cigaba da wake waken sa yayi ya fita ya barsu cirko cirko aiko Saude sai kuka take, itako gimbiya Masau'da zuciyar ta fas tasamu taban da zata yaki abokin gabarta wato Hamza dan taka fa tata sarautar tunda bata ita yakeba daga kauri sai guiwa.....

_Ikon Allah yauga soyayya ta zama kiyayya tsakanin aminan nan guda biyu_ _wato Hamza da Masau'da koya zata kaya kubiyoni sannu a hankali zakuji cakwakiyar_ _da zata wakana a cikin Masarautar Burhaan_

Baki daya Saude ta rike Masau'da tana rokonta arziki karta bari wannan  zancen ya fita, amma abin mamaki Masau'da tace."muddin Hamza bai dauki mataki akan dan saba saita tona asirin Barde ba Burhaan kadai ba saita yayata lamarin ya baje kaf kasar Cameroon."... lallai hankalin Saude yayi matukar tashi, dan duk jarabarta tana shakkar tsatson su Masau'da.....haka suka sabe sukabar sashen Barde a zuciyar Saude ko so take tana fita da dare tasa a badda gawar baiwar nan dan asirin jikinta dana mulkin danta ya rufu ita kuma Masau'da burin ta ta turo uwar bayi da wasu bayin sashen Barde da niyar gyara zasu ganema idanun su abinda ke wakana, tasan koda zaa kashe su bazasu yarda ba sai sun nemi hakkin su ita kuma intaga Hamza yaki basu hadin kai saita rubuta wasiku ta aikama sarakuna da sauran masu hannu da shuni tasan zasu tayata yakar Hamza kafin tafara turo mashi da bama baman asiran su......tana komawa da saurinta tasa aka kira mata uwar bayi tace taje da kanta itada bayi Barde na bukatar agyara mashi sashen shi, aiko batare da bata lokaci ba ta kwashi bayi har hudu sukaje sashen Barde sungama gyara ko ina suna zuwa karamin falo suka ga mutun yashe duk jini da sauri uwar bayi ta duba tana kallan fuskar ta taga ashe Yusrah ce mai gyarawa Sadauki daki, ba karamin kaduwa tayi ba baki daya wajen nan suka hau uban kuka kamar zasu mutu saboda yarinyar kirki ce, shiyasama Sadauki yace taciga da yimashi aiki, shi kanshi yarinyar taimashi ba ruwanta da son abin duniya kaf turakar bayi ba yarinya mai kamun kai, da sanin yaka mata ba kamar Yusrah nan uwar bayi tasa aka maida mata kayanta sannan ta fito ta kirawo wasu bayin suka dauke ta sai fa'da duk abin nan Masau'da na kallan bayin nan sai murna takeyi yau asirin Barde zai tonu suna shiga fa'da aiko dogarin Hamza ya daka masu tsawa amma sun rigada sun keke shi ko shakka babu a fuskokin su, hakan yasa Hamza ya daga mashi hannu sannan yayi shiru a tsakiyar fa'da suka shimfideta kallo daya Hamza yaimata sannan ya maida kallan shi ga uwar bayi cikeda tuhuma ba kunya balle shakka tace."danka ne Barde yaima yar mu Yusrah  fyaɗe ta sanadiyar hakan ta rasa rayuwar ta shiyasa mukawoma fa'da dan ta kwatar mana yan'cin mu.".....ba takaran Hamza ba hatta Abdullahi dasu Shamaki da dagatai dman anyi saa ranar fa'da ta cika tamkam zufa ke ketoma Hamza amma a zahiri sai cewa yayi." ki har wani yan'ci ne daku mene aibun Abbas dan ya huta da baiwa? daman kwanta ne yakare shiyasa ta mutu dan haka sunyi gaggawar kauda mashi da wannan baiwar tunkan su fuskanci mummunan hukunci."......ba bayin nan kadai ba duk wanda ke cikin fadar nan saida maganar galadima Hamza ta girgiza Shamaki ne ya nuna mashi rashin kyautawar hakan yace."koda bazaa hukunta Barde ba ya dace yai masu magana mai dadi dan rage radadin da zuciyoyin su ke ciki." kamar jira ya hau Shamaki da masifa sunaji suna gani aka sama Hamza ido.....nan yace d bayin su bacemai da ganin......cike da kulewa uwar bayi tace."a halin yanzun zamu dauki yarmu dan mu kaita ma kwancin ta amma kasani koda zamu kare wallahi bazamu hakura ba kamar yanda kace muba masu daraja bane, duk da musan bayima ya'yana my next book😁 ankama mutane masu daraja an wulakanta su balle mu damuka saba da wahala da wukakaci, bazaki damu da dukan abunda zakayi mana ba, kuma bazamu fasa fita, ku dauketa muje a shiryata saidai kasani wadan nan mutanan sine shaidar mu akan danka yaima yusrah fyade kowa yaga yanda jini je fita daga kasanta har yanzun inkuwa ka gardama ba majin kunyar budewa kowa ya gani."aiko tunkan ya musa ta bude wajen dik wanda ke gun saida ya kauda har shi kanshi Hamzan aiko yakasa magana, wasuma har kuka sukeyi sannn suka dauke ta suna kuka suka tafi da ita turakar bayi....duk wanda ke fadar nan saida ya tafi harta Abdullahi ya kasa tsayawa daga shi sai dogarinsa aka bari jiyake kamar yai kuka, yasan bayin nan sun fishi gaskia amma bazai bari ba dan shi  ya wulakanta taba a cikin Burhaan.....



Duk abin nan da akeyi labari ya karade Burhaan koda Hamza ya kira Barde ya tambaye shi bai musaba amma saiya dinga magana cike da gadara baisan sadda ya wanke shi da mari yana cewa. "kai mahaukacin inane?,da zaka kashe yar mutane ina laifin kadinga binta a hankali kana hutawarka da ita, ko kasan abinda ka aikata zai taba mulkina da darajar Burhaan yanzun gayacan zaa yimata janaza kasani naji kunya a gaban mutane masu daraja."......baki daya kwakwalwar Saude ta kulle tasan daga ita sai Masau'da sukaga gawar yarinyar nan amma ya akai bayan da wowar su zaace har anganta haka anya ba ture Masau'da taima suba? dan ta huce takun sakar da ke tsakanin ta da hamza ba.....tana cikin tunanin ta taji muryar Masau'da na magana"kai gaskia banji dadin abunda da danka Barde ya aika taba gashi anatacin ganiyar mulki harka kara kyau ga abinda dan kuka yajama uban sa, mene mafita Hamza."? Wani wawan kallon Hamza yayi mata sannnan yace. "Fitarma daga gida Masau'da tunkan nai maganinki."Murmurshi Masa'uda tayi sannan tace."Kaga kar kaiman ihu bayan baki daya duniya ta shafaa abinda ya faru kuma ya amsa laifinsa duk wani mari da zakai mashi bazai wanke kuba, yaka mata a matsayin ka na mai rikon kwaryar mulkin Burhaan ka fito a gaban kowa ka hukunta Barde yanda duniya zata shaida muddin ka kasa hakan lallai bazamu yarda ba, ai ciwon ya'mace na mace ne inda yarka Safiyyah akaima haka nasan kisa ya dace ga wanda ya aika ta abin yanzun Masarautar Burhaan tasa ido taga hukuncin da zakai ma danka Barde."dag'a hannu Hamza yayi zan wanke Masa'uda da mari, rike hannun tayi tace."ka kuskura kace zaka mareni zan fita waje infadama duniya akan nafada maka gaskia shine kace zaka haike mari kan kare kaina kaita marina,Hmmm Hamza muddin wannan maganar ta fita mi kake zato? Kaga Hamza kayima Masau'da biyyayya tunda Nafika iya tuggu inba haka ba nidakai muzuba mugani, bari injema mutanan ne gaisuwar rasa yarsu kafin muji abinda zaka yanke akan danka."....kanshi ya buga a bango ya fashe da marayan kuka, yace."shikenan Barde kagama zubda mani ƙima inaji inagani makiyana naimani dariya ya kake son inyi da raina?,Umma yazama dole in salwantar da rayuwar Masau'da na fahimci zata zamo mani barazana a rayuwa ta, tunda tagama sanin sirrina."....Saude tace."lallai da ka tabbata nonona kasha ba yanda banyiba akan ta sirrin ta abin nan so nike in dare yayi mu binne gawar da kanmu, shine tayomana cinne ta tabbata mulkin ka zai samu tan gyarda."Hamza yace...."lallai Goggo kamar  dai bake kika haifi hamza saidai in nazama gawa sannan hakan zai faru,muddin  da raina sai dai koni ko Masau'da."



*Allah sarki rayuwa kenan yauga soyayya tazama kiyayya shiyasa duk abinda zamu aikata musa Allah a ranmu, Allah ka rufaman asiri kasa mudace*

'''Kamar yanda kuka sani wannan labarin na''' *SADAUKIN BURHAAN* ( _Cigaban Izzah ko Mulki_ ) '''na kudine 300 paid, yan VIP kum 600 duk mai bukatar wannan buk din ya nemi wannan numbers din 07034464517 ko 08160508316 inayinku masoyana Allah yabar tare mai anfani, Yar Mutan Kankia ke maku fatan alkhairy'''

'''Sannnan kuma idan kina bukatar kiranta izzah ko mulki complete dan kisan ya Sadaukin Burhaan ya kusa ki turo 200 ta account number din da kika gani.'''

*Yar'mutan kankia ce ❣️*

Alqalami yafi takobi🖊️

Continue Reading

You'll Also Like

16.9K 181 128
The ancient saying goes: Most generals come from Guan Xi, while ministers come from Guan Dong. He Lisa was born to be a Star General. She was merely...
10M 754K 88
Marriage had always been my dream but not to a man about whom I know nothing. The moment my father fixed an alliance of me to a Prince without even t...
5.9M 385K 74
Losing this war means captured by the enemy empire and considered as their prostitutes and servants. Dreaming that situation made my heart race even...
10.5K 739 51
Just like how two shores of sea can never meet, they can never meet too, might be physically but never mentally. The other shore is too far to even t...