ILLAR MARAICI

By Bookaholicnutella

2.8K 275 80

Ta kasance sanyin idaniyar iyyayenta. Sanadin farincikinsu, dalillin jin dadinsu kuma 'ya kwalli daya ga atta... More

Jannah
Rahma
'Da na kowa ne
Me laifinta
Dangin Miji
Ramadan
Nigeria
Alkawari
Al'ajabi
Rashin Uba
Sabon littafi
Rabon Gado
Sabon Al'amari
Me Ke Faruwa
Sauyi
Zynat
Tashin Hankali
Takaici
Makirci
Sulaimi
Mugu Bai Da Kama

Rashin Gata

40 11 4
By Bookaholicnutella


Dedicated to bilkisuali and Aysherhayat  thanks for your votes and comments, Jannah loves you.

"Jennah! Jennah!"

"Open your eyes Jennah!"  Ji tai ana jijjigata kuma ana Kiran sunanta. Firgit ta tashi tana haki, fuskarta a jike da hawaye yayin da jikinta ya jike da zufa. Salati ta fara tana kokarin tashi.

Muryar Talib ne ya dawo da ita hayyacinta. A hankali ta dago jajayen idanunta ta kalleshi. Tuni jikinshi yayi sanyi ganin irin damuwa da tashin hankalin da take ciki. Cikin karamar murya yace

"Are you okay Jennah? You had a dream" girgiza Kai tayi tana share hawayenta kafin ta amsashi. "Talib, I want to see my sister". Ko rufe baki bata yi ba wata nurse ta shige dakin. Mikewa Jannah tayi da nufin shiga dakin amma Talib yayi saurin dakatar da ita.

"Jennah ki jira ta fita tunkunna" saurin girgiza kai tayi  ba tare da ta kalleshi ba tace " I need to see her". Shiru Talib yayi kamar ba zai amsa ba sai kuma taga ya matso inda take hannunshi dauke da sallaya. "You should first pray".

G'yada kai ta karbi sallayar hade da godiya. Ba ta kai minti goma da tafiya ba ta dauwo. Yanda ta barshi a bakin dakin, haka ta sake tarar da shi. Tana karasowa taga nurse na dazu da wani dogon doctor sun sake shiga dakin. Ba'a jima ba taga an shigo da stretcher cikin ICU an sa Rahma akai.

Girgiza kai Jannah ta hau yi tana zub da hawaye. A rikice ta kalli Talib tana jijjiga hannunshi "where are they taking her Talib? Tell them to stop... " Tun lokacin da taga an sa Mahaifiyarta akan stretcher taji ta tsani abin gaba daya. Tuni  numafashin ta ya fara yankewa.

Cikin sauri Talib ya zaunar da ita a daya daga cikin kujerun wajen. "Relax Jennah za ayi shifting dinta zuwa private room ne" Kallonshi tayi da rinannun idanunta tana son tabbatar da gaskiyar maganarshi.

"I promise". Nodding tayi ta sake mikewa tana me gode wa Allah. At least hankalinta ya kwanta daji za'a kai ta private room ne. A room 17 aka aje ta.

Fitansu doctors din kenan Jannah ta shiga dakin. A hankali ta zauna tana kare wa Rahma kallo. Addu'o'i sosai ta mata, tana me zub da hawaye. Har yanzu ta tabon da Ashir ya bar mata a fuska. Har yayi wani purple purple. Bakinta a bushe shima ya zama wani blue haka, ga shi tayi haske.

Bakin gashinta a zube akan pillownta. Tana bacci cikin kwanciyar hankali. Sumbatar ta tayi a goshinta sannan ta juya ta fice dan five minutes kadai aka bata. Fitowarta kenan ta ta ga Talib tsaye a bakin kofar.

"How's she doing?" Karamin murmushi Jennah tayi wanda yasa Talib rike numfashinsa na tsawon lokaci. A zuciyarshi kuwa cewa yake "Subhanallah! Fa tabarakallahu ahsanul khaliqiin"

Duk da cewa iya idonta kadai yake gani, sai kuma kadan daga cikin girarta da karar hancinta, yasan cewa ba karamin kyau Allah ya azurta ta da shi ba.
"Alhamdulillah, I think she's doing better".

Shi ma murmushi me kayau yayi sannan ya kawar da idanunsa duk da yanda yake so ya cigaba da kallonta yasan haramun ne tunda ita ba muharramarsa bace.

"Ma Sha Allah, that's good to hear. Why don't you eat something, kafin doctors din su dawo" sai a lokacin ta kula da disposable cup na coffee da chips dake hannunshi. Har zata ce a'a sai kuma cikinta yayi fara kuka.

Murmushi Talib yayi sannan ya mika mata abin dake hannunshi. "Sorry, this is all I could get". Murmushi Jannah tayi tana kada kai. "A'a Talib, this is more than enough. Thank you".

Bayan ta wanke hannu ta zauna zata fara ci, sai ta tuna dole sai ta daga niqab dinta. Ga kuma Talib yana nan. Kallonta Talib yayi, sai yayi saurin dauka wayarshi. "Excuse me Jannah". Yasan babu yanda zata ci abu a gabanshi. Jiya ma sai da yabar wajen kafin tasha coffee.

Dakin Mahaifiyarsa ya wuce. A zaune ya sameta tana tasbihi akan gado, har drip da aka sa mata jiya ya kare. Bayan sun gaisa ya zauna a kujeran dake gefenta. Yasa hannu da dauki Al Qur'an dake kan drawer. Cikin kyakkyawar kira'arshi ya karanta Suratul Yaseen.

Ko da ya gama, maida Qur'anin yayi sannan ya rike yatsun mahaifyarshi yana wasa dashi. Matsawa mahaifyarshi tayi tare da mishi nuni da gefenta. A hankali ya hau kan gadon ya zauna a gefenta.

Kwantar da kanshi tayi kan ciyarta tana karanta mishi addu'o'i tsawon lokaci. Ko da idar, babu wanda yayi magana a cikinsu. Har sai da ta fara magana.

"Me ke damunka, Abbati. You seem troubled". Juyawa yayi yana kallonta da idanunsa da suka cicciko da hawaye. Cikin rawar murya yace "Ummi I don't know". Rungumeta yayi, ya boye fuskarshi a cikinta yana zub da hawaye.

Gaba daya ya rasa me yake mishi dadi. Har ga Allah yana tsananin son Jannah. Idan aka dauke Ubangijinsa da manzonsa, bashi da wanda yake so sama da Jannah illa mahaifyarsa.

Kuma yana tsoron rasa ta, dan wani lokaci da wani school mate dinsu Tahir yace yana sonta, ba karamin duka ta mishi ba duk da cewa yaron ya girmeta

Shi ba ma dukan bane damuwarsa. Yasan ko a bacci Jannah baza ta iya dukarsa ba. Amma matukar ya bude baki ya ce mata yana sonta, to yasan har abada baza su shirya ba.

A kullum sai ya godewa Allah sanin cewa shi kadai ne namijin da take kulawa a school din. Dan ko teachers ma in ba dole ba magana bata had'a su.

Jin Talib yayi shiru yasa Ummi girgiza Kai. Tana me tausayin danta. Sake kallonshi tayi, kayan jiya ne a jikinshi, kuma ga shi ya dan yi squeeze. "You haven't changed, you didn't sleep either. Abbati a nan ka kwana ne?".

A rikice ya dago kai ya kalleta. Saurin dauke idanunsa yayi sanin cewa bazai iya karya yana kallon cikin idonta ba. Zai fara magana ta sake katse shi "kar ka min karya, Abbati".

"Promise you won't be mad" a hankali ya fada yana kallonta. Murmushi tayi had'e da g'yada kai. A hankali Talib ya tashi ya zauna, cike da nutsuwa ya bata labarin abin da ya sanni tattare da Jannah.

Ko da ya gama bata ce komai ba, hakan kuma ba karamin tayar mishi da hankali yayi ba. A duniya babu abin da yaki kamar fushin mahaifyarshi. Har sai daya fara regretting fada mata, sai kuma yaji tace

"You like her right?"

Da sauri Talib ya kalleta, zuciyarshi na dukan uku uku. Numfashi yaja sannan yace "I do, Ummi". Kyakkyawar murmushi tayi had'e da sumbatar goshinsa.

"I'm proud of you, Abbati". Nasiha sossai ta mishi, wanda yasa hankalinshi kwanciya. Kwantar da mahaifiyarshi yayi, sannan ya gyara mata pillow. Kallon agogo yayi yaga 6:54. Tun 6:07 ya bar Jannah. Addu'a yayi yana me rokon Allah da ya kareta.

"Always remember, Abbati. Idan matarka ce, in sha Allah kai ne zaka aureta. Amma idan ba matarka bace. Duk yanda kaso baza ka aureta ba. Ka roki Allah ya zaba maka mafi Alkhairi".

"Amin Ummi".

Zynat dake bakin kofan tun dazu, ta sa hannu ta toshe bakin ta. A guje ta fita tana kuka. Basu san tana wajen ba dake sun juya wa kofar baya. Kuka sosai tayi har sai da ta godewa Allah.

Dai dai lokacin a zata shiga kenan ya fara ba mahaifyarshi labarin Jannah. Ko makaho ne yasan irin son da yake mata daga yanayin maganarshi.

Dan ko yanda yake furta sunanta ma daban ne. Talib mutumin kirki ne amma baya taba bayyana emotions dinsa. Kuma bai taba zama da ko kuma magana da mace ya kai five minutes ba. Hatta ita da take cousin dinsa. Amma yau har kwana yayi a asibiti sabo da Jannah!

Kuka sosai tasa tana me tausayin kanta. Tun tana shekara goma take son Talib a lokacin kuma yana da shekara goma sha biyu. Dafe kanta tayi tana kuka "Ya zan yi da raina ni, Zynat".

Mikewa tai, ta share hawayenta da ta tuna abinci ta kawo wa Ummi da Jannah. Ko da ta tuna Talib ne ya Kira ya ce ta kawo ma Jannah abinci idan zata kawo na Ummi, sai taji ranta ba dadi.

Hannu ta daga sama cikin dashashiyar murya "ya Allah gani gareka". Cikin sanyin guiwa ta shiga dakin kanta a kasa. Sallama tayi ba tare da ta daga kai ba, siririyar muryarta.

"Ina kwana Ummi" Zynat ta tsugunna tana gaida Ummi. Cike da fara'a Ummi ta amsa. "Lafiya kalau Ummita an tashi lafiya". Er karamar murmushi tayi sannan ta amsa Ummi.

Ba tare da ta kalli Talib ba tace "Ina kwana Ya Abbati" Kamar ance ta daga idonta ta kalleshi. Murmushi me kayau yayi wanda ya bayyannar da dimples dinshi.
"Kin tashi lafiya Ummita?"

Yanda ya fad'i sunanta da kuma yanda ya ke mata murmushi ne yasa ta nemi fushi da bacin ranta ta rasa. Sai ma wani sanyi da taji a ranta.

"Lafiya Ya Abba" Abincin ya karba ya zuba wa Ummi. A hankali ya ringa bata duk da cewa taki har sai da ta gama sannan ya bata maganinta.

Kallonshi Ummi tayi, fuskrta dauke da er murmushi. "Ka gaji kaje gida, ke Ummita baki da makaranta ne?" Talib ne yayi saurin fara magana cikin ladabi yace "Ummi I'm alright. I think I'll take the day off"

"Ummi akwai school amma..." Shiru Zynat tayi ba tare da ta san yadda zata karasar ba. Murmushi Ummi tayi sannan tace da Zynat data tsunkuyar da Kai. "It's okay, Ummita just make sure ki samu Hutu". Murmushi sosai Zynat tayi had'e da yiwa Ummi godiya. Sannan ta wuce wajen Jannah, Talib kuwa ya wuce gida dan yin wanka

Da misalin azahar Talib ya dawo dauke da manyan flask na abinci. Sai da yaje wajen Ummi sannan ya wuce wajen Jannah. Tsaye ya sameta a gaban dakin Rahma tana kallon wayar dake ringing a hannunta.

Ba karamin kyau ta yi ba cikin army green abaya da cream gele duk da yau ma ta sake yin niqaab da black veil din. Sallama yayi had'e da kau da Kai. Da fara'a ta amsa ba tareda ta kalleshi sau biyu ba.

"Jennah, your phone is ringing, why don't you pick it up? Should I excuse you?" Cikin sauri Jannah ta dakatar da shi ganin Uncle Abdul ne yake kira for the fourth time.

"It's okay, Talib, you don't have to leave. Uncle na ne yake kira it's just that I don't want to talk to him right now. I don't know what to tell him"

Shiru yayi ba tare da ya sake magana ba sanin cewa tana cike da damuwa. Sai da ya tabbatar ta ci abinci sannan ya kyaleta ta je ta sami Rahma. Shi kuma yana jiranta a waje.

Ta dau tsawon lokaci a dakin Rahma tana me mata addu'a da kuma karatun Alqur'ani dai dai lokacin da take karanta ayan karshe na suratul Yaseen taji hannun Rahma dake cikin nata yana motsi.

A hankali Rahma ta bude idanunta. Kukan farin ciki Jannah tasa had'e da yiwa ubangijinta godiya. Ruwa ta ba Rahma dake tari sannan ta fice Kiran doctor ba tare da ta kula da Talib dake wajen ba.

Godiya Talib ya sake yiwa Allah ganin irin murmushin da take yi. Ba'a jima ba ta sake dawowa da doctors. Bayan an duba ta Jannah ta taimaka mata da mayafinta sannan ta shigo da Talib.

Godiya sosai Rahma tayi mishi bayan ya yi mata ya jiki. Jannah bata bar dakin ba har sai da Rahma ta sake bacci. Anan ta wuce dakin maman Talib.

Da fara'a Ummi ta karbeta sannan tayi ta mata addu'a da nasiha. Bata nuna mata tasan komai akanta ba. Saida tayi sallahn la'asar sannan ta koma wajen Rahma.

Zuwanta kenan Rahma ta tashi, basu jima ba wani mutum had'e da polisawa suka zo daukan report. Ba yanda ba'ayi ba amma Rahma taki magana kuma ta hana Jannah yin magana.

Ba karamin haushi Jannah taji ba amma bata ce komai ba. Kwanansu hudu a asibiti aka sallamesu. Cikin kwanaki biyar din da sukayi a asibitin karamin kokari Talib da Zynat sukayi musu ba, duk da cewa kwana biyu da suka wuce aka sallami Ummi.

Ba yanda Jannah bata yi ba amma Talib yaki tafiya gida. Kullum idan an tashi a school, zai zo wajensu. Ba shi zai tafi ba har sai bayan sallahn isha'i.

Kuma ko da wasa baya barin Jannah ta kashe ko sisi daga abin da ya kama abinci har magani da kudin daki. Duk da cewa Jannah taki har se data daina mishi magana amma bai dai na ba. Kullum sai yasa daya daga cikin masu aikin gidansu sun kawo musu abinci ko da yana school.

Parking motar yayi a bakin gate na gidansu Jannah. Kallon Jannah dake ta faman bata rai yayi. Murmushi yayi ganin irin hararar da take masa duk da cewa tana seat na baya.

"I'm sorry Jennah, but I can't just let you leave in an uber". Saukar da kai Rahma tayi sannan ta ja numfashi. " You've done a lot to us, Talib. I've been nothing but a nuisance and I don't wish to trouble you anymore"

Girgiza kai yayi yana kallon steering wheel dake gabanshi "You deserve everything, Jennah. I must leave now. I wish you a speedy recovery, Sister Rahma".

Murmushi Rahma tayi tana gyara zaman niqaab dinta. Allah kadai yasan irin tsoron da takeji tun da taga sun iso gidan.

"Thank you so much, Talib. Jazakillahu khair".

Da haka su ka fita a motar da karamin jakan dake dauke da uniform na Jannah. Rahama kuwa kayan da ta saka ranar da za'a Kai ta asibiti ta sake maidawa, kasancewar Jannah ta wankesu.

Ko da Jannah ta mayar mishi da kayayyakin da yasa Zynat ta kawo mata, kin karba yayi cewa yayi ta rike. Gaba daya sai taji ba dadi, hidiman yayi yawa.

A hankali suka tako zuwa cikin gidan. Jannah na rataye da jakarta a hannu daya. Dayar hannunta kuma na rike dana Rahma.

Suna bud'e kofan Rahma ta rike numfashinta sakamakon Hafsa da ta gani tsaye a bakin kofan. Idonta cike taf da hawaye...

Who should Talib choose? Jannah, Rahma, or Zynat

Thank you for reading.

~Zara ❤️

Continue Reading

You'll Also Like

169K 15.5K 30
"သူက သူစိမ်းမှ မဟုတ်တာ..." "..............." "အဟင်း..ငယ်သူငယ်ချင်းလို့ပြောရမလား..အတန်းတူတက်ခဲ့ဖူးတဲ့ အတန်းဖော်လို့ ပြောရမလား...ဒါမှမဟုတ်..ရန်သူတွေလို...
409K 5.5K 28
Emmett loves to be a rebel. He skips school to hang out, drink, and smoke with his two friends when suddenly he and his best friend are cornered and...
128K 1.6K 51
𝐈𝐭𝐬 𝐭𝐡𝐞 𝐟𝐢𝐫𝐬𝐭 𝐝𝐚𝐲 𝐛𝐚𝐜𝐤 𝐭𝐨 𝐬𝐜𝐡𝐨𝐨𝐥 , 𝐀𝐚𝐥𝐢𝐲𝐚𝐡 𝐢𝐬 𝐧𝐨𝐰 𝐢𝐧 𝟏𝟎𝐭𝐡 𝐠𝐫𝐚𝐝𝐞, 𝐰𝐡𝐢𝐥𝐞 𝐬𝐡𝐞𝐬 𝐭𝐡𝐞𝐫𝐞 𝐬𝐡...
651K 1.1K 22
Smexy One shots😘 Got deleted twice 3rd times a charm🤦🏻‍♀️😭