DUNIYA

By Fatima_writes_

100 6 9

A tunanin Shaheed ya dace da samun Shaheeda, mai zai faru lokacin da aka yi wa Shaheeda kisan gilla a daren a... More

1: Yankan ƙauna
2- Shaheeda

3-The Ɓagwais

18 1 3
By Fatima_writes_

A sanyaye ta nufi kitchen ɗin bayan ta yi wanka ta canza kayanta, in ta ce alaƙarta da Mommy bata damunta ta yi ƙarya, mutane na mata kallon wadda ta samu kusan komai a duniya, za a kaita makaranta a ɗaukota, tana da sutura, tana da gata, ba a isa a taɓata ba a makaranta, yanzu sai a ɗaure mutum. Sai dai basu sani bane, tana cikin kaɗaici sosai, bata da ɗanuwa ko ƴaruwar da zata bawa labarin makaranta in ta dawo gida;

Daddy yawancin lokuta yana wurin aiki kuma bai cika dawowa da wuri ba, He's a busy man, kai tsaye ba za a ce ɗan siyasa bane, sai dai kasancewar shi babban lauyan Hon. Ɓagwai; ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɓagwai a jihar Kano, yakan shiga al'amuran siyasa sosai da sosai, wani meeting ɗin ma da shi ake yi, shi ne abokin shawarar Hon. Ɓagwai, wannan ne ya jawo mai maƙiya masu yi masa baƙin ciki, tunda a da shi ba kowa bane, wasu a cikin masu yi masa baƙin cikin ma sun haife shi, sanadiyyar principal ɗinsu Shahee wadda ta kasance ƙanwar matar Hon. ya samu wurin zama sosai har ake damawa da shi.

Mommy kuma bata aiki duk da a da ta yi aikin banki, wannan ne ya sa bata wani samu lokacin ƴar tata ba, tun bata wuce wata uku ba ake barinta a hannun Hajja Talatu, da ta so ta ringa kaita gidansu, kasancewar akwai yara sa'anninta a gidan ya sa ake cin zalinta da sunan wasa, wannan ya sa take barinta a hannun Hajja, kuma ba laifi tana kula da ita. Abinda ya yi sanadiyyar barin aikin Mommy bai wuce ganin Shahee ta taso a sangarce ba, babu wata ƙwaɓar kirki da take samu daga Hajja saboda irin kashedin da ta sha a wurin Daddy, ya yi mata alƙawarin ƙarasa rayuwa a gidan yari muddin ya  gani ko ya ji labarin ta kai hannunta jikin ƴarsa da sunan duka, ko kuma ta ɗaga mata murya ta wuce misali. Ga wani irin zagi na ba gaira babu dalili da ta koya, all thanks to Hajja, ko baƙi aka yi suka nemi su yi mata wasa sai ta nemi ta zage su. Akwai wani lokaci da Hon. ya zo dubata lokacin da ciwonta na Pneumonia ya tashi, Shaheed ɗanshi na uku ya kai tissue hancinta zai goge mata saboda ciwon nata ya kan zo mata da mura. Babu tsoron Allah ta kalli idonshi ta ce masa:

"Banja, wawa mai 'aton kai, an ce maka ban iya fyacewa bane?" He was dumbstruck don shi ya ɗauka ma bata iya magana ba.

Hon. ya ɗan yi dariyar yaƙe sannan ya ce mata ta yi haƙuri a fyace mata kar majina ta gangaro bakinta. Shi ma ya samu nashi rabon zagin don ko ce masa ta yi:

"Ina luwanka?Ni bana shon shishshigigi babba da kai amma ka iya gulma wa ya sa da kai?"

Da Mommy ta zauna ta yi tunani sai ta ga ba a ko'ina ta koyi zagi ba sai a wurin Talatu da Adewale, sai ta ga gwara ta ajiye aikinta ta zama full housewife ta kula da tarbiyyar ƴarta. Me amfanin ka nemi duniya ka tara kuɗi ƴaƴanka su taso babu tarbiyya? Da ta faɗawa Daddy bai ƙi bata haɗin kai ba, shi dama ba son aikin yake ba.

Babbar matsalar shi ne lokacin da Mommy ta ɗaura ɗamarar inganta tarbiyyar ƴar tata, ba ta tsaya ta karanci matsalarta ba, balle ta san hanyar da za ta bi. Yaron da ya taso babu ƙwaɓa har ya saba ba lallai ne dare ɗaya ka ce zaka zare masa ido ka dake shi ya gyaru kuma ya gyarun ba. Wasu duka na gyara su, wasu kuma barazana ce, wasu yaran kuma nasiha kaɗai za a musu su shiryu da dai sauransu.

"Mommy kar ki sa kabewa, kin san dai bana ci."

"To Mama Salamatu, sai kuma me?"

"You messed up you idiot!" Shaheed an ta faɗa a ranta tana ɗan dungure kanta, ita da ta zo acting as a good girl ya zata fara da bada order?

"I'm sorry Mommy just wanted to start a conversation." Shaheedan ta faɗa tana haɗe hannunwanta alamun sorry.🙏

Mommy bata ƙara tankata ba, saboda ita yanayin yarinyar ma mamaki ya ɗan bata duk yadda aka yi wani abin take so. Ta ɗauko container ɗin da take ajiye Maggi da niyyar yin haɗi a miyar alayyahun da take yi. Ba kasafai take yin Tuwo ba a gidan, yawanci in dai ta yi to za a yi baƙi ne ƴan gargajiya, kamar dai Hon. duk wayewarshi da kuɗinshi babu abincin da ya fi so sai Tuwo, shi ya sa duk inda zai je baƙunta, da Tuwon ake tarbarshi musamman ma in an haɗa shi da miyar alayyahu.

"Kawo in ɓare miki" sai da ta faɗa sai ta ji kamar yanzun ma order ɗin ta bayar, sai ta yi maza ta gyara.

"Mommy don Allah kawo in ɓare miki"

"Toh, gashi" Mommyn ta miƙa mata wani abu na tattarewa a zuciyarta, wani abu mai kama da hope, kamar dai tana kusa da yin irin rayuwar da take fata da tilon ƴarta.

"Nawa zan ɓare?"

"Ɓare daidai da shekarunki"

"Shida kenan"

"Yeah" cewar Mommy tana zama akan ɗaya daga cikin kujerun da aka ajiye a kitchen ɗin.

"Mommyna gashi na gama"

"Toh yarinyar kirki, Allah ya miki albarka."

Sai Shaheeda ta yi murmushi, ba wai bata yi bane, amma sai Mommy ta ga kamar this is the first time da ta yi mata genuine murmushi, murmushin nuna jin daɗin abinda ta yi mata, ba wai Daddy ta yi wa ba ita ta yi wa. Me ya jawo murmushin?

"Kin yi mata addu'a mana, cikin salama ba tare da hantara ba." Wata zuciyar ta raya mata.

Sai Mommy ta tsinci kanta da tambayar kanta, shin me ya sa take denying facts? Ta riga ta san Shaheeda na son a ja ta a jiki, a nuna mata tana da mahimmanci, a kulata a zauna da ita a yi hira, amma ita bata taɓa yin haka. Misali in ta dawo daga makaranta zata shigo da kauɗinta tana cewa:

"Mommy yau aka daki wani ɗan ajinmu wai ya je da dirty uniform"

Maimakon ta biye mata su yi hirar sai ta jefeta da baƙar magana:

"To meye marabar ku da shi?dube ki don Allah kamar wadda aka ƙwato daga bakin kura." Yadda fuskar yarinyar take tattarewa alamun rashin jin daɗi doesn't go unnoticed, but Mommy doesn't care, a cewarta tana so ta daina wasa a makaranta tana ɓata uniform ɗinta ko da ta je da su fes.

Ranar da ta dawo bata ɓata uniform ɗin nata ba still ba ta tsira ba;

"Mommy yau ko wasa ban fita ba, kalleni fes na dawo abu na."

"Sai aka yi yaya? Ban hana ki shigo min gida babu sallama ba?"

Sai bayan ta tafi ɗaki rai babu daɗi Daddy ya ƙwabeta amma sai ta nuna baya son ganin laifin ƴar lelen tashi ne, sai dai yanzu ta tabbatar a wasu lokutan tana amfani da wrong approach wanda yake yi wa Shaheedan tsauri but a yanzu she's ready za ta gyara da izinin Allah, she wants her bubbly Shahee back. She wants to be the mother every child would ask for. Sai dai bata sani ba, bata da wannan lokacin.

Durƙusawa ta yi ta Janyo ƴar tata ta yi ta rungume tana jin wani irin feeling kamar na kewa, kamar na bankwana baza ta iya fassara shi ba, haka shi ma Daddy da ya zo ya sanar da ita isowar Hon. da iyalanshi ya ji, sight ɗin ya mishi kyau, amma sai jikinshi yake faɗa mishi ba lallai ne ya kuma gani ba, ba lallai ya kuma dace da ganin wannan mother-daughter moment ɗin ba. Shaheeda ta fara ganinshi saboda fuskarta ce take kallon kofar kitchen ɗin. Ta bashi thumbs up 👍kafin ta ce:

"Daddy it worked!Thank you" shi kuma ya yi replying ɗinta da:

"You're always welcome my daughter"

Mommy ta sake ta tana miƙewa kafin ta kallesu suspiciously, sannan ta ce:

"You two conspired against me right?"

Sai suka yi dariya suka girgiza kai kafin kowannensu ya ce:

"Babu ruwana" a tare.

Suka kuma ƙyalƙyalewa da dariya a tare. Kamar babu wani abu da zai taɓa farin cikinsu a nan gaba kaɗan.

******
Bayan sun kwashi tuwon shikafar ne, Hajiya Sadiya Shitu(Mommy) da Hajiya Hajar(matar Hon.) suka fara hira irin tasu ta matan manya, su Shaheeda da Salima su ma suka tafi wasansu a ka bar Shaheeda da saka musu ido don shi ba son shiga harkar Shaheeda yake ba, bai manta zagin da ta yi masa ba, ba ya son ta ƙara yi masa wani don rufe ido zai yi manta da wata kara ya yi mata ɗan banzan duka. Shi kuma Sa'id auta dama cikinshi na ɗauka ya yi barci.

"Wallahi Maman Shaheed rashin haihuwar nan ba ƙaramin damuna yake ba, ko kuma Allah ya yi ƴa ɗaya zan haifa a duniya ne ban sani ba, har cewa fa na yi Daddy ya ƙara aure ranar nan, baki ga yadda ranshi ya ɓaci ba, wai ai shi ɗaya ma ta ishe shi, kuma da haihuwa da rashinta duk na Allah ne."

"Ai da gaskiyar shi Maman Shaheeda, ni kaina da na ɗaga hankalina akan haihuwar nan, saboda ta zo mana da jarabawa kala-kala, akwai fa lokacin da aka ringa cewa wai Hon. kai yaran mu  yake ana yi masa kuɗi da su, kin san  ƴaƴana huɗu na haifa suna mutuwa da zarar an haifesu, ba Shaheed ne ɗa na na fari ba, yayanshi ƙyanda ce ta kasheshi, shi kaɗai ne ma ya yi shekara uku a cikinsu, sauran suna yin ƴan awanni suke komawa, sai daga baya ne aka gane ni ce Rhesus negative, shi ne fa ake yi min allura kafin na haihu, ƙarshe ma a haihuwar Sa'id aka cire min mahaifar gaba ɗaya a cewarsu ta gaji haka. To da na ɗau haƙuri ba gashi nan ba muna zaune lafiya ba, sai fatan Allah ya shirya mana zuri'a"

"Amin ya hayyu ya ƙayyum, wato kowa da irin jarabawarshi, Allah ya sa mu dace, Amin."

Su Barr sun daɗe suna tattaunawa don sai da aka yi sallahr Isha'i sannan suka tafi, fuskar Barr. da Hon. ɗin ba yabo ba fallasa, da alamun koma meye suka tattauna ba abu ne mai daɗi ba. Cikin dare Mommy ta nemi jin me ya ɗagawa Barr hankali ya ce mata ta ƙyaleshi bai shafeta ba, karo na farko a rayuwarsu da ya ɓoye mata abu har haka, ba wai yana faɗa mata details ɗin abinda suka tattauna da Hon. bane amma yakan sanar da ita abinda ya san bai saɓawa aikinshi ba, kamar ya ce mata sun tattauna ne akan wani project ne, ko wata kwangila, ko yi masa signing ɗin wasu takardu amma ranar sai ya nuna mata babu ruwanta, ita ma sai bata matsa masa ba... Ko me Hon. Ɓagwai ya zo da shi? Allah masani.

Continue Reading

You'll Also Like

529K 21.2K 89
Join the ride full of possessiveness, love,hate,pain,happiness,joy,rudeness.
14.9K 2.3K 24
جۆنگ کوک:بە نەفرەت بیت وازم لێ بێنە چیت لە من دەوێت تایهیۆنگ:ششـ ئازیزم بۆچی هاوار دەکەی ئارام بە بۆ باروودۆخت خراپە ༄༄༄༄༄༄༄ جۆنگ کوک:تـ تۆ چیت کرد ت...
14.6K 2.5K 9
In the elite ranks of DRDO, Ardik Rajwasnhi, a young prodigy, is fueled by ambition to secure a coveted position among the legendary Team Phoenix. Ho...
107K 3.6K 40
Y/N was a teenage introvert who enjoyed having her own space and being alone. She loved listening to music in her room, which was a great escape for...