"MALEEK"

By mrs_Avbdool18

39.3K 2.8K 81

labarin soyyaya ne tsakanin mai kudin da mulki dakuma yar talakawa Inda mahaifiyarsa tace bazaya auretaba sa... More

preface
MALEEK 01
MALEEK 02
MALEEK 03
MALEEK 04
maleek 5
MALEEK 06
MALEEK 07
MALEEK 8
MALEEK 09
maleek 10
MALEEK 11
MALEEK 12
MALEEK 14
maleek 15
maleek 16
MALEEK 17
maleek 18
maleek 19
maleek 20
21 A tsawace tace Kai nake sauraro, to wallahi kashiga hankalin aure maleek 21
maleek 22
maleek 23
maleek 24
maleek 25
maleek 26
maleek 27-28
maleek 29-30
maleek 31-32
maleek 33-35
MALEEK 35_36
MALEEK 37_38
maleek 39_40
maleek 41 _ 42
maleek 43 _ 44
maleek 45 _ 46
47 _ 48
maleek 49 _ 50
maleek 51_ 52
53 _ 54
maleek 55 _ 56
maleek 57 _ 58
maleek 59 _ 60
maleek 61 _ 62
maleek 65 _ 66
maleek 67 _ 68
maleek 69_ 70
HUMEYRAH

maleek 63 _ 64

525 58 0
By mrs_Avbdool18


  63 _ 64

Not edited

"Saukar da kanta tayi kasa cikin tsanan kunyar abinda maleek yamata kokarin Maida kwallan da yake neman zubo mata take, gaba tayi ta bude motar su tashige cikeda kunyar abinda maleek yamata.

Duk wa enda ke gurin basuji dadin abinda maleek yayi ma meenal ba Sam bade kamar mom, su Meena binta sukayi suka shiga motar suma, mom karasawa tayi tabude motar da yake ciki tazauna Itada maleeka, muhassin kuma seat din gaba na gefen driver ya shiga.

Motacin excort ne sukafayin gaba motar su maleek na tsakiya sai sauran escort na rufa musu baya.

Adede tankamemen gidan suka faka, dasauri maigadi ya Dannan remote nan da nan gate ta zuge suka Dannan Kai ciki, kasancewar harbar gidan data wadatu yasa duk yawan motocin suka dauke.

Dasauri daya daga cikin escort ya zagayo yabude murfin motar maleeka ce tafara fitowa da nan sai mom sai daga karshe gogan naku ya fito yana wata tafiya mai cike da takama,

Adede bakin kofar kowa ya tsaya maleek ne ya matsa gaba ya Dannan pin din kofar nan da nan kofar ta zuge duk suka shige ciki, bin falon suke da kallo sbda ya tsaru iya tsaruwa da kayan alatu na kyalelen duniya,

Maids ne suka fara dawainiyar da manyan warmers da wanda su mamy suka kawo, abinci aka dafa yafi kala 10, mikewa sukayi suka nufi draining mai cin mutun 12, meenal wucewa tayi daki Don bazata jure kallan da maleek ke aika mata ba, bayan kowa ya hallara mom ta waiga takalla meena tana banga meenal ba, go and call plss.

Mikewa meena tayi tanufi dakin, ganin meenal tayi zaune ta kifa uban tagumi idon ta jajur da gani kuka taci, kallonta meena tayi tace haba meenal miye maanar hakan ne plss ki kwamtar da hankalin ki yanzu tashi muje kici abinci everyone ix dere ke kadai ce bakinan, pretend as if noting happen tashi ki wanke fuskarki muje, da kyar ta lallabata tamike suka Isa dinning din sarving kadan tayi taja kujera ta zauna.

Shiru kakeji sai kas kas karar cokali, meenal wasa kawai takeyi da spoon din Amman takasa cin abincin, duk jitayi ta takura kamar Ana kallonta, dogo kanta da tayi yayi dede da na maleek kamashi tayi yana kallonta, yayi saurin Janye nasa idon, mika hannu tayi zata dau cup shima yasa nashi akan nata wani shock taji  tayi saurin sakarmasa ashe shima yasake, tass kakejicup din ya tarwatse a kasa.

Hakan shiya jawo hankulan mutanen gun, mom ce tafara magana subhanallah ya haka meenal hope bakiji ciwo ba, girgiza Kai tayi kawai mikewa maleek yayi zewuce ciki, mom takallesa tace Kai were to Beko kalleta taba yace am done tareda fita, kowa nagama kamalla cin abincin ya Mike nan maids suka shiga tattare gun.

Bayan kowa yayi sallah an huta, mom ta kalle kowa tace lets have a word zamu Dan tattauna, guri duk yayi tsit mom tafara magana kamar haka,

"Dan allah yayana ku yafe min nasan na aikata babban laifi agareku Amman Dan allah ku yafe min wallahi natuba sharrin zuciya ne, nayi muku alkawarin Gina muku sabuwar rayuwa mai cikeda Kula da tarairaya duk abinda kuka rasa ada nayi alkawarin yimukushi tafada jikinta a sanyaye,

Amman nasan Idan kukaji abinda na muku wallahi bazaku taba yafe min, Abdulmaleek nacutar dakai kayafe min Dan allah, sauke ajiyar zuciya tayi tana Nina kashe mahaifinku sanadiyar ziga dakuma son zuciya irin rawa Amman wallahi nayi nadama kuyarda Dani tafada kwallan takaicin abinda ta aikata ya zubo Mata,

Zubara maleeka tayi jikinta har rawa yake tareda bakinta cikin takaici tace mom ban taba sanin muguwar zuciyar ci takai hakaba I never knew u have reach up to that extent inalillahi wa inna ilaihi rajiun sbda duniya u choose kimaida mu ophans ke kuma widow sbda abin duniya anya mom kinada inamani kuwa, bana tunanin ke kika haife mu toshe bakinta tayi sbda kuka da ya kwace mata ajiye dan ta tayi tawuce daki dasauri ta kulle kanta tasaka key,

Gaba daya salati aka dauka kowa na kallon mom babu wanda ya taba tunanin zaluncinta yakai haka babu ma mai bakin magana,

Maleek ma mikewa yayi yana jin kamar zefadi tsabar tashin hankali baitaba tunanin abinda zeji ba kenan dago idonsa yayi dasukayi jajur ya watsa ma mom wani kallo mai cike da tsana sannan yanufi dakin sa.

Shiru ne yabiyo baya sai shesshekar kukan mom, wayar abba ce tayi ringing mikewa yayi a dasauri to gani nan zuwa tareda kashewa kallon mamy yace Fatima wai falmata na can ba lafiya tashi muje ok duk Mekewa sukayi abban yaba mutanen gun hakuri yace ko zuwa gobe ko jibi insha Allah zasu dawo.

Suna isa  gidan falmata sukaga adama sai kuka take sharbawa da sauri meenal takarasa gunta tana dafata tace adama yajikin mama, nuna mata dakin kawai tayi mikewa tayi tashiga dakin a bakin kofa ta kafe tana kallonta ga wasu kwallan tausayi na fito mata, duk wani mai imanin da zaiga falmata sai yamata kuka Don kuwa takoma kamar ba itaba tarame kamar kwarangwal tayi wani baki ko tashi bata iya yi ga wani ciwo a kafarta dake zubda ruwa sai wari gurin yakeyi sosai tanan kwance.

abba karfin zuciya yayi kawai yasa shima baiyi kuka ba, kallon adama yayi yace yaushe ciwon yayi tsanani haka?

jiya tafada tana share kwalla, to meyasa baki kira kika fada mana ba, wayana ne ba chargy Amman na fada ma baba yanzu suntafi siyo mata magani shida yaya, to bari sudawo mugani in abinyaki sai muje asibiti.

Many dake tsugunne gaban falmata sai sharbar kuka take, da kyar falmata ta iya bude baki da maganar ta wadda baaganewa sai ka kasa kunne tace "Dan allah kudemin kuka adduah kawai zakumin duk Nina jama kaina wannan Balain ba wani ba naje na kwaso ma kaina Aids gashi yanzu tana neman zama ajali, nidai kawai rokom da Nike muke ku yafe min nasan na cutar daku na iya cuta har Wanda bakusani ba Nina zuba ma mahaifin mijinki guba a cikin abinci sbda tsanar sa nake masa,kuma nama Abdullah asiri sbda kar yacigaba a rayuwa ban kyale sa saida Naga na lalata masa rayuwa bashida komai tukun, yanzu gashi shine mai taimakona tafada tana kuka da kyar don kukan ma yaki fitowa Sam, shikanshi malam bukar ban barshi haka ba saidai naje gun boka na mallekesa na hana shi auren kowace mace bayan ni duk kina tunanin wadannan hakkin na alumma zasu barni zauna lpia bayan kuma wasu alummar Dana cuta sakkayyace take bibiyata" , ta kwalle mamy wacce idon ya kumbura sbda jin abinda falmata ke fada.

Fatima ku guji zalunci duniyar ba komai bace wallahi nigashi yanzu tawa tazo karshe Dan Allah kobayan raina ku rike min yayana Amana naso Naga auren su Amman hakan ba mai yiyuwa bane, rungume ta mamy tayi tana ya isa haka munyafe miki Allah y yafe miki shima bazaki mutu yanzu ba insha Allah kidefadan haka,meenal dake tsaye bakin kofa jin  abinda falmata tadafa yasa kafafunta suka fara rawa ban go tadafa da kyar takoma falo tana zauna jabar.

Mamy sundade haka Jim falmata tasake ta takoma ta kwanta yasa takalleta ganin idonta a bude kamar sun kafe yasa tayi sauri jijjigata Amman saigani tayi ta sankare mikewa tayi a tsorace tana kiran abba da saurin ya karaso yana lpia, cikin kukan tashin hankali tace falmata  amman takasa karasawa sakamakon wani kuka daya taho Mata.

Shiga dakin abba yayi Amman yakasa karasawa ganin falmata Allah y karbi abinsa salati kawai yake maimatawa jikinsa na rawa,

Shigowarsu kAwu kenan rike ledar magunguna sai sakin ledar yayi ganin yanayin mutanen gun suke ciki bai ma tambaya baasi ba shima yakoma jikin ban go yana dafe kansa,

Adama kuwa tana ganin mamy daman tafito a gigice tasan Allah yayi ma mahaifiyarta rasuwa jitayi komai nata ya tsaya lokaci guda ta yanke jiki ta zube, da sauri aka zuba mata ruwa ta farka ta kuka sosai.

Nan da nan gida yacika sutura akamata aka mata sallah batareda bata lokaci ba aka dauke ta izuwa  makwancinta (Allah y gafararfama wa enda suka rigamu mutuwa) duk zazzaune suke sun sha hijabai sai shigowa ake ana musu gaisuwa su ummie da alhaji suka shigo kowa jikinsa a sanyaye don mutuwar ta girgizasu sosai don babu wanda yaba falmata mutuwa.

Yakarin hakuri amsawa sukayi cikin da sasshiyar murya haka mutane suka dinga shigowa har dare, mom kam kamar ita akama mutuma jikin ta yayi sanyi sosai takara saduda na neman yafiyar ubangiji,meenal da kasa Dena kuka Idan ta tuna lokacin zaman su da falmata Kai rayuwa kenan Yanzu kuwa babu ita, (-hmm inde duniya ce da haka kowa zaya Barta Allah kaimana kyayyawan karshe)

Mutane basu sarara da zuwa ba saida akayi sadakar ukku tukun Ranar su mamy suka koma gida tareda adama bayan an kulle gidan falmata, mutuwar falamata ta Balain taba mom jikinta yakara sanyi sosai takara neman yafiyar su mamy kuma sunyafe mata abinda ke damunta kawai yaranta basa Kula ta.

Fatima hankalina yakasa kwanciya yau kwana hudu kenan yarana basumin magana kamar ma sun tsane ni wallahi insonsu sosai sbda sukadai gareni Dan allah kutaimaka kushawomin kansu,

Ajiyar zuciya mamy tasauke tace kibarsu suhuce yanzu Dan gaskiya sun dau zafi, kinmusu babban laifi kinsan mahaifi fa kika kashe musu  kika  Maida su marayu karfi da yaji,Amman zasu yafe miki ke mahaifiyarsu ce kije kuma ki ta tubanma Allah, Allah ya yafe mana baki daya,

nagode Allah yasaka miki da alkhairi hakika kin cika mutum ban taba gamo da mutum me kyayyawar zuciya ba irinki, mutum Mai saurin yafe sharri saike Allah y biya ki da aljannan firdausi kuma zanyi koyi dake insha Allahu.

Motarta tashiga ta koma gida, wani sabon tashin hankalin ta iske ganin su maleeka sunyi parking Itada maleek sunfiffito da kwatinan su waje sun kwashe komai nasu meena na rike da mus' ab tana rokon maleeka,

Haba aunty kiyi hakuri ki yafe ma mom Dan allah karku tafi kubar mu anty wallahi binki zanyi bazan zama babu ke ba plss aunty tafada ta kama mata fada,

Itakuwa maleeka kamar Kara tunzurata take kallon maleek tayi tana shiga mota ta firzge kafarta daga rikon meena tana kokarin shiga mota durkushewa meena tayi tana kuka sosai tareda kan kame mus'ab shima kuka yake ganin mahaifiyarsa tana shiga mota.

Mom tasauko a guje tana me meye hakan kuma kukeyi, maleeka tace zamu tafi Inda zamuyi rayuwa cikin kwanciyar hankali ne tinda baki kaunar mu baza mu iya zama da ke ba driver ja muje,

mom tare gaban motar tayi tana kuka sosai kamar Ranta ze fita saidai kutakani ku wuce yakukeson nayi da rayuwa na wallahi in kaunar ku har cikin raina karku tafi kubarni karku manta ni mahafaiyar kuce Idan kuka tafi na tabbata bakin cikin ne zai kashe ni....kuka sosai takeyi mai taba zuciyar mai karatu

Maleek har cikin kokon ransa yakejin kukan mom Dafe kansa yayi zuciyarsa na karyewa jinkukan mahaifiyarsa..........

Ohhh ni yasmeen wai yakikeso na miki ne meenal tinda mama falmata ta rasu kika Dena cin abinci sai kuka ko adama fa ta dangana balle ke,

wallahi madau nike tausayi gashi beyi aure ba yazaiyi da yaruwarsa tafada tana share kwalla

Hmmm nikan nakasa gane miki keda madau dinnan nace ki yarda sonsa kike Amman kinki, so fa na tareda tausayi Allah kuwa

Nifa ba sonsa nake ba kawai tausayi yake bani, tafada tana hararar yasmeen da jajayen idanunta,

Yesmeen yazanyi da raina maleek yaki saurarona kwatata baya min mgna abin yana cumin tuwo a kwarya wallahi abinda na damuna gashi yanzu Naga kamar meena yakeso kuma har nafara jin kishin kishin din auren su har lokacin kwalla ne a idonta,

To miye naki kekam  bakinada murad ba kibar suyi auren su mana tinda bake yakeso ba, kuma kishare shi shima tinda yashare ki kema

Fashewa meenal tayi kawai tayi da wani kuka Wanda ita kanta batasan dalilin shiba

Mikewa yasmeen tayi tace zandawo gobe in kingama kukan ya Ayman najirana a waje, tafitowa taganshi zaune shida adama sunata fira yana sakata dariya duk tamance damuwarta ma...........

To next chapter akwai daru fa........ iya commemt iya update

Allah y Jikan falmata ya gafarta mata

Shin  su maleeka zasu amince su dawo ko kuwa tafiya zasu yi?

Shin MALEEK zai amince da auren meenal?

Kubiyoni next chapter Don ganin yanda abin zai kasance.

Comment and share plss

Mrs Abdool ce

Continue Reading

You'll Also Like

85.1K 9.2K 14
Ku biyoni don jin Labarin Hauwa... Its a True Life Story... Kyauta ne, ba na siyarwa ba ๐Ÿ˜‰ Its Free Y'lls โ™ฅ๏ธ
59.8K 4.5K 78
Najib yaron littafin bai dda buri da aaddu'a sai ta Allah yaya bashi mace ta gari mai ilimi Sumaiyya Yarinya ce yar karya wacce ba abinda ta iya sai...
127K 7.2K 45
Complicated๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค Find out๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
1.2M 37.1K 100
Matar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan