maleek 69_ 70

1.3K 57 2
                                    


  69_ 70

NOT EDITED

"Zaman yan bori tayi a bathroom din ta jingina da kofa, itakan kanta tarasa kukan me takeyi ma, jitake kirjinta mana zafi sosai don taci kuka har ta gode ma Allah, tana Ana knocking yafi sau dari Amman tail budewa sbda tabason ganin kowa.

Many ce ta taho rike da spare key tasa ta bude kofar, kallon meenal tayi Wanda tama fuskarta daje daje da kwalla idon nan kuwa kamar jini, cikin daurwar fuska babu alamun wasa kwata kwata mamy tace miye hakan kike yi wallahy Idan baki Mike kika wanke fuskarki ba ranki zeyi mummunar faduwa sakaryar banza kawai, cikin tsawa tace zaki tashi kokuwa!

Ganin fuskar Many babu alamar wasa yasa tafara kokarin mikewa tana share kwalla, jitayi wata muguwar juwa ta debe ta, kafin ta dafa bango har takai kasa, maleeka ce tayi saurin rike ta tana salati fitowa da ita akayi aka yayyafa mata,

Kokarin bude ido tayi Amman takasa kasancewar wani uban nauyi da idon yamata, ga wani mugun zafi da jikinta yayi, waya akayiwa murad da sauri yakaraso ya mata allurai yasaka mata drip da maguguna bai dadeba Jim anata kiransa a waya sosai nu musu magungunan yayi yace bace zai wuce.

Maleek kuwa sha hotuna babu karya daga can kumu suka wuce wani babban hall Inda zaayi reception abinine kala kala da drinks sai kazaba wanda yamaka sannan amaka serving.

Bayan ruwa ya kare tacire Sannan tasake wanka sai a lokacin taji karfi ajikinta ga kuma gida cike da alumma harda kawayenta da sukazo mata biki harda su husna da hanan duk sunzo biki (na littafin sakamako).

DA yamma wani shirin suka sakeyi wannan karoncikin gowns masu Balain kyau sosai kasancewar suna shirin dinner da mom tahada musu,

Meena na hango Ana ma make up tayi kyau sai kace yar tsana, cikin gown gold colour wacce ke jan kasa,tasha sarka da dankunne da bangles, zobe harda sarkar kafa duk na zinari asamin kyauwun da Allah yamata ya futo sosai, haka adama da Zahra duk sunyi sai kusan karfe takwas na dare akamaga shiryasu,

Meenal kuwa babu yanda baayi da itaba Amman tace babu inda zata bata lpia haka sukayi hakuri suka kyale ta, motocine ubansu aka fake a kofar gida Wanda itace zata kwashe Amaren zuwa dinner,

Karas karsa najiyo wanda karar ita taja hankalina nayi saurin juyawa mom na hango cikin wata iriyar shiga ta alfarma wanda inka ganta sai kace sarauniya ce, tasha ado da zinari ga wani less kalar baki da golden wanda yakara hasko kyayyawar fuskarta, ga wata jaka ta ratayo wanda akalla kudinta zai Kai naira dubu dari biyu da yan Kai, wata sarka na hango a kafarta wadda itace ke Sanar da mutane zuwanta kafin takaraso Kai masha Allah mom tasha kyau.

Itama maleeka tagama shirinta cikin cikin gown din material mai Balain tsada tasha makeup sosai inka ganta sai kayi tunanin wata zukekiyar budurwace,

DUK kowa yagama kammala shirinsa sunshiga motoci don zuwa gurin Dinner.

Bayan drivers sun sauke su suka nufo hall din, wani katafaren hall ne mai masifar kyau anmasa decoration ba karya kana gani kasan bakaramar dukiya aka narka a gun ba, guri duk suka samu suka zazzauna a Inda aka tanada.

Kawa yagama hallara shigowar couples din kawai ake jira, canza salon music din akayi zuwa na soyayya Inda couples din suka bayyaba sun sha har sunkoshi clapping aka shiga yi har suka zazzauna a Inda aka tana darmusu daga nan programs kuma yafara.

Ankira Amaren da angunansu su tattaka, daga nan kuma aka kira sauran audience, yan home of novels na hango a tsaki yar hall sai Tikar rawa suke ido akan Amira madobi yafara sauka Itada zahraty sun sha ankon material sai zanku suke bazawa ana musu tabi, daga gefe ma Fatima walah ce itama rawarta take bakin rai bakin fama, hangawa nadingayi naga banga maman abdallah ba ashe baban abdalah ne yahata zuwa dinner tanacan taci kukan ta bakarya.

"MALEEK"Where stories live. Discover now