"MALEEK"

By mrs_Avbdool18

39.3K 2.8K 81

labarin soyyaya ne tsakanin mai kudin da mulki dakuma yar talakawa Inda mahaifiyarsa tace bazaya auretaba sa... More

preface
MALEEK 01
MALEEK 02
MALEEK 03
MALEEK 04
maleek 5
MALEEK 06
MALEEK 07
MALEEK 8
MALEEK 09
maleek 10
MALEEK 11
MALEEK 12
MALEEK 14
maleek 15
maleek 16
MALEEK 17
maleek 18
maleek 19
maleek 20
21 A tsawace tace Kai nake sauraro, to wallahi kashiga hankalin aure maleek 21
maleek 22
maleek 23
maleek 24
maleek 25
maleek 26
maleek 27-28
maleek 29-30
maleek 31-32
maleek 33-35
MALEEK 35_36
MALEEK 37_38
maleek 39_40
maleek 41 _ 42
maleek 43 _ 44
maleek 45 _ 46
47 _ 48
maleek 51_ 52
53 _ 54
maleek 55 _ 56
maleek 57 _ 58
maleek 59 _ 60
maleek 61 _ 62
maleek 63 _ 64
maleek 65 _ 66
maleek 67 _ 68
maleek 69_ 70
HUMEYRAH

maleek 49 _ 50

486 41 0
By mrs_Avbdool18


     49 _ 50

Not edited

2yrs later

Haba maleek wai  ni ya kakeso nayi da Kai ne eye, nidai nayi iya abinda zan iya zan iya yi maka Amman ka kasa hakuri, sheraka  biyu da yan kai ai ba wasabane kilan ma ta manta da Kai a rayuwa me yiyiwa ma tayi aure,

Lumshe ido maleek yayi yakoma ya jingina da kujera,duk yazama abin tausayi kallo daya zaka masa kagane muguwar ramar da yayi kamar bashiba ga kuma rashin kwanciyar hankali karar a fuskarshi,

Da kyar yabude baki yace sis me kuma nayi nifa bance komai ko kinganmu Ina kuka ne nace miki nadena fa kuma tin daga nan bansakeba, kuma mgnar meenal kiyi hakuri Amman nasan har abada bazan taba cire meenal araina ba kuma Kullum zuciya ta nagayamin meenal tananan kuma zan ganta da kaina tan nan tana jira na kamar yadda nima nakejiranta,

Kallon anya kasan abinda kake cewa kuwa take masa,

Kamar koya yasani yace sis nasan abinda nakeyi kuma zaki ce nagaya maki,yana gama fada ya miki ya wuce daki abunsa yakulle kanshi,

Tagumi maleeka ta zuba tace ohhni nashiga ukku wai yanzu haka rayuwar yarannan zata kasance, toh Allah y kyau ta ya kawo mafita.

Muhassin yana zaune a folon maleeka bayan  sungama gaisawa tace ya madam din,

Dan Sosa Kai yayi yace she's fine,

Daman sis abinda yakawoni shine nifa alamarin maleek yana Bani tsoro Sam yadena mgna baya Kula kowa daga masallaci sai daki, duk yabi ya rame, ya lallace nikaina fa gaisuwa kawai ke hada ni dashi and that is all shifa aganinshi nasan Idan meenal take Bana son gyamasane, ya tsane ni kwata kwata yana min mgna me ma badon yanasoba,sbda mace Kai gaskiya da sake dole musan abinyi kafin issue din yazama out of hand.

Kaga muhassin I  have do my best bansan kuma me zansakeyiba nide Ina masa addua and that is all,Allah y shige mana gaba,

Amin ni zanwuce Sis, agaisheda mus'ab

Murmushi tayi tace zeji yana gurin Nanny dinsa, Ka gaidamin samha Inan zuwa insha Allah.


Dandazon al'umma ne yara da manya sai ihu suke a kofar wani gida kana de ganin gidan kasan gidan hayane,  tsakiya kuwa mata biyu aka basu fili sai dambe suke Bana wasaba, can na hango falmata ancire mata zani daga ita sai Dan skirt, matar ta kai kasa tana cigaba da nusar mata baki daga hannu tayi da karfi ta kaimata nushi a hanci, nan da nan hanci ya fashe jini da yafara gangarowa mutane sai kokarin rabasu suke Amman sunki,

Wasu samarine suka cikin zafin nama suka Janye falmata, tana huci ta kama kugu tana girgiza tace billahillazi yarinya ta kara zakina taga yanda zan ragargaza bakin ehe, tafada tana huci

Korar yaran samarin suka shiga yi suna watsewa,

Horn din mota yasa falmata shigewa gidan da gudu, mutumin na shigowa gidan cikin fushe yana,ramu kina inaa,

Jin shiru yasa yashige dakin kwance yaganta an lika mata auduga ga hanci, meye haka kuma ya tambaya fuskarsa a murtuke,

Kuka tafashe dashi tace mai gida gaskiya banzan iya zama da wannan mahaukaciyar matarba, wai daga su bara'atu sunzo shine suna tafiya tashigo har dakina ta cakumeni da dambe wai muna tamata habaici,

Cikin tsananin fushi yace shine sbda ku Tona min asiri zaku fita titi kuna dambe ko,

Fita yayi a fusace ya tsaya tsakar gida yana kwala ma falmata kira,

Fitowa tayi taci damara a kugu tana wai ubanwaye ke kwala min wanann kiran sai kace a mahauta,

Mutumin baibi takantaba yace Ina son yanzu basai anjima ba kitattara ki ki barmin gidana don banzan iya da masifa, Don ke wallahi annobace tinda kikazo kika watsa min gidan Kullum cikin tashin hankali daga taimako,  To ko minti 5 ban son ki kara maza ki kama gabanki ki koma Inda kika fito matsiyace,

Ya mutsa fuska tayi takoma ciki tana inga ubanda za fiddani ehe,

Samarin dazune daya mai kimanin shekara 26 daya kuma 24 suka shigo dakin ta suna kwasar kayan ta suna watsawa waje saida suka kwashe komai Sannan suka rufe gidan kwado, 

Umma tagaida assha Allah y raka taki gona mudai abarmana gidan mu gara muyarda kwallon mangooro kila murabu da kudi,

Falmata tace tafi nono fari sai me Dan nabar wanan akulkin tafada tareda kwashe kayanta sukayi waje adama na biye da ita.

A bakin wani madaidaicin flat me kyau suka sauka, kwankwasa wa tashigayi wani yaro yabude mata, cewa tayi kiramin me gidan, yace to tareda wucewa,

Badadewa saiga kawu Sanye cikin manya kaya yafito, yana bude kofa yaga falmata yabuga uban tsaki yaja kafarsa ya rufe,

Sunaji yana ma mutan gidan gargadi karwanda yasake bari matar nan tazo Mai gida,

Haka suka karaci zaman su ganin ba alamar nasara yasa suka Mike suka gaba.

Meenal da dadawowarta kenan aiki ranar around five, taji Ana knocking  mikewa tayi tabude kofa,still tayi tareda zaro ido tana Dan komawa baya tanason rufe kofar,

Yaken dole falmata tayi tace meenal bude mana mushigo mana,

Bude musu tayi suka shige ciki har lokaci tana tsaye bakin, ahankali ta tura kofar gidan tadawo cikin falon ta zauna,

Bakinta na Dan rawa tace inawuni mama, daga ina kuke haka tayi tambayar da mamaki karara a fuskarta,

Kwallane ya fara kokarin zubo mata tana dannewa

Mamy da itama fitowarta kenan daga daki tayi still daga Inda take tana kallon falmata,wadda bata da maraba da mahaukaciya don inbaka santaba sai kace mahaukaciya ce sabon kamu, duk sunyi datti ga wasu kaya a buhu, gakuma ramar yunwa,

Karasowa  mamy tayi tadake tace falmata ke ce nake nake gani haka kuwa, daga ina da yamma haka,

Kwalla tashare tana don girman Allah Fatima kiyafe min wallahi nasan hakkin ku ke bibiyata tafada tana kuka sosai,

Ajiyar zuciya mamy ta sauke tace yanzu de ajiye wannan gefe bari akawo muku abinci tukun don Naga kamar yunwa kukeji ko,

Da sauri adama tace eh wallahi Rabon mu da abinci tin shekaranjiya,

Abinci aka zubo musu shinkafa da miya ga kuma salad a gefe da farfesun naman rago, wani uban miyau falmata ta hadiye kamar mayya tareda da matsowa kusada kwanon abincin don rabonta da irin wannan abincin har ta manta.

Cokali tasa tafara diba  tana kaiwa baki, ganin kokalin ze bata mata lokaci yasa ta duma hannu ci take ba kakkautawa,

Mikewa meenal tayi ta dauko chill five alive tareda ruwa ta aje musu, ai falmata bata ma jira cup ba ta balle kan tacigaba da kwankwada,

Saida suka cinye abincin tass, tayi gyatsa takoma ta jingina da kujera,

Meenal wacce sekace tasamu tv haka take kallonsu,

Zanyi fitsari cewar adama, mamy tace kaisu boys quarters su aje kayansu da sai suzo mu tattauna,

Toh tace tareda mikewa suna biye da ita a baya kalle kalle kawai sukeyi a gidan, bude musu dakin tayi takoma part dinsu.

Saida sukayi wanka sannan suka fito suka koma part din su meenal, sai a lokaci suka sanyi pasali, zama tayi akasa Itada adama

Mamy tace falmata daga ina kuke, Ina kawu Ina madou?

Labarine mai tsayi, tace bayan rabuwarmu abubu dayawa sunfaru, Sabon rashin mutunci da gori tsiya ta yau daban ta gobe daban haka nakema kawu, Ana nan daman adama tanada saurinda take so har anyi maganar auren su, Ana haka saiga wani alhaji ya fito na bade idona tsab nace sai shi matansa ukku itace ta hudu kawu yace bazata aureshiba nikuma nace shizata aure, na nashiga nafita saida nayi yaddanayi alhajin nan ya aureta bayan ya narkamin uwar dukiya, haka kawu yaba saurayin hakuri yawuce, watansu 5 Kacal da aure yasaketa kishiyoyi da uwar miji sun sata gaba ga yan dauke dauke da nasata tarinka yi,

Bayan ta dawo gida mukayi fada da kawu yace tinda na kashe mata aure Nima intafi ya sakeni,  daman kafinnan yabani sharadi akan duk randa na kashema adama aure to nima nawa ze mutu,haka nattara ta muka tafi naje na auri wani alhaji mai mugun kudi duk naraba shi da matansa karshe nima yasake ni ashe kanjamai ne dashi gashi nima ya gogamin tafada tana fashe wa da kuka

Bayan yaje asibiti an gwada shi yace nice na shafa masa yamin duka sannan ya koreni bai barni na dauki komai ba haka muka tafi muna neman haya kowa sai yace bazai bani haya ba, da kyar wani mutumi yabani wani bangare a gidansa muzauna Ina biyansa 20k a wata, nan nafitinesa Kullum sai munyi dambe da matarsa nahasa zaman lpia Balain yau daban na gobe daban, haka shima ya gaji da halina ya koreni,

Nakoma gun kawo ya koreni yace baya San Kara ganina ma, kuma yayi aure yanan da matarsa gashi yayi kudi harda mota tafada ya kara fashe wa da matsanancin kuka mai cin rai,

Bayan korar mu haka muka dinga gantali a titi kamar marasa galihu  duk indanaje gidan kawayena sai su koreni wai basuda gurinda zasu ajiyeni, da kyar nasamu wata taimakamin da gurin kwana ba abinci.

Don girman Allah ku yakemin ko nasamu sauki, nasan nacuci mutane kuma hakkinsu bazai barni ba,gashi nayima kaina na Yima yata yanzu gashi can sauriyinta yana kaduna yayi kudi da matarsa, na kasa hakuri yanzu ga malam bukar can cikin daula nashiga ukkuna don girman Allah ku Maida ni WAllahy inasonshi sosai,

Mamy datayi shiru cikin jimami yace to Ina madou, madou yatafi karatu waje ance yagama Amman har yanzu bansaka shi a ido na ba, kuka take sosai kamar Ranta ze fita,

Meenal ta goge kwallan dake idonta tace mama ai ni tini nayafe miki,Allah y yafe mana baki daya,

Fatima baki ce kinyafe minba,

Mamy da idonta yayi ja tace nayafe maki duk abinda kikamin, Amman kina nufin kina daukeda cutar kanjamau,

Gyda mata tayi tana share hawayen da suka kasa Dena zubowa, da jajayen idanunta ta kalli mamy tace don Allah Fatima kutaimakemu muzauna tareda ku zanrika muku aiki kuna bani abinci Dan Allah,

Mamy tace to a yanzu de kuzauna Amman gaskiya zaman nan bezeyiba zamu same kawu akan maganar maidake Idan zai iya, za dai ku zauna kafin musan abinyi.

Kingani falamta abinda Nike nuna miki kenan duniya bata da tabbas, Idan yau tayi da Kai to gobe da wani zatayi, Amman ki Kadauki dogon buri kika saka ma kanki yanzu kinga yanda kika kare ai Allah yasa dagaske kin tuba ba tubanmazuru kikayiba, gashi yanzu gashi kin cuci yar ki da kuma kanki kin Gaza hakuri gashi yan zu kawo nacancikin daula,  ke kuwa abincin dazakici na gagararki,

WAllahi Fatima dagaske nayi nadama naga izna duniya tamin hankali, shiyasa akace karka wukanta kowa,bakasan wanda ze taimakekaba gashi ku dana wulakanta kuntaimake tafada cikin kuka.....

Yanzu de ya isa duk wannan yawuce kigode ma Allah da kika gane laifinki kika tuba yanzu Cewar mamy.

Meena ce Janye da yar Jakarta mai taxi ya sauketa kofar gidan su maleek tsoron shiga take don batasan yanda mom zata dauki zancan ba,

Asanyaye take tafiya tana Janye da Dan Karamin kwatatin tana zuwa tasakiya gidan suka kusa karo da mom kallon ta mom kawai takeyi,still tayi ta zaro ido meena  kirjinta na dukan ukku ganin irin kallon da mom ke mata, wani abu tahadiye da kyar tareda dafe kirjinta.........


Mrs Abdool ce........

Continue Reading

You'll Also Like

4.6M 293K 106
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
7.1K 132 7
Look rayhana ni nan da kika ganni babu abunda baxan iya yiwa namiji ba idan har zai bani kudi, dan haka ki bar bata bakinki waazinki baxai taba sakaw...
1.3M 68.4K 59
π’πœπžπ§π­ 𝐨𝐟 π‹π¨π―πžγ€’ππ² π₯𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐑𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐒𝐞𝐬 γ€ˆπ›π¨π¨π€ 1〉 π‘Άπ’‘π’‘π’π’”π’Šπ’•π’†π’” 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 ✰|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...
4.1M 170K 63
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally ❣️ Cover credit...