"MALEEK"

By mrs_Avbdool18

40.9K 2.8K 81

labarin soyyaya ne tsakanin mai kudin da mulki dakuma yar talakawa Inda mahaifiyarsa tace bazaya auretaba sa... More

preface
MALEEK 01
MALEEK 02
MALEEK 03
MALEEK 04
maleek 5
MALEEK 06
MALEEK 07
MALEEK 8
MALEEK 09
maleek 10
MALEEK 11
MALEEK 12
MALEEK 14
maleek 15
maleek 16
MALEEK 17
maleek 18
maleek 19
maleek 20
21 A tsawace tace Kai nake sauraro, to wallahi kashiga hankalin aure maleek 21
maleek 22
maleek 23
maleek 24
maleek 25
maleek 26
maleek 27-28
maleek 29-30
maleek 31-32
maleek 33-35
MALEEK 35_36
MALEEK 37_38
maleek 39_40
maleek 43 _ 44
maleek 45 _ 46
47 _ 48
maleek 49 _ 50
maleek 51_ 52
53 _ 54
maleek 55 _ 56
maleek 57 _ 58
maleek 59 _ 60
maleek 61 _ 62
maleek 63 _ 64
maleek 65 _ 66
maleek 67 _ 68
maleek 69_ 70
HUMEYRAH

maleek 41 _ 42

508 39 0
By mrs_Avbdool18

       41 _ 42

Not edited

Falmata da tahango sabbin kudin sun watse kasa, zaro ido
tayi kamar tayi hauka tace lalle yasin bugun abujane, lokaci guda tashiga wani rudani tarasa yanda zata fara kashe kudin,

Dafe Kai meenal tayi cikin azaba jini sai zuba yake a goshinta mikewa tayi tana layi, ta kalle kasa kudin da suka watse ko ta kansu bata bi ba, complemary card din da alhaji yabata kawai tadauka,

Madou yashigo gidan yakaraso a rude yana subhanallah meenal lapia meyasa meki,  saurin rike mata hannu yayi ganin kamar zata fadi,

Afusace tajuyo tamaka masa wani mugun kallo tace "let go of me now" atsawace jiyowa tayi tace "mama basai kin hallaka niba nasan su kike mawa, u can have it cos I have noting to do with dem"

Tashige daki batare da Kara kallon kudinba,

Many tace meyasame ki meki meenal a rude, da kyar meenal tace mamy I mistekly fell down, how cames to kamar bakya gani,

Dasauri da tadauko spirit da cotton tamata dressing gun tasaka mata plaster.

Kawu daya dawo daga rakon alhaji yaga falmata sai wawusar kudi take tana cusawa cikin zananta, 

Sakin baki yayi yamata kallon mamaki,

Tana ganinshi ta fashe da kuka tana nashiga ukku wannan cin mutunci har Ina, malam kana kallo yarinyar nan ta watsa min kudin ajiki wai gasunan mune matsiyata yiiyiii haka tacigaba da kuka kamar gaske,

Wani uban tsaki madou yasaki yafita ransa a bace yana mamaki halin mama, shima kawo tsakin yasaki tareda shigewa daki,

Ya mutsa baki falmata tayi tace oho dai nade nasamu kudi banyi aikin banza ba ehe.

Daddare bayan Abba yadawo meenal tabasa card din tana masa bayanin yanda sukayi da alhajin,

Yace to shikenan daman kawu yamin bayani dazun insha Allah zuwa jibi zanshirya natafi don gwada sa'a kunsan ance sai an gwada ake gane na gari,

Cike da murna mamy tace Allah de yasaka ma wannan bawan Allahn da alkhairi, Allah kuma ya tabbatar da alkhairi.

Muhassin na kwance suna waya da fiancee dinshi

Dear kasan wani abu ta tambayeshi da yaren turanci

Ehen am all ears,

Dad yace Indai inada Wanda nakeso namishi mgna don aure zemin, sbda  kasan Nagama karatun, kuma daman fa baka taba zuwa ba,

Kiyi hakuri dear insha Allah zanzo Amman inada issues din da nake son nayi settling but nan da less than a month zaki Ganni

Haka suka dinga fira at last ya Mike yashirya don zuwa asibiti,

Parking yayi a farfajiyar asibiti yafito rikeda fruit a leda,  dede zeshigo asibitin yaga Ana fita da gawar sholy, still yayi a bakin kofar gurin yabinta da kallon tausayi, wasu kwalla ne yaji suna niyar fito masa, dasauri yakarasa kusada wata mata daketa sharbar kuka, yace were a they taking her to, matar da idonta yayi jajur tace she's late tana Kara fashe wa da kuka, muhassin ji yayi kafarsa yagaza daukarsa da kyar yace may her gentle soul rest in blossom of God yana share hawaye, thanks nagode tafada tareda wucewa,

Yadade a gun yakasa tafiya yama rasa meke masa Dadi lokaci daya meenal tafado masa arai,  Indan meenal taji mutuwar sholy ya zataji,  wucewa yayi jiki a sanyaye yashiga ward din maleek,

Maleeka da ganin yanayinsa tamike da sauri tana, is something wrong, wasu kwalla ne suka Dada sakko masa, a rude maleeka ke kallonsa tace plss talk to me am confused,
A friend of mine is late I just saw her corpse Ana fita dashi,

Maleeka tace Ayya hard luck Allah y jikanta

Yace ameen A sanyaye, ya jikin maleek

Alhamdullh he is improving Ana samun cigaba yanzu kan, ko Dan yaji zaa tafi neman meenal ne oho

Dariya Taso ba muhassin yace haba sister maleek da bemasan abinda muke cewa ba yaushe yaji wannan,

Tabe baki tayi tace bar wannan lover boy din kawai, Allah zaka sha mamaki kaga yanzu ya kike yaga meenal gaban sa,

Murmushi muhassin yayi yana matsawa kusada gadon maleek.

Tinda asubah around 6 Abba yagama shirinsa da yar jakarsa Karama ya dauki duk CV dinsa, yana zuwa park ba dadewa mota tacika suka kama hanya, tin abba najim dadin tafiyar har yagaji don tafiya ce bata wasaba, suna zuwa kano suka tsaya sukayi salloli Abba yadan samu abu yasaka ma cikinsa wani abu, kafin suka Kara kama hanya basubane suka sauka  Abuja sai around 8pm na dare.

A jabi park suka sauka, waya sukayi da alhaji ganin dare yayi yace gaskiya mota zata maka wayar samu kuma  mun fita driver baya nan Amman bari murad yazo ya dauka, toh alhaji godia nake Allah y saka da alkhairi,
No bakomai just find some were safe and wait.

Yana Zaune a park kamar 1hr haka saiga murad ganin mutum tsaye da jaka shi kadai yasa yagane shine, sauka yayi yaje kusada dashi ya bashi hannu suka gaisa cikeda girmamawa,

Wata mota mai mugun kyau suka nufa shi murad ya zauna maxaunin driver shikuma Abba yashiga dayan Gefen, tafiya me Dan tsawo sukayi Abba yaga sunshigo wata unguwa mai mugun kyau shiru take babu ko babura, saidai fitin streetlight da suka ma gurun ado,

Gani yayi sunyi horn a bakin wani kantamemen gida, nan da nan aka bude masa gate ya kutsa Kai cikin farfajiyar gidan duk da dare, Amma hakan baisa Abba rashin ganin kyaun gidan ba kasacewar fitulu sun Haska ko ina, murad  ya zagayo yabude masa tareda karbar jakarsa, gaba yayi abba nabiye dashi abaya,

Adede bakin kofar gidan Wanda Ginin yakasance gidan bene sukayi knocking, wata ce wadda kana ganinta kasan yar aiki ce tabude musu kofa, kutsa Kai murad yayi cikin falon tareda ma Abba iso, duk abba bawai farin shigarsa gidan masu kudi bane Amman baiyi tunanin gidan alhajin yakai haka,

Wani sassayan kamshine mai Dadi yamasa sallama, shiga yayi ya zauna kan daya daga cikin royal chairs din yana bin haddaden falon da kallo, murad ne ya haura sama tareda sallama ya tura dakin ummyn shi, kan sallaya yaganta

Durkusawa yayi har kasa yana, ummie barka da dare barka de murad kundawone eh ummie yana falo, toh bari naje mugaisa tafada tareda mikewa cikin hijab dinta,

Abba dake zaune yana kallon kantamemiyar tvn dake aiki, yajiyo alamar tafiya a steps yana daga kansa yahango wata kyayyawar mata wadda shekarunta bazasu wuce 45 ba kyakyyawa ce sosai gata fara sol, karasowa tayi fuskarta daukeda murmushi,

Gaisuwa sukashigayi da Abba cikin girmamawa, tace gashi kazo alhaji baya nan yaje meeting karfe goma ze dawo, dining aka kaishi Inda aka shirya abinci kala kala zuba iya Wanda zeci yayi yaci don ma baya jin yunwa don agajiye yake,

Ummie ta kalla murad ciki yaren fulatanci tace kakaishi daki kila yagaji yana son hutawa, daukar jakar abba yayi abba yabisa suka nufi wani matsakaicin part mai kyau key yasaka yabude, part din ko ina a tsabtatace yake yashiga ya aje ma Abba jakarsa, yace Abba Idan akwai abinda kake bukata kamin waya, toh murad nagode Allah shiyi albarka.

Abba binsa yayi da kallo yana shawar yaron don akwai tarbiya da ganin girman manya, mikewa yayi yashiga cikin dakin komai a gyare yake toilet yashiga yayi wanka tareda yin salloli yana gamawa yakira mammy bai wani Dade ba bacci yayi gaba dashi Don dama agajiye yake.

Washegari bayan sallahn asuba sake komawa yayi gurin 8am yaji kamar Ana buguwa fitowa yayi yabude kofar da murmushi ya kalli saurayin sai kuma yaga Bana jiya bane amman de suna kama sai kuma yaga kamar najiya shine babba,

Ina kwana abba y gajiyar tafiya, Alhmdullh cewar Abba yana sake kallonshi, yace ni sunana Ayman kanin ya murad yafada yana murmushi dad yace namaka mgna, ok to inazuwa shiga yayi ya shirya sannan yafito yaga har lokacin yana zaune yana jiransa, tare suka shiga cikin part din dad Wanda yafi najiya tsaruwa,

Karo suka kusa ci da murad ya tsaya yana Abba katashi ya gajiyar jiya tareda mika masa hannu suna musabaha, sai a lokacin abba yakkali nakusa dashinyaga ya Dan dara yayan nasa tsayi shikuma murad yadanfishi haske Amma de suna kama sosai,

Alhamdullh murad, ai da Ayman yashigo nayi tunanin Kaine,

Dariya yayi yace to ai ni gani abba Ina sauri zanje Asibiti yanzu aka kirani ankawo wasu patient,

To Likita Allah y taimaka yabada sa a, Ameen abba nagode yawuce dasuri yana shiga mota.

Zauna suka iske Alhaji shikin shirinsa, nan suka shiga gaisawa da Abba kamar daman sun San juna, Alhaji yajasa dining suka yi lafiyayyan break fast su ukku cikeda nishadi, sai a lokacin Alhaji kecewa Ina murad, Ayman yace dad ai ya fita tin dazaun wai kiransa akayi, ok toh kaifa ba case yau ne, Abba Akawai fa buh sai anjima zanfita,to Allah taimaka,Ameen dad.

Shide abba yana ta kallonsu cikeda shaawa don gaskiya yanayin gidan ya burgeshi sosai.

Alhajj da Abba suka fita tare, saida suka gama processing  komai agunda abba zeyi aiki babu dadewa suka kammala komai abinka da kudi,A hanyarsu ta dawowa Abba yana ta kallon garin don garin yamasa kyau sosai, Alhaji ne yace masa Amman kanada gurin zama koh don gaskiya aiki nan nanda sati daya zuwa biya akeson kafara zuwa gaskiya,

Abba yace babu Amman inason nasiya, toh kashirya siye kokuwa muje sai ka dawo, ah muje kawai gara muyi komai yanzu Dana tashi nasan parking kawai zamuyi,

Awata unguwar suka yafaka itama mai mugun kyau babu ma tazara sosai tsakanin gidan Alhajin suzuwa wannan unguwan gidajene masu kyaun gaske Amman de basukai na alhajiba,

Alhaji ya kallisa yana ce ma Abba kazabi Wanda yamaka acikin su abba yazabi Wanda yamasa mai mugun kyau dan Daidai, Alhaji ba bata lokaci yakira agent dinsa yana suzo zaayi cinikin wani gida, duk batareda bata lokaciba aka kammala komai gida yatashi 5m duk da Abba yasan alhaji yace yabada ne Kawai Amman wannan gidan yatasamma milyan 10 Don gidan is well furnished komai akwai shiga kawai zasuyi.

Mikama abba ta takardun gidan yayi tareda makulli yana cewa Allah congratulations, da murmushi abba yace tanks am greatful.

Murya kam gurin abba har ya rasa Inda zai saka kanshi yakuma rasa da wani bakin zai ma alhaji godia don yagama masa komai a rayuwa, bayan duk sungama duk abinda yadace aranan washe gari abba yace zai wuce Don yaje su shirya, Alhaji kirikiri yanasa hawa mota wai akwai nisa kuma ba security,

Nan da da nan aka gama shirin Jirgi, Ayman yatafi kaisa airport ba dadewa jirginsu yatashi zuwa borno..........


Mrs abvdool ce....

Continue Reading

You'll Also Like

832K 70.1K 59
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zaz...
503K 41.7K 59
MAFARI...komai yana da farko, komai yana da tushe, komai yana da asali, HARGITSIN RAYUWA kan faru cikin ƙanƙanin lokaci. Duniyar daka saba da ita za...
4.6K 129 6
"'Daliba ta a makaranta ze aura" "......Se da na gama kwalliya na sa kaya fa, sannan na fita nayi kwaskwarima na 'dauraye qafa na da hannu na, ni br...
547K 3.4K 6
A story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......