"MALEEK"

By mrs_Avbdool18

40.9K 2.8K 81

labarin soyyaya ne tsakanin mai kudin da mulki dakuma yar talakawa Inda mahaifiyarsa tace bazaya auretaba sa... More

preface
MALEEK 01
MALEEK 02
MALEEK 03
MALEEK 04
maleek 5
MALEEK 06
MALEEK 07
MALEEK 8
MALEEK 09
maleek 10
MALEEK 11
MALEEK 12
MALEEK 14
maleek 15
maleek 16
MALEEK 17
maleek 18
maleek 19
maleek 20
21 A tsawace tace Kai nake sauraro, to wallahi kashiga hankalin aure maleek 21
maleek 22
maleek 23
maleek 24
maleek 25
maleek 26
maleek 27-28
maleek 29-30
maleek 31-32
maleek 33-35
MALEEK 35_36
MALEEK 37_38
maleek 41 _ 42
maleek 43 _ 44
maleek 45 _ 46
47 _ 48
maleek 49 _ 50
maleek 51_ 52
53 _ 54
maleek 55 _ 56
maleek 57 _ 58
maleek 59 _ 60
maleek 61 _ 62
maleek 63 _ 64
maleek 65 _ 66
maleek 67 _ 68
maleek 69_ 70
HUMEYRAH

maleek 39_40

711 45 4
By mrs_Avbdool18

39 _  40

"Da shirinta tsab tafito Sanye da hijab don zuwa yi musu cefene gurin mamy ta karbi kudin bayan tagama mata lissafin abinda zata siyo.

Tafito taga mama zaune tsakar gida tana fice gyada, ko kallon gefenta batayiba bare ma tasaran gaisuwa wucewa tayi har takai kofa tajiyo muryar mama tana to "zaatafi gantalin da aka Saba ko mude kubari saikun koma gidan naku kar ajamana abin kunya a gida ehe"

Meenal de bata juyoba kuma kokadan bata damuba don tasaba da irin wadannan maganganun na mama harda wanda sukafisu ma.

Tanafita ta tsaida Keke napep direct kasuwa tawuce ta musu siye siyen su harda su kwai,Irish,indomie Dade sauransu tana gamawa wani yaro yakowo mata bakin titi tabashi hamsin.

Tadade tsaye bakin titin bata samu abin hawa ba wata arniyar jibce kirar highlander tawuce gabanta, har tawuce kuma motar tayo reverse zuwa sai tinta itade kanta gefe bata juya ba, yayi minti biyar kafin ya sauke glass din kasacewar shi tinted sai da yagama kare mata kallo tukun

Sallama yamata yana Ina zuwa haka da kaya,
Jin ya dameta da suratai yasa tajuyo ta kalleshi a karon farko sai aloakcin taga ashe ma ba yaro bane don babban mutunne amma kana ganinshi kasan kudin sun zauna masa don babu alamar talauci attareda dashi hasalima yana zuje glass din daddadan kamshine mai gauraye da sanyi ya bugeta, saurin dauke kanta tayi gabanta na faduwa, Dan gaba ta matsa daga Inda motar take ahankali shima ya taka motar zuwa Inda take "kinga yan mata kiban nombanki sai muyi mgan kokuma kimin kwatance gidanku sai nazo anjima, yana gama mgnar dede mai napep yazo wucewa tayi saurin tareshi ta shiga ya zuba mata kayanta tace "muje" Alhaji ganin tawuce ma ya tabe baki yana nasoki da murad dina  Amman as she wish fizgar motarsa yayi gaba yabar wajen shima.

Tana sauka gida tabashi kudinshi ta kwashe kayanta da daddaya tana shiga dasu, kawu ta tarar a tsargida yana sauraron radio Dan durkusawa tayi tana "sannu da gida baba", "sannu meenal andawo", eh "baba to barka dazuwa"

Saidata tagama shigar da kayan gidan tawuce dakin mamy tana nuna mata abinda tasiya

Kawu  dake zaune wayarsa ta dau Kara, dubawa yayi yana dauka da hanzari,

"A'a alhajin Allah kenan kwana biyu ya gida ya aiki kuma"

Daga  dayan bangaren akace: "Alhamdullh malam bukar ya naka iyalan dama nashigo garin jiya ne nace in kana nan nashigo mugaisa"

"Ah Ina nan Alhaji ka shigo kawai"

"To masha allah zuwa anjima zanshigo kamar da yamma"

"To Allah ya kawo ka lpia"

Yana kashe wayar ya kwala ma falmata kira, karaso tayi tana wannan kira kuma haka malam lpia kuwa,

Lapiyar cemtakaeo haka maza je kifara shiri Alhaji bello mainasara ne yamin waya yashigo gari,

Falmata da tabata fuska da tawashe hakora Kai yaushe zaizo to kaga daman nayi shinkafa da miya je siyo salad a hada masa kasan tuwon girma miyarsa nama,

"Hakane bari  infita yanzu fadar kawu"

"To harda Dan lemon na kwali duk kahado tafada tana mikewa"  

Bayan kawu yafita babu dadewa saigashi yadawo daukeda leda, ledar falmata tafara budewa tana Kara washe baki, babban kwalin exotic ne da ruwan roba sai yar kaza dakuma salad,

Dauka falmata tayi tanufi cikin kitchen cikin kankanin lokaci tagama hado komai, har kulas sabba akasaka Wanda akafara saima adama na aure.

Mama tashigo daki taga adama kwance tana waya, ke  dalla tashi kiyi wanka kiyi shafa kazama kawai, mama name kuma, mama datayi kasakasa da murya tace Alhajin Abuja abokin babanku zezo kika sani ko a dace koshi ko dansa,

Haba  Mama bade shi ba saidai Dan nasa, to in shidinne miyene toh

Kai mama yafa tsufa , ke dalla Ina ruwanki da tsufansa bakiji ance tsoho da kudi yaroba, maza kimike yakusa zuwa, toh mama, yawwa yar albarka tafita na kwashe yellow teeth dinta.

Kawu dayasa aka gyara Dan karamin falon gidan yayi kyau balaifi sai kanshin turaren wuta ke tashi,

Motace jibgegiya tai faking dede kofar gidan kawu, driver ne yafito dasauri yabude kofar motar baya, wani dattijo ne yafito Wanda baze wuce shekara 56 ba aduniya, ba fari bane Amman kudi da hutu sunsa fatarsa kyalli, kyawwane iya musali Danma girma dayafara kamashi, sanyake yake cikin babbar Riga da yan ciki na wagambari light blue ga hula yar maiduguri ya daura kansa, fitowa yayi cikin takunsa na manya yanufi cikin gidan.

Kawo dake jiran sa yamika masa hannu yana barka da zuwa Alhajin Allah, mushiga daga shiga, Alhaji kwashe rugarsa yayi sama sbda kasa suka shiga falon kawu, kan kujera ya zauna suka hau gaisawa irin ta tight frnds

Falmata dasauri tashige dakin adama tana fito inkingama kifara dauka kina Kai masa, adama dataci kwalliya cikin atamfar roba tasha dinkin Riga da skirt an adauko gyale an yafa, dukawa tayi tadauki tray din lemo da ruwa da cups zata Kai,

Karo sukayi da kawu tai saurin bashi hanya kallon ta ya tsaya yi da mamaki dariya Taso kamashima Amma baiyiba  yagirgiza Kai kawai sanin wanan kadan ne daga aikin falmata, cewa yayi Ina meenal je kirata kukawo tare sai kugaisa,

Turo baki adama tayi tashige daki tace meenal baba yace kizo ki gaida baki, toh kawai tace adama tafita,

Meenal mikewa tayi ta dau mayafin Arabian gown din dake jikinta, babu wani makeup a fuskarta tafito, kawo yace dauki wannan trayn kema ke Kai, toh baba taduka ta dauka, Banda harara babu abinda mama ke binta dashi,

Ta shiga tareda sallama taduka har kasa ta ajiye trayn alhaji dake latsa waya tinda ta shigo ya dago Kai yana kallon ta, dede ta dago kanta ita, gaban tane ya hau dukan Tara Tara ganin mutumin dazun, tunani ne kala kala yafara zuwar mata to meyakawoshinan ko dai bayanta yabi bayan ta taho,

Kawu dake dakallonta, tayi sauri sauke Kanta tana dede natsuwarta cikin sanyin murna tace Ina Wuni y aiki
sannu dazuwa,

A taikaice ya amsa mata Alhamdullh ya makaranta, shima tunani fal zuciya he is even confuse ma,

Alhamdullh tafada tareda mikewa ta fice.

Su falmata tagani zaune waje adama tana turo baki tana gyama mata, mama kinga Dana gaishe shi ko Kai be daga ba balle ya kalleni ma

Falmata tace Wacce aljanar ce tahana Allah y sa itama be kalle ta ba.

Kawu Wanda ya zuba masa abinci yace, Alhaji ya yaran ne anata makaranta ko , yar dariya alhaji yayi yace ai babba yagama tuni yana ma aiki shima karamin yagama ai daman kasan su biyune,

Ok Allah sarki to aure fa suna ta shiri yi ko, Alhaji yace hmm inata fama wallahi ko yan mata basuda shi ma, so Nike kawai na zabo dakaina in aura musu,

Yar dariya kawu yayi yace abarsude sunzaba da kansu sai yafi,

Alhaji yayi Dan Jim yace, wai malam bukar ashe bayan waccan akwai wata budurwar Amman ban taba ganinta ba ko karatu take,

Eh Alhaji bello wallahi ba ta wajena bace atakaice yaba shi labarinsu su meenal yace to su daga misra suka dawo nan, shine suka yada zango kafin uban nata yasumu abinyi.

Allah sarki to Amma baban nata yayi karatu shi inji alhaji, eh yayi de Dan degreen nan da akeyi, itafa yarinyar tayi makaranta, nan ma kawu yace eh tayi a can kasar inji iyayenta wai takaranta likitanci, ok toh yayi,

Alhaji ya kalli kawu yace katambayeshi Idan yana shaawar aiki Abuja nan da sati biyu yazo ya same ni don yanzu sauri Nike gobe zanwucema sbda wasu abubuwa da suka Taso,
Kaga itama yarinyar sai tafara aiki a asibitin Dana bude ma 'Dana damshima abinda yakeyi kenan intana shaawa,

To alhaji insha Allah,Allah de ya Kara girma munata godia Allah yasaka da alkhairi mungode kakwarai,

Am in bakomai malam bukar ai duk Yima Kaine,

Kawu yace bara ma Naturo maka ita sai ka tambeyeta da kanka ma sai yafi yafada tareda mikewa yanufi kofa,

Badadewa sai gashi da meenal, tanazuwa ta duka tanajiran Jim abinda zece, Kai tsaye yace kinyi karatune, daga Kai tayi tareda cewa nayi,

yace wani mataki  kika tsaya, tace degree ne,

awani bangare kikayi degreen, department of gynecology a Cairo,

masha Allah kinada shaawar aiki, saurin daga Kai tayi tace eh,

yazaro card dinsa yabata yace kiba abban ki wanann inyadawo he should give a call my digits are there, sake soka  hannu yayi cikin aljihu yazaro bandir din 500 yamika mata, kinkarba tayi saida yamata Jan ido sannan takarba tareda godia sosai,

Fitowa tayi ta nufi daki farinciki cike a fuskarta, wani malolon bakin ciki ya turnike faltama ta Taso da zafin nama ta fizgo meenal Wanda hakan yasa ta faduwa ta gwara Kai da bango............


Maleeka  ta kalle muhassin tace, so what action next did u think u should take cos am very scared a about maleeks situation, this two weeks fa Amma bawani chanji,

Sauke ajiyar zuciya muhassin yace wallahi sista am even confused,  Amma wait its as if I am trying to remember  something, Jim yayi yana tunani yace sister kinsan lI can remember muntaba maganar country din da meenal take lokacin da tanan Amma gaskiya bansan wacce but insha Allah I will try to remember,

To muhassi that is very good of you, Amman the problem here ix Idan munsan country ta Ina zamu fara namanta, kuma kaga baka taba zuwa can din ba,

Ehen sister I can remember country din fiancee Dina take Nigeria, she is a Nigerian

Wani sanyi maleeka taji har cikin Ranta tace first problem solve, yanzu plss try and remember d state yanda abin zezo mana da sauki..........




Mrs abvdool ce....

Continue Reading

You'll Also Like

17.9K 1K 111
Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zat...
9.5K 396 23
A story about Love,Hypcrisy, betrayal, sacrifice and sorrow, Is all about two kingdoms who are families but unknown to them,and they all wish one day...
547K 3.4K 6
A story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......
5.5K 200 36
Labari ne a kan wata mata da kishiyarta ta haukatar da ita da tsohon cikin ta tafi ta haife cikin a halin hauka