HIKMAH

By Shatuuu095

123K 13.7K 914

HIKMAH.... The limping lady More

1⃣
2⃣
3⃣
4⃣
5⃣
7⃣
9⃣
8⃣
🔟
1⃣1⃣
1⃣2⃣
1⃣3⃣
1⃣4⃣
1⃣5⃣
1⃣6⃣
1⃣7⃣
1⃣8⃣
1⃣9⃣
2⃣0⃣
2⃣1⃣
2⃣2⃣
2⃣3⃣
2⃣4⃣
2⃣5⃣
2⃣6⃣
2⃣7⃣
2⃣8⃣
2⃣9⃣
3⃣0⃣
3⃣1⃣
3⃣2⃣
3⃣3⃣
3⃣4⃣
3⃣5⃣
3⃣6⃣
3⃣7⃣
3⃣8⃣
3⃣9⃣
4⃣0⃣
4⃣1⃣
4⃣2⃣
4⃣3⃣
4⃣4⃣
4⃣5⃣
4⃣6⃣
4⃣7⃣
4⃣8⃣
4⃣9⃣
Finale

6⃣

2.5K 295 11
By Shatuuu095

_I've seen all your comments and votes on wattpad... It's always thank you. Nasan Hikma Ya tado tsohon ciwo, as I can see comments na mutane that went through the pain of infertility. I'm sorry Allah Yana tare daku, he'll ease all of your pains_

*The first six chapters of HIKMAH are dedicated to every infertile family... You will have your baby sooner or later Inshaaa Allah*

"Zamui referring dinku Teaching hospital na gwagwalada"

Doctor Ya fada lokacinda yazo duba babyn Hafsa, kallonshi Hafsa tayi tareda kallon babyn sannan tace

"Amma babanta yace kace zaayi discharging dinmu ne, Naga ta samu sauki referral na Meye Kuma?"

Kanshi Ya girgiza sannan yace

"Eh sallamarku Zamui amma Kinsan zaku dinga zuwa follow up ko? babanta yace dani a Abuja kuke, so is better Ku cigaba acan than ace zaku dawo nan"

Ajiyar zuciya Hafsa ta saki tayi Murmushi tana kallon halittar dake hannunta, da gaske bata taba kawo yarinyar zata murmure har Haka ba, kullum gani take yarinyar zata mutu kafin Washegari amma rai hannun Allah yake.

"Mun gode sosae, kuma Inshaaa Allah Zaa dinga zuwa follow up din"

Kanshi Ya gyada sannan yace

"Kinsan yarinyar preterm ce, akwai organs dinta da are not well developed, to akwai abu da ake kira kangaroo mother care KMC, shi Zaa dinga mata"

Cikin rashin fahimta Hafsa tace

" Bangane ba"

Tsayuwar shi ya gyara yace

"Kinsan kangaroo nada pouch jikinta Wanda take zura danta ko? "

Kai Hafsa ta kada, ya cigaba

"zaki cire rigarki, ki daura babyn bayan kin cire kayanta a kirjinki, ki daure da zani, dumin jikinki zai dinga regulating nata body temperature, sannan breastfeeding is also essential "

Kai ta gyada cikin fahimta, tayi mishi godiya sannan ya fita, yana fita Miss A'isha ta shigo Don hada kayan, Hafsa na zaune ita kuma Miss A'isha ta kammalla ganin Hafsa batada niyyar tashi yasa tace

"Tashi mu tafi mana, kina bata min lokaci yau nake son tafiya"

Dagowa Hafsa tayi tace

"Haba Mom, tafiya zakiyi ki Kara barina? "

Sakaka Miss A'isha ta kalleta sannan Tayi tsaki tareda karbar babyn ta rufeta cikin Farin shawl me baza red a jiki, ganin zata fita yasa Hafsa riko hannunta tace

"Mom me yasa kuke Haka keda Alhaji? Idanunku na nuna abinda kukeso amma kunki, Haba Mom rekindle your love mana.... "

Zancenta ya katse saboda shigowar Alhajin, kallon hafsan kawai yake Se kuma ya Kalli Miss A'isha kafin yace

"Hafsa haka kikeso? "

Da sauri ta gyada kanta batareda ta furta komai ba saboda wani irin excitement da ya lullube ta, kallonshi Miss A'isha tayi tace

"Ina fatan ba fada mata Kake zaka maida ni ba, Abbas ka manta nace Bazan kara komawa gidanka ba? "

Murmushi Alhaji Yayi yayinda jikin Hafsa ya Fara rawa yace

"Eh kin fada A'isha, amma inasan kisan ni dake we're match made in heaven, har yau shekaru ashirin da biyar kin kasa aure, kinga you're telling Abbas is only you I want. Badan ke zanyi ba sedan farin cikin Hafsa. "

Daga Haka ya fice, Miss A'isha ilahirin gabobinta Sunyi sanyi, Hakanan tayi Shiru Ta rasa me takeji, Hafsa ce ta dafa ta Murmushi saman fuskarta tace

"You should happy Mum! Alhamdulillah! "

Suna zuwa gida zance har ya bazu akan Alhajin sama zai maida Mum, masu farin ciki nayi, mahssada nayin nasu Wanda Dama su sukai sanadin wancan rabuwar. Masoyan Miss A'isha a familyn Sunyi murna, ga Murnar dawowar Hafsa gida. Washegari wajen hudu na rana aka maida auren Alhaji Abbas Maina da A'isha, zata huta a Nigeria na sati biu kafin ta koma California saboda aikinta duk Wanda ya samu Dama se yazo. Aminu murna Kamar me, Washegari suka juya Abuja.

Gidan an gyarashi Wanda hakan ya bawa Hafsa mamaki seda ta shigo taji Ihun little Maina yana

"Maa oyoyo, kince itace Matata ko? "

Kanta ta gyada wani kayataccen Murmushi na fitowa tace

"Babana wannan ita ce matarka gata nan "

Ta mika mishi ita, gaba daya shekarun yaron basufi goma ba, shi ne Babban Dan Salima kanwar Aminu, mijinta Nafi'u yayan Hafsa uba daya, Rana daya akai musu aure dukkansu.

Kallonta Maina Ya tsaya yi ganin tana wasa da hannunta a baki ga Idanunta sak na Hafsa Manya dasu, Murmushi yayi yace

"My Lulu Catty"

Shikenan Lulu ta bita Dama sunan Dada aka saka mata Baa fada kowa da abinda yake fada mata cikin dangi seda Maina yasaka mata Lulu shikenan kowa ke kiranta Haka. Duk Friday da an tashi a school driver ya sani gidan Hafsa yake kawo Maina anan zai yini Se dare kafin ya koma gidansu, Don Haka bayan iyayenta Hafsa da Aminu babu Wanda Lulu ta gane Kamar Maina.

Ranar asabar suka karbi bakuncin Habibu da Lubabatu, ranar Ansha hira Kamar me, Aminu Ya dinga musu tsiya akan yadda basu yawo da yaransu ,Habibu Ya tabe Baki yace

"Kuma doki kuke da zarar Kun Tara da yawa zaku daina wallahi, ta Ina zaka dinga yawo dasu."

Hafsa ce tace

"Amma basu taba ganin kanwarsu ba, at least da Kun taho dasu ai "

Lubabatu tayi dariya tace

"Da tuni sun hautsina ko ina, kada ku damu Hutu Zaa kawosu gaba daya"

Dariya Duka sukai sannan sukaci Abinci, bayan Maghrib aka kaisu airport suka koma Lagos bayan Lulu Tasha abin Arziki har seda Aminu Yayi fada Wanda yasa Lubabatu fadin

"Lallai Se Yanzun Kasan kudi akwai amfani, idan bamuyiwa gudan jininka ba se wa"

Godiya sukai musu suka rabu cikeda kewar junansu.

A kwana a tashi Har Lulu tayi wata bakwai, dukkan Wasu dokoki babu Wanda Hafsa ke tsallakewa, yarinyar tayi girma sosae Kamar ba bakwaini ba, ta murmure babu inda ta baro Hafsa Har skin color din, kyakyawa ce yarinyar, nan Hafsa tasa wata mata ta kawo mata Nanny Wanda da kyar Aminu Ya yarda don da farko cewa Yayi sede a Nemo professional daga wata kasar amma Hafsa tace

"Haba dai dear Dan bata kudi, nanma Allah zai kiyaye"

Nanny Batafi 18years ba Christian ce mazauna kauyikan Abuja, anan aka samo ta, sosae aka kafa mata dokoki kuma babu laifi yarinyar tana kokari sosae. Indai Hafsa na gida to Lulu na gurinta sede idan ta fita shi ne.

A kwana a tashi watanni suna ta tafiya, rayuwarsu gwanin dadi har shekara ta zagayo lokacin birthday din Lulu ta zagayo, ana saura sati daya Hafsa da Cynthia Nannyn Lulu suka tafi gidan Salima inda Zaa tsara grand birthday party.

"Kinsan baayi suna ba lokacin muna asibiti, so nake nayi kara'i da suna da komai. "

"kina shaanin Ki matar nan, tunda grand ne mu Fara plan Tun yanzu"

Take aka dakko paper da pen aka Fara tsarawa basu gama ba se dare tukunna Aminu yazo daukarsu, a Mota take cemishi

"Birthday din Lulu fa next week ranar asabar"

Cikin rashin kulawa yace

"Lulu ta girma"

Dariya Hafsa tayi tareda gyara zama tace.

"So Ina shirya mata grand birthday party"

"Birthday party kuma? Saboda me? "

Dan bata rai tayi tace

"Eh mana, ka manta baayi suna ba mutane nason su ganta, kaga party zai saka suzo Ko? "

Kanshi Ya girgiza yacr

"ki manta da wani birthday stuffs Kinji Hafcy na"

Shiru tayi Batace komai ba hakan yasa yace

"Yawwa my love! "

Nanma Batace komai ba hakan yasa ya yi tunanin ta hakura, ita kuwa karkashin ranta tana tunanin abinda zai Hana party dinnan abu me girma ne. Batareda sanin Aminu ba Hafsa ta cigaba da shiri Kamar yadda mutanen ta ke shiri abinsu, seda ranar Tazo Aminu Ya gama shirinsa tsaf sannan Hafsa tace

"Kayi hakuri for the first time kace na bar abu ban hakura ba, yau zanyiwa Lulu party"

Tsira mata idanunshi yayi yace

"Amma nace banaso right? "

"Ka fada but lokacin Har cake nayi order, babu abinda zai faru Inshaaa Allah "

Ta fada tareda bashi peck a kumatu, mayar mata da martani yayi sannan yace

"Its OK, ayi lafiya"

Rungumeshi tayi wannan yana Kara jika son Aminu a ranta, akwai sacrifice, Allah Ya barsu tare.

Karfe hudu gidan Ya cika mutane sosae abin harda mamaki, Lulu tayi kyau cikin kayan da aka saka mata dake Har lokacin bata zama se kafa da take, Tayi kyau ko ina Maina na gefenta, Haka akaci aka sha aka yanka cake, lokacin photo session Hafsa ta canza mata kaya zuwa wata riga silk ta ciki amma saman duk net ne color red Se karamin crown silver a wuyanta, hannunta tasa mata wata silver bracelet Wanda wani katako da aka lullube da takarda tayi Rubutu a jiki, duk na yadda suke sonta itada Aminu, yau birthday dinta how special ranar take garesu. Anyi hotuna sosae seda aka gama sannan ta bawa Cynthia akan taje ta canza mata kaya, nan gidan Ya Fara Bajewa daga kawayenta Se Salima, su suka taya ta gyaran gidan sannan suka tafi, nan ta samu tayi wanka sannan ta shirya abincin Aminu. Se wajen karfe Tara Aminu Ya shigo tana kallonshi taji wata muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta, Har seda ta bude Idanunta, da murmushin nan na kullum ta tarye shi seda yaci Abinci Yayi wanka sannan yace

"Ni Banji hayaniyar Lulu ba, ko tayi bacci"

Kai Hafsa ta girgiza tace

"Ta gaji na bawa Cynthia ta mata wanka har Yanzun basu fito ba, Nima gyaran gida ya dauken hankali, lemme check them"

Mikewa tayi ta nufi dakin amma kafin ta bude taji wani jiri nason dibarta, da sauri ta daidaita Tsayuwar ta sannan ta shiga, Idanunta ta runtse ganin babu kowa a dakin, kayan da ta bayar a sawa Lulu yana yashe a Kan gado, zuciyarta na harbawa ta isa bandaki nan ma babu kowa a ciki, Shiru Hafsa tayi gaba daya ta kasa tantance meke shirin faruwa,

"Cynthia! Cynthia!! Cynthia!!! "

Ta shiga kwala kira amma Shiru hakan yasa ta fito da sauri Tana zuwa sukai karo da Aminu Wanda yazo dubata jin yadda take kwallawa Cynthia kira

"Menene? "

"Ban gansu ba Aminu, basa nan"

Kallonta Yayi cikeda rashin fahimta yace

"Wa kenan? "

Se jikinta Ya fara rawa ganin irin kallon da Aminu ke mata, harshenta Yayi nauyi ta kasa magana Se Idanunta da ta kafe a kanshi, gefenta yabi yana jin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa ya leka dakin nan ma babu kowa hakan yasa ya dawo yace

"Hafsa kidding me right? Ina Yata? "

Ya fada da karfin da seda Hafsa taja baya, Binta yayi ya shake mata wuya............

Jakadiyar kainuwa

Continue Reading

You'll Also Like

112K 10.9K 62
Labari ne da ya k'unshi tsana, k'iyayyaya, mugunta, da uwa uba soyayya. Ku biyo ni kuji me zai faru a littafin //Zafin Rabo//
685K 120K 120
Title - It is not easy being a master Author - Jin Xi Gu Nian / Eng translator - Xi Xi Burmese translation period - Jan 5,2021 ~ Oct 14,2022 ရှန်ကျစ...
20.5K 1.6K 52
Ƙwarangwal ɗin suna tafe wani irin ruwa mai yauƙi na fita daga gaɓɓan jikinsu tamkar waɗanda aka kunna fanfo ajikinsu, daga kowanne ɓangaren hallita...
14.4K 2.2K 31
Labarin d'an bature labarine dayazo muku da sabon salon rubutu, wanda ze nishad'antar fad'akar yakuma wa'azantar, labarine akan yarinya yar mulki me...