HIKMAH

By Shatuuu095

124K 13.7K 914

HIKMAH.... The limping lady More

1⃣
3⃣
4⃣
5⃣
6⃣
7⃣
9⃣
8⃣
🔟
1⃣1⃣
1⃣2⃣
1⃣3⃣
1⃣4⃣
1⃣5⃣
1⃣6⃣
1⃣7⃣
1⃣8⃣
1⃣9⃣
2⃣0⃣
2⃣1⃣
2⃣2⃣
2⃣3⃣
2⃣4⃣
2⃣5⃣
2⃣6⃣
2⃣7⃣
2⃣8⃣
2⃣9⃣
3⃣0⃣
3⃣1⃣
3⃣2⃣
3⃣3⃣
3⃣4⃣
3⃣5⃣
3⃣6⃣
3⃣7⃣
3⃣8⃣
3⃣9⃣
4⃣0⃣
4⃣1⃣
4⃣2⃣
4⃣3⃣
4⃣4⃣
4⃣5⃣
4⃣6⃣
4⃣7⃣
4⃣8⃣
4⃣9⃣
Finale

2⃣

3.2K 321 7
By Shatuuu095

                      💕HIKMAH💕
                               2⃣

✍️SHATUUU♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

💖Shatuuu095@wattpad

Kwanan su Aminu da Hafsa biyu cikin Garin na Germany, babu inda suke zuwa banda daki, shi ne ma Ya fita Nemo musu sabon SIM saboda suyi communicating da gida, yana siyowa ya dawo inda suka cigaba da kashe junansu da soyayya, they're very romantic couples Wanda da ace hakan shi ke kawo haihuwa bana tunanin zasui shekara bakwai da aure ba tareda sun haihu ba, amma Allah shi ne Allah! Shi yake tsara mana yadda rayuwarmu zata kasance shiyasa ya jarabce su da hakan.

Alarm din dake gefen gadon nasu ne ya Fara bugawa saboda setting dinshi da akai Ya buga a kowacce sallah don idan zasu biyewa timing lallai bazasu yi sallah ba. Hafsa ce ta Fara yunkurawa ta mike tareda fadawa toilet Don daura alwala, seda ta kammalla sannan Aminu Ya shiga yana fitowa Ya jasu sukai sallah sannan suka koma.

Karfe takwas suka kammalla duk wani shirinsu don wannan ce ranar appointment dinsu da Doctor da zai musu aiki. Seda sukaci Abinci kafin suka biyo lift suka sauka kasa, Asibitin baifi 10 meters bane daga hotel din, hakan yasa suka wuce da kafarsu suna ta hira wadda duk yawanci Aminu keyi akan Babynsu ita kuma tana dariya don duk yadda take zumudin babyn Aminu yace bani guri don kullum zancen yake.

Cikin nutsuwa Baturen doctor Ya gama duba file dinsu, lokacin ya dago idanunshi Ya sauke Kan Hafsa da Aminu da suka tsira mishi ido, cikin turanci dinsu Ya Fara musu bayanin yadda procedure yake

"It's my pleasure having you here, na duba file dinku bayan test da kukai running Ya nuna mana male partner yanada low sperm count, while female partner lafiya take, gashi Kunyi signing Kun yadda da aikin Ko? "

Aminu Ya dubi Hafsa sannan yace

"Yes! Mun yadda amma baayi briefing dinmu yadda procedure din take ba, chances na nasara, failure da adverse effects dinta"

Kai Doctor din Ya gyada tareda sake gyara zama yace

"Intrauterine Artificial Insemination, procedure ce da ake yi don addressing Infertility, Yanzun Zaa duba lokacinda ya dace ayi aikin, lokacinda mahaifar ki zata fi karbar ciki, zaka bamu Sperm sample dinka Wanda Zaa saka a mahaifar ta, akwai chances me karfi na nasara, side effects very few ne, kuma ido biyu akeyi"

Wata sassanyan Ajiyar zuciya Hafsa ta saki Don duk tunaninta yanka ta zaayi ayi aikin, hannun Aminu ta sake damkewa cikin nata hakan yasa ya gyada mata Kai alamun karfin gwiwa, basu fito daga office din Doctor ba seda sukai clearing dukkan doubts dinsu kafin akaje inda Hafsa ta kara running Wasu test, kwanaki goma Ya basu da magunguna na Fertility suka koma masaukinsu.

Bayan Sallar ishai suka fita waje Don shan coffee Dan dukkansu biyu addict ne, da wuya kaga daya na son Abu daya baya so, perfect couples ne Wanda suka fahimci kansu sosae, a zamansu Hafsa zata iya irga sau nawa sukai fada, dukkansu free minds ne dasu shiyasa ko sun samu matsala there and then kowa zai fadi abinda ke ranshi. Matsalarsu daya wannan rashin haihuwar itama sune suka damu don kuwa kullum suka shiga dangi kasamcewarsu dangi daya yasa duk inda suka shiga Baki ake basu kada su damu haihuwa lokaci ne. Shekarar da ta gabata Baban Aminu Yayi suggesting suje Germany tunda anan an rasa daga Ina matsalar take, suna zuwa akai komai anan aka gano daga Aminu take, nan hankalinshi Yayi masifar tashi dukda Hafsa na nuna mishi itafa matsawar zata zauna dashi to haihuwa ba komai bace, bayan sun dawo Baban Aminu yace lallai Se an raba auren Dan kada a cuci Hafsa, Anga Tashin hankali marar misaltuwa kada ma Hafsa taji labari. Wannan yasa Baban Hafsa matsayinshi na Babba yace a kyalesu tunda sunji sun gani sun amince. Haka rayuwar ta cigaba har Aminu yace suje suyi Insemination dinnan, babu Wanda suka shawarta Haka suka taho abinsu saboda sunsan family dinsu babu Wanda zai yadda da hakan. Hakan yasa sukai yin kansu saboda suna ganin shi ne kadai mafita a tare dasu.

"Idan na haihu wa Kake ganin zaka fi so? Ni ko babyn? "

Hannunta ya riko yana kallonta cikin ido, da nashi idanun masu saka zuciyarta narkewa yace

"Ke mana! Babyn ai Bakuwa ce"

Murmushi tayi tareda bashi peck tace

"I love you man!"

"I love you wife"

Suka karasa shan coffee se suka koma ciki Don bacci, Suna shiga dakinsu Hafsa ta shiga tayi wanka da dukkan abinda ta saba kafin kwanciya sannan ta fito, shima wankan ya shiga, fitowarshi Har ta shirya Tana Dan gyara dakin. Seda ya shirya kafin ya bude system dinshi, Tana ganin Haka ta wuce gado don tasan aiki Zaiyi, shi din kuwa Yayi, ya jima yanayi kafin ya kashe system din Ya dawo gefenta ya kwanta batareda Yayi abinda zai tasheta ba. Sede kallonta kawai Da yake yana jin yadda zuciyarshi ke kara budewa sonta na shiga, hannunshi yasa ya shafa bakaken lashes din Idonta da suke a mike ya taba, Kana kallon Hafsa Kasan a yarenta akwai tambaya, Tashin farko mutum bai isa Ya sata a category wani race group din ba, saboda an samu hadakar yare aka haifar da ita, hakan yasa bazaka taba cewa itada Aminu cousins suke ba saboda kammanin kowa daban. Maman Hafsa black American ce wadda ta musulunta dalilin kawarta iyayenta suka Kore ta, Baban Hafsa Wanda usulin barebari ne na maiduguri yaje Karatu Ya dawo da aurenta, bayan anan ya bar uwargidanshi da Yaya uku, hakan yasa Hafsa yin Baki tunda gaba daya iyayenta bakake ne kada ma Babanta yaji labari, Aminu mahaifiyarshi bafullatanar Adamawa ce, a gidansu zakaga mixture wannan fari wannan Baki, anan Aminu Ya samo kammanin da yake dashi.

Hannunshi yakai bakinta hakan yasa tayi juyi tareda ture hannun nashi, Murmushi yayi don se ta tashi hakan ya kudurce, a hankali ya dinga yawo da hannayenshi duk sensitive part dinta babu shiri ta Mike zaune Tana turo bakinta, Idanunta Sunyi jawur saboda bacci tace

"Haba Dear! Bakaga bacci nakeji ba?"

Ko kulata baiyi ba ya hade bakinsu guri daya, itama tasan halin mijinta dole Haka ta hakura da baccin don aure sacrifice ne, you can sacrifice anything for your partner.

Rana bata karya sede Uwar Diya taji kunya, wannan Haka yake Don kuwa ranar da aka sawa Aminu da Hafsa yin dashen ciki Tazo, Daren basuyi bacci ba banda addua da suke akan Allah Ya tabbatar musu da cikin, yasa ayi a saa sede babu Wanda Ya roki alkhairin abin, idanunsu Ya rufe, cikin kadai suke so kowanne iri ne kuwa. Tirkashi!

Suna kammalla Sallar Asuba sukai wanka sannan Yayi musu order Abinci amma Hafsa tea kadai ta iya sha, shi ne ma yadan taba French fries din. Kallon agogo Yayi yaga sunada wajen 3hours ya rage hakan yasa ya dakko system dinshi Don duba mails dinsa, Se da yayi Dana sanin hakan Dan kuwa Email din Baban Hafsa dashi ya Fara cin Karo, yana dubawa Ya zare glasses din idanunshi jikinshi har wani rawa yake Ya Kara kallon sakon yasan tabbas zai aikata abinda ya fada, da sauri Yayi slamming system din tareda runtse idonshi a take kuma wani Tsoro ya kara Kamashi, yasan waye Alhaji yasan abinda zai iya.

"Dear! Menene Naga mood dinka Ya canja all of a sudden? "

Hafsa ta fada tana dafa goshinshi, idanunshi da suka riga sukai ja Ya bude tareda riko hannunta yana kirkirar Murmushi yace

"Bansan yadda zata kasance ba, I'm nervous! "

Zama tayi gefenshi tareda daura kanta a kirjinshi tace

"Please don't be! Let's all have fate! "

Kanshi Ya gyada alamun Ya gamsu amma a Kasan ransa Tsoro ne fal ciki. Sun jima tana bashi Baki Har lokacin Yayi suka wuce asibiti, babu bata lokaci akai implantation aka gama, seda aka bata Hutu ta huta kafin aka sallamesu suka dawo gida.

"Hafcy, Kinzo da visa dinki ta America? "

Hafsa dake kwance tayi saurin dago da kanta tace

"Me zaayi da ita? "

Zama yayi gefenta yace

"America zaki tafi.... "

Da sauri Ta tashi zaune tace

"Dalili? Nace inason Naga Mum ne? "

Girgiza Kai Aminu Yayi, jikinshi a sanyaye yace

"Hafcy, Ki saurareni and please reason with me, dazun Naga email din Alhajin sama( Baban Hafsa) Yayi min, I dunno Wanda Ya fada mishi munzo Germany a Dasa miki ciki, yace Ko Anyi Se ya zubar da cikin... "

Hawaye sosae Ya Fara yiwa Hafsa zarya a kumatu, Meye kuma ya taso Haka? Hannunta Aminu Ya kama yace

"Hafcy go to California gurin Mum, itada Dada kadai zasu iya kula mana da cikin jikinki, Dada is stuck a cikinsu babu abinda zata iya amma Mum can do it, idan na gama handling dinsu Seki dawo mu reni cikin"

Kai Hafsa ta girgiza Tana kuka shabe shabe tace

"Ba Haka mukai dakai ba, lokacinda mukai aure Munyi alkawarin fuskantar kowanne kalubale tare, ni da Kai da abinda aka dasa min Yau we're a team, tare Zamui komai, Zan bika Nigeria tare muyi facing Komai tare! "

Kanshi Ya girgiza sanin halin Hafsa akan kafiya da naci, yasan zaayi Haka amma yasan Alhaji tunda ya furta zai iya abinda yafi zubar da cikin kowa yasan tsaurin shi, hakan yasa suka boye Mai asalin zuwansu Germany.

"Hafsa! Kinsan abinda Alhaji zai iya right? Zubar da cikinnan kalilan daga abubuwan Alhaji zai iya yi ne, kije kawai saboda mu samu muyi protecting abinda muke nema ido rufe, na miki alkawarin da zarar Ya lafa, I'll come for you"

Ita yar Alhaji ce tasan abinda zai iya da Wanda bazai iya ba, mutum ne me tsaurin gaske, Tana kallo Mum ta koma California amma mirsisi ya hanata bin Mamanta sede duk December taje ta dawo, seda Tasha kukanta Dan ta Fara hango masifar dake kokarin binsu tunda Alhaji ya samu labari, a hankali muryar ta na rawa tace da Aminu

"Kayi booking next flight zan tafi"

Rungumeta Yayi yace

"I love you Hafcy "

Kafin ya saketa Yayi waje, a gurin ta durkushe Tana kuka Har seda kanta ya Fara ciwo kafin ta tashi ta tattara kayanta, ta hada mishi nashi, ta dade Tana jin Inama ba Alhaji Ya haifeta ba, a tsaurinshi yake shiga hakkin mutanen dake tareda shi, shiyasa kullum Mum dinta na cewa

"Hafsa da Abbas an halliceshi zamanin Annabi Musa bana tunanin he'll believe in him, saboda kafiya da naci irin nashi"

Wanda duk Yayansa Hafsa din ce ta gado wannan shima bawai sosae ba. Karfe Tara na dare jirginsu Hafsa ya tashi zuwa America, Ko mum bata fadawa ba don itama bata hayyacinta, tunda ta suka tashi cikinta ke hautsinawa ga zazzabi da ya rufe ta, Wanda tasan side effects din implantation dinne, hakan yasa tayi lum a kujera tareda rufe idonta sede Ko awa biyu bata cika ba, ta Fara amai Wanda Ya jawo hankalin hostess din nan aka Fara bata taimakon gaggawa!

What's coming?

Yours Truly

Shatuuu ♥️

Continue Reading

You'll Also Like

270K 42.6K 122
Our S.C.I leader Mouse Xiao Bai and Cute Psychologist Cat Zhan Zhao's love story
37.7K 3.6K 94
An Interesting Love story
62.3K 10.6K 66
A story of Safiyya and Usman
696K 120K 120
Title - It is not easy being a master Author - Jin Xi Gu Nian / Eng translator - Xi Xi Burmese translation period - Jan 5,2021 ~ Oct 14,2022 ရှန်ကျစ...