ILLAR MARAICI

By Bookaholicnutella

2.8K 275 80

Ta kasance sanyin idaniyar iyyayenta. Sanadin farincikinsu, dalillin jin dadinsu kuma 'ya kwalli daya ga atta... More

Jannah
Rahma
'Da na kowa ne
Me laifinta
Dangin Miji
Nigeria
Alkawari
Al'ajabi
Rashin Uba
Sabon littafi
Rabon Gado
Sabon Al'amari
Me Ke Faruwa
Rashin Gata
Sauyi
Zynat
Tashin Hankali
Takaici
Makirci
Sulaimi
Mugu Bai Da Kama

Ramadan

175 15 3
By Bookaholicnutella

Sumayya da ta kasa bacci tsananin tashin hankali ta mike daga kan gado. Cikin sauri ta yi wanka had'e da shiryawa cikin doguwar riga. Taje kanta tayi kafin ta nufi kan gado domin tasin Ahmad. "Al'ameen wake up" ta fa'da yayin da take ta'ba shi. Murmushi ya sakar mata had'e da mikewa. "Good morning beautiful wife" "Morning husband ka tashi kar mu makara kaji?" Shiru yayi kafin ya mike. Ko k'ad'an baya son tafiyar nan.

Jiki a sanyaye Sumayya ta mike zuwa d'akin Rahma. "Daughter tashi ki ki shirya" Juyawa Rahma tayi had'e da buga kafada. "Umm umm" "C'mon Mercy tashi kinji?" "Aunty ba school fa please let me sleep" "Kin manta yau zamuje Nigeria?" Ai kua da sauri ta mike. "Hasbunallah Allah na manta". Cikin sauri ta nufi bathroom gudun sa su letti.

"Angel!" Sumayya ta kira Jannah. "Umm umm Mommy please" ta sake cusa kanta cikin pillow. "Ke umm umm Rahma umm umm ya zanyi da kune?" Shiru Jannah tayi kamar bata ji ta ba. "Wake up Baby kin ji?" "Mommy five minutes" da k'yar Sumayya ta samu ta lallaba Jannah ta tashi.

Ai kua tana ji Nigeria za su je ta saje komawa kan gado. "Jannah me haka? weren't you the one insisting?" "Not anymore Mother dearest I'm out because i can't stand Granny". "K'aryanki kuma ai'' da haka ta d' aga ta cak." Mommy put me down!!! "" You wish baby" har sai data sa ta a k'arkashin shower kafin ta fito tana cewa. "Fifteen minutes Jannah".

Kitchen ta wuce a nan ta sami Rahma dauke da bowl na Poutine da plate na Jacket Potato. Ita har yanxu mamaki suke bata. Ta rasa me suke so a cikin Poutine ko Jacket Potato gani tayi duka ai dankali ne.

"Sannu daughter" Murmushi Rahma tayi kafin ta tayata k'arasa BeaverTails da lobster rolls data fara. Cikin two hours suka gama girka komai hade da jerawa bisa dining. Kamar ance suje parlour ai kua samun Jannah suka yi tana faman fad'a da Umma.

"Wai Granny me hakane? Idan haka zamu cigaba da zama Allah I'm not coming ai I'm not obliged to" "Toh sannu Firdausi ko me ma uwar taki taje kiranki dole sai kinzo ko kina so ko ba kya so" "Toh amma ai I'm not obliged to cook any kuka thing. Wait mema kikace Miyir kuk..ku.." "Dalla matsa miyar Kuka ake cewa" "Subhanallah you mean kuka na crying ko? Please dont tell me da hawaye ake yi. Yuck! K'azanta sai 'yan Nigeria."

"Ke dan abu kaza kazanki har kin isa ki zagi Nigeria? Abincin mu befi jagwalgwalonku na iraq da na turawanku ba?" "Allah befi ba" Jannah ta b' ata rai. "In kinga dama ki fashe amma nidai yau bazanci kayan aman naku ba. Wa yasan ma ko alade kuke dafawa mutane". Dariya Jannah ta tayi har da rike ciki.

"Granny what is Aledede?" Harara Umma ta watsa mata "Wawiya Alade ake cewa not Aladede" "Whatever ni dai tell me. Please.." "Mtcheewww Alade shine pig kuma naman shi ba shine pork da kuke ci ba?" "Ohhh that dirty thing? Amma ai yafi 'yan Nigeria tidiness saboda baya cin hawaye" Jannah ta fad'a fuska dauke da murmushi. "' Ya dai fi Uwarki wawiya kawai" da gudu Jannah ta mike ganin Umma na kokarin Jefa mata pillow.

"Ni dai I'm not wayiya" "Jaka wawiya ake cewa not wayiya" "Whatever I'm not a bag I'm a human... Ouchh!!" sai kuma ta saki ihu sakamakon karo da sukayi da uncle Abdul. "Jannatul Firdaus..!" "Sorry Uncle" "it's okay"

Daidai lokacin Ummul Khair ta shigo tare da 'ya' yanta Zara me shekaru fourteen da Mufida me shekaru seventeen kasancewar manya biyun Hamza da Usman sunyi aure. Zarace ta fara k'arasawa wajen Jannah. "Hey Jannah you look good" ta fada tana k'arewa abayan da tasa kallo "You too sister" nan suka gaisa da mul Khair da Mufida.

"I heard some commotion downstairs d'azu da nake shiryawa" Ummul Khair ta fad'a tana kallon Jannah. Hararan Umma Jannah tayi ganin bata kallon ta. "Ni kike harara?" suka jiyo muryar Umma.

"Mtcheewww" Jannah tayi tsaki k'asak'asa. "I didn't hararara you old woman". "Kin ga irin rashin kunyar da uwarta ta d'orata a kai ba?" Umma take fad'a wa Ummul Khair bayan sun gaisa.

"Ummul Khair mom did no such thing! She was just comparing a soup made from tears and our delicious iraqi food". K'asaitaccen murmushi Ummul Khair ta saki "I don't get you Jannah" "Miyar ku.. Kokuwa... No ku.. Ku" cak ta tsaya ganin ta k'asa tuna sunan.

"You mean Miyar kuka?" Ummul Khair ta tambaya. "Yes Ummu. She's comparing that thing with iraqi and Canadian dishes". Murmushi Ummul Khair ta sake yi sannan ta zaunar da ita. "First Miyar Kuka ake kira not kokuwa. Some call it Luru soup. It is made from Baobab not tears kinji?" nan Ummu ta ciro wayarta ta nuna mata hoton.

"It looks like Spilt pear soup sae dae it's darker" Jannah ta furta idonta akan wayar. Sumayya bushewa tayi ta k'asa koda motsi saboda wani kunya da tak'aici da ya cikata. Ita kam ya zatayi da Jannah. Shigowa tayi Rahma na biye da ita suka gaishe da Umma data amsa sama sama. Nan suka fara hira da Hajiya Sadiya wato Ummul Khair matar Ya Majid.

"Ni kam ina Hafsa ne?" Umma ta tambaya. "Bata tashi bafa" cewar Ummul Khair. "Ke Zara je ki tasota" Umma ta fad'a tana kallon Zara. "Kai Umma yanxu fa zata fara zagina idanna tasheta."

Kowa yasan Hafsat da wannan dabi'a na zagin wanda ya tasheta. "Ke! Rahama kike ko waye? Je ki taso Hafsat". "Toh" Rahma ta gyad'a kai zata mike Ummul Khair tayi saurin cewa. "A'a Umma Mufida zata je" Tabbass idan har Rahma taje zata dawo tana kuka. "Ummu bank'i zuwa ba amma k'in san Aunty Hafsat na iya zagina ko kuma tayi gigin tab'ani"

"Jannah come let's go get your Aunt". Sumayya ta fad'a tana tashi. "Babu wata Jannah da zata rakaki go by yourself naga ai babu wanda ta rakoki lokacin da zaki mallake min d'a a sunnan aure dan haka ke kadan ki zakije" gyad'a kai Sumayya tayi kafin ta mike Uncle Abdul yayi saurin cewa. "Ki zauna Aunty ni zan kirata". "A'a Abdul kai namijine be dace ba I'll go".

Ummu ta so rakata amma Umma ta hana. Jannah na ganin haka ta mike tabi mahaifiyarta. "Ke Firdausi dawo nan" Banza tayi da Umma kamar ba da ita take ba.

Bayan minti biyu Sumayya ta sauko tana kokarin rike hawayenta. "Tana zuwa" ta sanar dasu sannan tayi saurin ficewa daga wajen. "Allah Granny you should warn Aunt Hafsat, she wouldn't be the happiest with my presence idan har bata fita daga rayuwar Mommy ba" Babu wanda yayi expecting haka daga Jannah amma ko ma me ai Hafsat ce ta jawo.

Ko da suke cin abinci a dining Jannah batayi magana ba. Tanaji Hafsat ta sauko tare da Asiya da Sulaimi dama Ashir da Abbas already sun fara cin abinci. Ko da gwada mata magana shareta tayi ba tare da ta damu ko Ya Umar yana gani ba. "Ke me kuma wannan?" Umma ta nuna tashreeb da Sumayya take ci.

Sam ta kasa cin sauran abubuwan dan gani take sun yi nauyi a ci da safe kawai tayine dan sanin umma na son abinci me d'an nauyi shi yasa tun zuwansu bata iya cin abinci me kyau da zaran tayi abin breakfast cewa take yayi light da yawa. Ko kuma ta ce abin be mata ba ko yayi abin kyama ko kuma bazata iya ci ba.

"Umma abinci ne" "kin ji nace kashine?" Jannah da ke cin abinci makewa tati tabar wajen dama Rahma tun d'azu wasa kawai take yi da abincin saboda Aunty Hafsat dake gefenta da kuma Ashir dake ta faman taka mata kafa. A hankali ta zame ta bar wajen.

Awansu biyu da gama breakfast suka wuce airport. Ahmad da Sumayya na tafiya daga baya Umma ta kirawo shi. Juyawa Sumayya tayi ta kalli Rahma da Jannah da basu saka niqabinsu ba.

"Where are your niqabs?" "They are with me muna saurin fitane bamu samu mun saka ba" Rahma ta fad'a tana ciro nata.

"Quickly put it on...", sai kuma ta carke sakamakon abin da ta gani. "Akhi!!!..." ta tsala ihu a guje ta fara gudu tana shiga cikin mutane. Jannah na ganini haka ta fara binta da gudu hannunta na rik'e da niqabin. Ahmad ma da gudu ya biyota. Rik'eta yayi amma sai fusge fusge take ta tana kuka tana cewa

"Akhi... Please don't go... Akhi don't leave your Summy" ganin bara ta dena gudun ba yasa Ahmad rik'o hanunta tare suka kutsa cikin mutane. Jannah sai sauri take tana binsu a baya gudun karsu bata mata.

Tana cikin gudu tayi karo da mutum "ouch!! Are you blind?" Ta fad'a yayin da ta tsugunna daukan niqabinta ko damuwa da kallon mutumin bata yi ba. Juyawa yayi ko Allah zai sa yaga matar da yake bi sai dai kash! Tari ga da ta b'ace masa. Cikin b'acin rai da zafin nama mutumin ya finciko yarinyar da ko kirjinshi bata wuce ba.

"The hell?" Jannah ta yi kara. Hannu yasa dan gyara mata mayafinta da iska ke faman hurawa so yake ya mata magana yana kallon fuskanta dan rashin hankalintan yayi yawa. Sai dai mutuwan tsaye yayi ganin yarinyar dake gabanshi ba kowa bace illa younger version na matar da yake bi.

Sake juyawa gefe yayi ko dai matar d'azun ce? Toh amma wancan kuka take yi kuma da gani tare da mijinta take. Kan shine ya sake dorewa ganin kamarsu daya da mahaifinshi wanda wasu suke dauka yayanshi ne tsananin kama da suke yi kamar an tsaga kara. Cikin fushi da b'acin rai Jannah ta fara magana

"Let go..." cak ta tsaya tare da tsala ihu "who... are.... you?" kasa amsata yayi ya tsaya yana ganin ikon Allah. Hannu Jannah ta kai fuskrshi tare da tab'a fuskarshi. "You look like me.. Just like Mommy are you a ghost.?"

sai kuma ta tsaya da ta tuna da mahaifiyarta. "Leave me." Kin sake ta yayi sai ma kallonta da yake yi. Komanta irin nashi ido, hanci, baki... "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un please lat me go Mommy" sai kuma ta fara hawaye.

"Ramadan?" Dafa kafadanshi akayi wanda yayi dai dai da zuwan Rahma. Juyawa yayi tare da cewa "Ya Meenah look at her.." kafin ya karasa yaga wata me niqabi ta janyeta tana cewa "Jennah what's wrong me haka?". "Me zan gani Ramadan?" ya jiyo muryar Ya Meenah. "Forget it" ya k'ada kai.

"Jannah?!" Ramadan ya sake maimaita sunan a ranshi.

Continue Reading

You'll Also Like

104K 230 17
My wlw thoughts Men DNI 🚫 If you don't like these stories just block don't report
243K 12.2K 92
Being flat broke is hard. To overcome these hardships sometimes take extreme measures, such as choosing to become a manager for the worst team in Blu...
43.1K 1.5K 45
She had always feared the night, but everything changed when someone showed her its beauty. The calming moonlight and soothing night sounds transform...
37.5K 813 14
Jake, Sunoo and Jungwon went to a bar they had never been to before, And while they were there in that bar, they didn't know that there were four men...