ILLAR MARAICI

By Bookaholicnutella

2.8K 275 80

Ta kasance sanyin idaniyar iyyayenta. Sanadin farincikinsu, dalillin jin dadinsu kuma 'ya kwalli daya ga atta... More

Jannah
Rahma
'Da na kowa ne
Me laifinta
Ramadan
Nigeria
Alkawari
Al'ajabi
Rashin Uba
Sabon littafi
Rabon Gado
Sabon Al'amari
Me Ke Faruwa
Rashin Gata
Sauyi
Zynat
Tashin Hankali
Takaici
Makirci
Sulaimi
Mugu Bai Da Kama

Dangin Miji

156 12 3
By Bookaholicnutella

"Al'ameen kana ganin babu matsala? I don't like the idea of them coming kuma su tarar da su Jannah basa gida" Sumayya ta fada tana kaiwa da kawowa.

"Relax Sumy ki dena daga hankalinki ae ba yawo taje ba makaranta fa taje that too with Rahma" Ahmad ya fada yana kokarin kwantar mata da hankali.

"Ni ba shine damuwa na ba remember the other time da suka zo nan da zamuje Saudi? Kaima kaga ransu baiso ganin yaran nan cikin kanan kaya ba duk da cewa decent abu suka saka". Sumayya ta zauna akan kujera hankali tashe.

Yaya zata fara fuskantar 'yan uwan mijinta da suke nuna mata tsana karara? Ita ba ma shine damuwanta ba idan suka iso kafin su Jannah su dawo daga school to tabbas za'a samu matsala kasancewar riga da dawando suka saka sai jacket da yake dai dai guiwa hade da gele da sukayi rolling.

"Wallahi sai yanzu nake da na sanin rashin dinka musu natives" Sumayya ta fashe da kuka.

Zama Ahmad yayi a gefenta yana dafa kai. Ba abin da yafi daga mishi hankali kamar kukan matarshi ko 'yayanshi barin ma yau da 'yan uwanshi zasu zo all the way from Nigeria. Bai ga laifin Sumayya da take kuka ba saboda su a kullum basa rasa laifinta tunda dama ba sonta suke yi ba.

"Sumayya so kike ki daga min hankali? Dan Allah ki dena kuka I know it's not easy amma Allah baya daura wa bawansa abin da yafi karfinsa" Baba ya share mata hawaye yayin da yake rike da hanunta

"Hakane Al'amin amma bani da yanda na iya". A hankali Sumayya ta fada tana kallon kasa.

"Says who?" Baba ya tambaya yana murmushi, ido ya zuba mata yana kallonta hankali a kwance.

"Huh?" Sumayya ta sake baki tana kallonsa, ganin tana kallonshi ne yasa ya daga mata gira.

"Ki dena Sumy mesa kike kallona haka? Nayi miki kama da wani ne?" Ahmad ya karasa maganan yana fixing collars enshi kamar yanda samari suke yi.

"Really Al'ameen?" Sumayyah ta fashe da dariya, har da rike cikinta.

"Ko kefa Sumy? At least grace me with your smile. Yanzu tashi musan abin yi." Baba ya mika mata hannu.

"Toh ae Al'amin basu da dresses ko gowns. Na kyautar da duka last month dan kwatakwata sun nuna basa so"

"Ba matsala we can shop online" a cewar Baba da ya dauko macbook dinshi.

"A'a baba ni nafiso muje Arabian mall dake kusa da gida kaga wancan fifteen minutes drive ne kawai"

"As you say wife"

Misalin 2:45pm suka dawo daga mall. Zama Sumayya tayi a dakin Rahma sai data jera mata duka a closet kafin ta shiga dakin Jannah bayan ta gama arranging stuffs din tayi wanka ta canza zuwa wani grey vintage gown.

Saukowa tayi ta kara duba komai gudun a samu matsala.

Turaren wuta,

Abinci,

Towels,

Toothbrushes,

Toothpaste,

Toiletries,

"Phew Allah please help". Rufe bakinta ke da wuya wayan Al'ameen ta fara ringing.

"Assalamu alaikum" Al'amin yayi picking call din had'e da sallama

"Eh na turashi tun dazu but I'll be on my way"

"I'm sorry gani nan zuwa" da haka ya yankar da kiran, juyawa yayi yana kallonta.

"Allah yasa lafiya" fadan Sumayya kenan. Ganin yayi shiru bai ce komai ba.

"Lafiya Ya Majid ne ya kirani wai sun yi landing. Sumayya come let's go". Ahmad ya karasa yana kokarin jan hannunta.

"A'a Al'amin kaje kawai I'll take care of something here" ta girgiza kai, dan har ga Allah tsoron zuwa take yi.

"Kin tabbata?" Ahmad ya saje6 tambaya sanin cewa tsoron fuskantar su take yi.

"Eh Baban Jannah, you should leave now. Fi amanillah". Ta juya ta shiga ciki, ganin haka shi ma ya kama gabanshi.

Wani peach vintage gown ta dauko hade da brown mayafi. Kara saka turaren wuta tayi sanan ta duba komai intact. Ita damunwanta a yanzu shine su Jannah dake school. Har yanxu da sauran awa biyu kafin su dawo.

Saukowanta keda wuya taji doorbell na ringing. Cikin sauri da tashin hankali ta bude.

"Sister-inlaw!!.." Ko gaishesu batayi ba taji an rungume ta. Ko a mafarki tasan ba kowa bane illa Ummul Khair, matar Ya Majid.

"Welcome Aunty" Sumayya ta murmusa had'e da gaisheta.

'Daya bayan' daya tabi su da gaisuwa. Daga masu amsawa sai masu hararanta har mada wadanda basu amsa. "Umma ga wajen zama" ta fada cikin gu6ataccen hausarta.

"Jimin 'yar mutane, ni da gidan 'dana amma ke kike bani wajen zama? Lalle Sumayya wuyarki ta isa yanka" Nan jikin Sumayya yayi sanyi. "Kiyi hak' uri Umma" "yi min shiru munafuka" haka tayi ta zuba har sai da k'arfinta ya k'are. Da zaran Ahmad ya bude baki sai ta fake da cewa ya fifita matarsa sama da uwarsa.

Sallamarsu Jannah ce tasa su maida hankali kofa. "Mommy we are home!!!..." Jannah ta shigo tana gudu, Rahma na biye da ita. "Slow down baby sis" Rahma ta fad'a yayin da take binta. Hakan ta kasance musu 'dabi' a. Jannah zata shigo tana ihu Rahma na biye ta ita har sai sun k'arasa ciki amma yau kam mutuwan tsaye sukayi ganin gaba daya palourn na cike da mutanen Nigeria.

"Karaso mana" Muryar Umma suka jiyo. Cikin sanyi Jannah ta k'arasa Rahma kuwa kasa motsi tayi sanin me zai biyo baya. "Ke bara ki shiga ba ne? Ko kuma shima salon munafurcinne?" Umma ta cigaba da masifa kasancewa bata son Rahma ko kadan.

"A'a Umma kiyi hak'uri" ta karasa a durk'ushe. Ganin Rahma ta durk'usa yasa Jannah durkusawa. "Ni ba Ummar ki bace munafuka" shiru Rahma tayi kafin ta sake cewa "Allah ya huci zuciyarki Kaka". "What does that mean?" Jannah ta tambaya ita ko kodan bata san me suke fada ba.

"Toh ke kuma Uwar taki daura ki tayi kan 'dabi' un yahudawa?" Umma ta fada tana hararan Sumayya. "No namesake I'm not Yahudawa... Aren't they Jews? Ni musulma ce" Jannah ta karasa rai bace. "Yo ashe uwar taki tana da sauran hankali".

"Wai Granny me ya kawoki ne. And why are you just insulting mom and big sis? Father never does that". "Yo ke dan kaza kazan ki har kina da bakin gaya min haka? Ke a tsawon shakarunki goma sha biyu..." "Ni I'm not sha biyu I'm goma da uku. I repeat, I'm thirteen." Jannah tayi saurin katse ta.

"Toh koma dari uku ne kin taba ganin daya daga cikin dagin uwarki sun zo daga Iraq? Har ke kin sameni ma kike da bakin yi min maganar banza". "Jannah apologise" Sumayya ta fada cikin baci rai. Ita bata taba tunanin Jannah na da baki haka ba. "I'm sorry Granny" "Munafuka sai kace ba ke kika koya mata ba" Umma ta harari Sumayya.

"Jannatul Firdaus, Rahmatullah" suka jiyo an kira su. Aguje Jannah ta mike da gudu ta rungumi k'anin mahaifin nata. "Uncle Abdul! Ya Allah missed you so very much" "Me too Jannah" "Welcome Uncle" Rahma ta gaishe shi. Daka suka ci gaba da hira har dare yayi.

*

Satinsu biyu suka fara shirin tafiya. Ana cikin breakfast Umma ta fara magana. "Ahmad listen to me." "I'm all ears mother" Al'amin ya amsata, duk da yasan cewa korafi kawai zata yi tayi.

"Yar ka ta girma kuma har takai wani minzili so nake ka koma gida Nigeria da zama tunda kaki k'ara haihuwa ko ince matarka tak'i kuma kaki k'ara aure toh bazan yarda ku lalata yariya a karancin shekaru ba. Ko yanxu ka gani yara basu da kayan sawa sai riga da wando kokuma dogon riga. Kwatakawata basu da natives ko daya? " shiru Ahmad yayi kamar wanda aka watsa wa ruwan sanyi. "Da kai nake shanyanye. Yarinya karama ta mallake ka"

"Umma ina laifin ki bamu lokaci?" Ya fad'a a sanyaye dan shi ko kadan bashi da ra'ayin komawa Nigeria saboda irin tsana da tsangwamar

"A wani dalili?"

"Umma su Jannah basu gama semestern nan ba. Ina laifi idan suka karasa exams sai muje hutu."

"Hutu? Haka ita matar taka ta kitsa maka? Toh naki."

"A'a Umma gani nayi basu saba da can ba amma a hankali zasu saba idan suna zuwa hutu"

Cikin sauri Hafsat matar Ya Umar wanda k'ani ne ga Ya Majid kuma yayan Ahmad tasa baki. "A'a Ahmad hakan bai dace ba kamata kawai yayi su tare ai rayuwa ce. Ina amfanin ace yarinya yau tana hutu a London, gobe tana Italy jibi tana Morocco duk a sunan hutu sanna zuwa Nigeria ya gagare ta. Bayan can ne asalinta?.

"Umma a bashi lokaci gaggawan ai ba amfani. Sannan Hafsa Umma da Yaya take magan ba dake ba ai ko ba komai ya girme ki amma kike tsoma baki cikin abin da bai shafeki ba" Uncle Abdul ya fada. Dama Kwatakawata basa shiri da ita saboda mugim halinta.

"Kai ya shafeka ko?

" Eh mana tun da yaya ne ne ba k'anin miji na ba".

"Kuyi hak'uri" Sumayya ta fada.

"Ae ya zama dole Aunty. Yauwa get ready yau Jannatul Firdaus da Rahmatullah zasu nuna mana Toronto. Ummul Khair you are coming ko da Ya Majid bare zoba dama he's a fun killer"

"Banda Granny!" Jannah tayi ihu.

"Sai naje dan ubanki" Umma ta fada rai bace yayin da kowa ke dariya.

Continue Reading

You'll Also Like

167K 15.4K 30
"သူက သူစိမ်းမှ မဟုတ်တာ..." "..............." "အဟင်း..ငယ်သူငယ်ချင်းလို့ပြောရမလား..အတန်းတူတက်ခဲ့ဖူးတဲ့ အတန်းဖော်လို့ ပြောရမလား...ဒါမှမဟုတ်..ရန်သူတွေလို...
39.6K 109 21
Just a slutty whore who needs to get all her thoughts and feelings on a page. Loves being submissive to her dom daddy 🧎‍♀️ DISCORD- jessieleihuyg8t...
128K 1.6K 51
𝐈𝐭𝐬 𝐭𝐡𝐞 𝐟𝐢𝐫𝐬𝐭 𝐝𝐚𝐲 𝐛𝐚𝐜𝐤 𝐭𝐨 𝐬𝐜𝐡𝐨𝐨𝐥 , 𝐀𝐚𝐥𝐢𝐲𝐚𝐡 𝐢𝐬 𝐧𝐨𝐰 𝐢𝐧 𝟏𝟎𝐭𝐡 𝐠𝐫𝐚𝐝𝐞, 𝐰𝐡𝐢𝐥𝐞 𝐬𝐡𝐞𝐬 𝐭𝐡𝐞𝐫𝐞 𝐬𝐡...
38.2K 2.5K 61
𝐭𝐡𝐞 𝟐𝐧𝐝 𝐛𝐨𝐨𝐤 𝐨𝐟 𝐬𝐡𝐨𝐫𝐭 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐢𝐞𝐬 𝐚𝐛𝐨𝐮𝐭 𝐨𝐥𝐢𝐯𝐢𝐚 𝐫𝐨𝐝𝐫𝐢𝐠𝐨 𝐚𝐧𝐝 𝐲/𝐧'𝐬 𝐦𝐞𝐞𝐭-𝐜𝐮𝐭𝐞𝐬/𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐬𝐭𝐨𝐫𝐢�...