Sarkakiya

Por Bintabusaddiq

6.5K 540 2

Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruw... Mais

Hadari 🌧🌧🌧🌧
Wacece ita
Ina zan ganta😪
Tsefe
Akasi
Alkawari
Jigo
Abaya
Sakaci
Sarah
Sarah (ii)
Matambayi
Kwarjini
Cherry🍒
Hutu
Rarrashi
Monday
Boyayyen mosoyi
Reply
Malami
Malam Jabir
Birthday
Vacancy
Alhaji Audu 1
Alhaji Audu 2
Alhaji Audu 3
Rikici master
Muhawara
Interview
Interview 2
Interview 3
Tsohon ciwo
Selection
Office
Se yaushe ne
Takeaway
Aura
Gyara
Tsawa
Bacci
Yaudara
Dokoki
Dizgi
Kuka
Why
Tuhuma
Barazana
Al'ada
Al'ada 2
Dariya
Tour
Kira
Sabon Al'amari
Dinner
Dinner 2
Dinner 3
Sorry
Aniversary
Aniversary 2
Aniversary 3
Night call
Laifi
Asbiti
Wa take so
Lallashi
Makoci
Tafiya
Confession
DSS
Amana
Soft spot
I love you
Kano
Kano 2
Dan uwa
Tun farko
Dame ya zo
Zumudi
Shakku
Tambaya
Rejection
Asbiti
Alfarma
Tashin Hankali
Aure
Mari
Depression
Rashin lafiya
Rashin lafiya 2
Fire🔥🔥
Punishment
Tafiya
Dalili
Maamah
Hakki
Sweet night
Babymorry
Habo
😢😭 2
Allahu Akar
Wasiyya
Motherhood
Paris
Kayan barka
Iv
Station
Ango
Chanjin yanayi
Alkawari ya cika
Karshe

😢😭

42 4 0
Por Bintabusaddiq

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
A kwana kadan umar ya chanza kamar ba shi ba saboda yadda yake jin jiki ba kadan ba, kasan idon har purple yayi. Kana ganin shi kasan yana jin jiki don Ya rame yayi baki.

Alh ibrahim da ke zaune a kusa da shi yaji umar yace
"Dad"

Yadda ya kira shi ya matukar bashi mamaki saboda a iya sanin sa tun bayan mutuwar sarah umar ya dena ce masa dad.
Idanun Alh suka cicciko da hawaye. Da sauri ya kama hannun umar tare da fadin
"Ina jin ka my son kana bukatar wani abu ne"

Umar ya girgiza kai sannan yayi magana da kyar
"Nasan nayi maka abubuwa da yawa na rashin kautawa da basuyi maka dadi ba. Bana so na tafi ban roke ka gafara ba akan kura kuren da nayi da maganganun masu zafi da neke maka. Kayi hakuri ka yafe min"

Hawayen da suka taru a idon Alh ne suka zubo ya kara rike hannun umar ya matse gam tare da fadin
"Ni ne zan nema gafara a wajen ka, ni zan ce ka yafe min. Ba kai ne kayi min laifi ba nine nayi maka. Decisions din da na dauka a rayuwa ta sunyi affecting dinka sosai and i am to blame. Nayi su a bisa jahilcin fakewar da nakeyi akan rayuwar ka nake so ta inganta. Ka yafe min umar, ka yafe min"

Kuka ne yaci karfin Alhaji ya ci gaba da yi wiwi, umar ma kukan yakeyi.
"Na yafe maka dad Allah ya yafe mana baki daya"

Suna cikin wannan kukun ne khairi ta fito daga toilet, da sauri sauri suka fara share hawayen su saboda sun san idan khairi ta gani zata kafa nata, kuma nata kukan baya jin rarrashi. Kullum a cikin kuka take haka yasa kullum fuskar ta a kumbure take.
Tana ganin su taga emotions kala kala a kwance a faces dinsu. Ta samu guri ta zauna suka ci gaba da tagumi, bini bini se ta share hawayen da ke fito mata ta gefen ido.

Umar ya taba kumatun ta yana murmushi, kana ganin murmushin kasan na wahala yake yi sannan yace
"I have missed seeing your bright face"

Khairi tayi murmushi me ciwo, hawaye na biyowa kan kuncin.
Umar ya sa hannu ya share mata hawayen da ke zuba yana girgiza kai alamar tayi shiru.

Alh ibrahim yana ganin abun na masoya ne ya tashi sum sum ya bar dakin don ya basu space.

Khairi ta rike hannun sa da yake share mata hawayen tana kissing ko ta ina.
"Please get well soon, i want us to be back home. Ina so much koma gida mu ci gaba da rayuwar mu yadda muka saba"

"Do you love me?"
Umar ya tambaya yana kallon cikin kwayar idon ta

Wani zazzafan hawaye ne ya kwace mata, bata taba zaton ze bijiro mata da tambayar nan ba. Murya na rawa tace
"I do, wallahi i do. I love you soo much"

Umar ya sake murmushi sannan yace
"And that's enough for me, nayi ta son naji wannan kalaman daga bakin ki and finally naji su yau"

Khairi ta rakwafo tayi hugging dinshi yana kwance tana wani irin kuka me ban tausayi, shi kuma umar yana shafa bayan ta yana cewa
"shhhhhh its okay"

A haka umma da Abba da Alhaji ibrahim suka tarar da su, basu san ma sun shigo dakin ba se da Alh ibrahim yayi gyaran murya sannan khairi tayi saurin tashi daga rungumar da tayi ma umar.

Gaba daya jikin abba da umma yayi sanyi ganin umar a condition din. Jikin ya rikice gaba daya, ga wasu machines da aka jojjo na masa. Umma kasa daure wa tayi ta fashe da kuka. Tana tuno yadda yar uwar ta zarah ta rasu da yarintar ta gashi yanzu danta ma rai a hannun Allah.

Da kyar abba ya iya rarrashin umma tayi shiru. Umma ta zauna a gefe kan gadon umar tayi mishi addu'a hawaye na zuba, har zata tashi umar ya riko hannun ta sannan ya rada mata wani abu a kunne wanda yasa umma ta kara fashewa da kuka.

Da gudu gudu ta tashi ta nufi hanyar waje kukan yaci karfin ta

Bayan lokaci kadan Abba yayi ma umar da Alh ibrahim fatan samun Lafiya sannan yayi musu sallama gaba daya. Khairi da Alh suka biyo bayan shi suna masa rakiya
Ko da suka fito bakin dakin abba yace musu su koma tunda akwai mara lafiya ba se sun raka su ba. Ya kara yi musu sallama sannan ya fita wajen umma wanda tun da ta bar dakin bata kuma dawowa ba.

ALH ibrahim da khairi suka koma dakin jiki a mace, ko da suka shiga sun tarar da umar yayi bacci. Dududu fitar su be fi minti 5 ba amma har bacci ya dauke shi.

Khairi ta danyi murmushin jin dadi tace da Alhaji
" Alhamdulillah kaga umar ya samu bacci daman jiya beyi bacci ba kwata kwata"

Cikin jin dadi Alh yace
"Masha Allah, to bari na fita na karbo sakon Umar da yasa a kawo daga Abuja. Sun kira ni dazu cewar sakon ya iso Yanzu zanje na karbo a DHL"

Khairi ta amsa da" to shikenan a dawo lafiya"

Bayan fitar Alh khairi ta dan tattara dakin, ta saka magungunan sa a inda ya kamata. Ta wanke cup din da ya ya sha pudding. Ta de yi kai kawo a dakin tana kintsa gurin. Bayan ta gama ta shiga toilet tayi alwala tayi sallar la'asar.
Wannan zirga zirgan da tayi ya dauke ta kusan minti 30. Ta gama komai ta dawo ta zauna a kujerar kusa da umar tana kallon sa.

Abun da ya bata mamaki shine yadda ta barshi haka ta zo ta tarar da shi ko yatsa be motsa ba. Gashi de bacci yake cikin kwanciyar hankali, mutum ma baze ce mara lafiya bane saboda a kankanin lokaci fuskatsa tayi washar tayi kyau.

Cikin damuwa ta taba hannun shi taji shiru, ta kara taba shi da karfi shima shiru, ya kamata ace ko da bacci yake idan an taba shi yayi responding. Tana kara taba hannun ta ga hannun ya fadi sharaf. Nan da nan hankalin khairi ya tashi ta fita daga dakin da gudu tana kiran nurse

Suka dawo dakin ita da nurse da gudu, nurse ta danyi dube duben ta sannan tace tana zuwa ba tare da tayi ma khairi wani bayani ba.
Se ga nurse sun dawo tare da dr ilyasu, kana ganin
Fuskokin su kasan suma hankalin su a tashe yake.
Dr ilyasu yayi dube duben shi, ya taba nan ya taba can, ya sa stethoscope a nan ya sa a can har kusan minti 5 yana abu daya. A sanyaye dr ilyasu ya kalli nurse tare da girgiza kai, nan da nan damuwa ta bayyana a furkar nurse din

Murya na rawa khairi tace da dr ilyasu
"Dr yaya? Kaga baya motsi, me yake faruwa? Ko zaa maida masa oxygen dinne?"

Dr ilyasu yayi shiru yana kallon kasa ya rasa ta ina ze fara fada mata abun da ya samu umar.

Khairi ta kara tambayar sa kuka ya fara cin karfin ta
"Dr baka ce komai ba, me ya samu umar"

Dai dai nan Alh ibrahim ya shigo dakin dauke da jaka a hannun sa, yana ganin yadda akayi cirko cirko gaban sa ya fadi. Khairi tana ganin shi tace
"Alhaji kaga sun ki su fada min me ya samu umar, tun dazu be motsa ba"

Alh ya kalli dr ilyasu yana neman answer a idon sa. Suna hada ido Dr ilyasu ya girgizawa Alh kai, ko be fadi komai ba Alh ya riga ya gane. Cikin tsananin tashin hankali yaji kafar sa tayi sanyi baza ta iya daukar sa ba, Jiri ya kama shi yayi diri diri ya rike bango tare da maimaita

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

Khairi tana jin abun da Alh ya fada ta tabbatar da zarginta ya zama gaskiya. Da gudu ta koma kan umar ta fara girgiza shi da karfi

"Ka tashi umar, ka tashi dan Allah. Mutuwa ba abun wasa bane. Dan Allah ka tashi"
Khairi ta gama girgiza shi taji shiru, ta dawo gurin dr cikin rudu tana cewe
"Dr kayi wani abun mana. Baka gani bacci fa yakeyi,
wallahi bacci yake"

Ta janyo mask din oxygen ya saka ma umar, gaba daya ta rude kamar zaucacciya
Ta kuma dawowa gurin Alhaji
"Alhaji kayi masa magana idan yaji maganar ka ze tashi"

Hankalinta ne ya kai kan jakar da ke hannun Alh. Da sauri ta warchi jakar kamar mahaukaciya ta nufi umar da gudu. Babu wanda ya iya hana ta a dakin, kowa da kalar tashin hankalin da ya shiga

"Ga sakon ka ma ya zo, yanzu Alhaji ya je ya karbo. Ka bude idon ka ka gani kaji"

Ta ci gaba da girgiza shi da karfi har se da nurse ta zo ta kama ta.
"Kiyi hakuri ummulkhair, LOKACI YAYI SE HAKURI"

Kalmar nurse din ne ya dawo da ita reality wanda yasa maganar ta tsarga mata. tabbas da alama umar ya tafi kenan.

Ji tayi kanta ya fara juyawa, taji wani irin matsainaicin tashin hankali da bata taba shiga ciki ba. A take taji wani kulukun abu ya tsaya mata a makoshi yana hana ta shakar iska. Kanta yana sarawa, zuciya na bugu kamar zata cire, baki na rawa amma ta kasa cewa komai.
Bata ankara ba se jinta tayi a ta fadi jikin nutse, daga nan kuma ba ta kara gani ko sanin komai ba, she went blank.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

Continuar a ler

Também vai Gostar

965K 71.7K 37
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
126K 7.2K 45
Complicated🤐🤐🤐 Find out👇👇👇
7.5K 310 36
labari mai matukar ban tausayi, son zuciya, soyaaya mai zafi da shiga rai, hadi da nadama.....
10.3K 566 16
A wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki...