A DAREN AURENA(SABON SALO)

By MissDmk

1.7K 68 1

Based on True life event More

Complete story(chapter 1-21)
Page 1
Page 2
Page 3
page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
10
12
13
15
16
17
18
19
20
21

14

48 0 0
By MissDmk

*A DAREN AURENA*
  _SABON SALO_

Page 14

Doctor yace Abba ya na bukatar gannin Aisha, ina jin haka na shiga da sauri, hawaye na zuba daga idanuwa na, na durkusa a gabansa,ina mai nema gaffarah

My Doctor ? Abba yayi magana cikin taushin murya, kasa amsawa nayi sai embracing insa da nayi, ina kuka mai tsuma zuciya,  Abba am so sorry for the pain I caused you, please Abba forgive me..

I've already forgiven you but please come back home, yayi maganar yana kallona...

Inajin haka na tsaya cak da kuka na, ina kallon sa, haryanzu dai Abba baya son aurena da Mujaheed? Jin nayi shuru yace My Doctor?

Abba... Ban karasa magana ba aka shigo da small Abbah dake famar kuka, cike da mamaki Abba ke kallon yaron, maimakon na amsa yaron na mika wa Abba, ga takwaran ka Abba. Nayi maganar ina kallon expression insa..

He was memontarily dumbfounded and loss for words...can yace

Aisha kece da yaro? Yayi maganar cike da mamaki..

I reluctantly smile and tilts my head up, alamar Eh.

Kasa cewa kome Abba yayi sai kallon Al'ameen  dake famar kuka,
Can yace Allah mai iko, Allah ya raya mana shi, yayi maku albarka ya na fadin haka, ya mikamin yaron, amsa Abbah nayi ina lalashin sa, Ummah tace sai kije kiji dashi ai...

Mikewa nayi nabar dakin na samu wuri na zauna..

Abbah kallon Ummah yake cike da mamaki, can yace shikenan a haka kaddaran Aisha yazo? Aisha ne haka Maryam? Dan Allah ki duba yadda Aisha ta koma? Sai kace ba ita ba? Abba yayi maganar cikin damuwa da daci.

Honourable to ya zamu yi? Tunda ita ta zabar wa kanta? Dan Allah Hon ka kwantar da hankalin ka, tunda tana tunanin farinciki na tare da wannan yaron.sai mun bita da adu'a kawai..

Ai na hakura da tsamani cewa Aisha za ta dawomin kamar yadda nake zato Maryam? He smiled in grief, sai kawai gannin ta nayi da yaro?yanzu na hakura da saka burina akanta Maryam.

Gara haka Hon. Shekara kusan biyu kenan kake dauke da fushin ta, gara ka hakura kawai mu bita da adu'a, Ummah tayi magana cikin taushin murya..

8pm

Duk muna dakin da Abba yake, Addah  Aseeya na ba su labarin abinda Ya Fahad yayi. Da kuma yanayin da ya tsince ni kafin har akasamu damar ceto rayuwana dana da'na..

Ya Nura yace ai ban taba ganin mara zuciya irin Fahad ba, in banda rashin zuciya irin tasa Walhi ni ko kara waiwayar ta ba zanyi balle har na taimaka masu..

Innaro tace A'ah Nura wannan hali ba halin Krista na gari bane, karka kuma, idan kana so maganar nan taka tayi armashi ga wacce za kayi wa, tunda yarinya ta koma Dodi minal Dodi ba taji maganar manya saide na mijinta, oh oh ni naga jaraba, Innaro tayi magana tana rike da haba, to ke Shatu na tambayeki yanzu da kika  auri wannan fakirin riban nawa kika samu?

Shiru nayi kamar ba dani take yi ba.. Coz duk maganar da su keyi bai dame ni ba, tunda yanzu Abba ya yafemin.

Ke dake na keyi kike wanni mirsisi da ido kamar a murje gyada, Innaro tayi maganar tana nunani da sanda ta, can kuma tace dan Allah Nura ka dube ni ka dube ta, ko ni da nike tsohuwa nafi ta ganuwa, kalle ni shadaudau dani gwani sha'awa amma kalle ta kamar an murje taliyar hausa, Sam ba fasali..

Addah Aseeya tace ai Innaro ko miye zaki fadi ba zata saurare ki ba, zuciyar a toshe yake..

Ashiya to ai Dodi ce shiyasa ba zata fahimce yaren ba, in baki labari lokacin ina yammata da naso nima na zama Dodi minal Dodi kamar yadda kika ga wannan kanwar taki, amma Allah ya kareni ban shiga figar kazar wahala ba,tuni nabi biyayar iyaye na auri Alhaji Gidado, to ba gashi ba sai gannin albarka na keyi ko ta ina ba? Hajj da Umrah duk shekara, kaji sai naci na ture amma Walhi ko kaffara ba zanyi ba, rabon ta da nama tun tana gidan Aminu,

Addah tace ina alamar dadi daman a wannan jiki Innaro? Mutum duk ya tsotse ya kyanjame, wai haka fa ta dan farfado kenan, da lokacin da take asibiti ne, sai kinyi mata kuka

Ahab Yo hauka ma akeyi da zaki ga alamar dadi a wannan jiki? Ai dadi shine kaci nama kasha madara, to itafa? Kin ga ina wanni zata ga kajin da zata ci? Ashiya kika ce zanyi kuka? To aradu ba wanni kukan da zanyi mata, ai bani na ake ta ba,
Gannin surutun bame karewa bane Abba yace lokacin barcina yayi Hajiya..

Wato korar mu kake yi Aminu ?dan mun hana kanmu zaune da tsaye akan ka? To shikenan Nura zo ka mayar dani gida,Innaro tayi magana rai bace..

Ana cikin haka JayD ya shigo dakin, tsabar farinciki ganin sa, yasa naji kamar nayi hugging insa..

Durkusawa har kasa yayi yana gaida kowa na dakin kafin ya mike naba shi gun zama ya zauna,

Innaro tace ka ga dan albarka yaji ambato, yanzu fa nake tambayar kishiyar tawa nace ina balarabe ashe kana tafe...

Cike da mamaki kowa ke kallon Innaro..

To arziki bana Allah bane wai nikam na tambaye ku? Mutum ke ba kansa arziki? Duk kun bi ku dame yaranan, kun sa su a bakin duniya? kaji balarabe dauki matar ka, kayi gaba ke kuma Aisha ki kama mijinki ki liliya shi kar wata ta kwace maki shi, dan maza masu kyau mata binsu suke yi kamar yadda Bunsuru ke bin akuya, nima akan Gidado sai da nayi tsaye, kafin na samu kujeran mulki a zuciyar sa, Ashiya ya naga kina harara na ne?

Adda Aseeya tace Innaro mai bakin ganga..

Ashiya ni kike zagi? Akan na goyi bayan gaskiya akan karya? Yo so kuke Akashe auren mu banu? Kema kanki sheda ce Shatu bata  gama koduwa ba, a wannan auren?

Abba yace Nura dauki Hajiya ka kaita gida ta huta. Dan yaga idan ba barin nan Innaro tayi ba kawai jagule kome za tayi...

Nura ya mike ya dauki jakar Hajiya hade da rike mata sanda takawa dan ta mike..

Shima Mujaheed ya mike hade da daukar Abbah a hannun sa, yace Abba, Ummah Allah ya kara sauki mu zamu koma Akku yau...

Cike da mamaki kowa na dakin ke kallon sa..

Addah tace kai ko ka bari a sallame Abba ai kafin ta koma gidan naka ko?

He sneered before he said ina jiran ki a waje, the arrogance of his aura made me to stood up..
Abba bara mu koma gobe in shaa Allah zan zo kafin a sallame ku,

Allah Aisha baki da hankali, Aseeya tayi maganar cikin daci, Ummah tace to shikenan Allah ya kaiku lafiya sai kin dawo gobe

Tana fadin haka nabi bayan sa cikin hanzari

Salati dakin ya dauka, har Innaro dake tsaye tsakin baki hade da rike haba tayi cike da mamaki, gaskiya Aminu sai kunyi da gaske, niko nace Aminu sai kunyi dagaske ba haka yabar yarku ba, nima ince ba wanda zai zabi wiya ya bar dadi, ashe dai da walakin goro a miya?

Abba reluctantly smile and loss for words.

11pm

Haka muka issa gida ba Uhm ba Uhm Uhm, abin har mamaki yake bani,

Ummah ta fito tana mana Sannu da zuwa, hade da tambayar ya mai jiki, amsawa nayi kafin na gaida ta, bayan nan shige daki..

Sai can ya shigo rike da Abbah dake barci ya kwantar dashi..

JayD ya Abuja? Har angama kome? I'd to burst out the silence..

He gave me a disdain look before he undid his shirt off..

JayD ina magana fa...?

Magana kike yi bacin kinsa kinyi laifi..? Yayi maganar hassale kuma a kausashe..

Haba JayD na baka hakuri fa? Kuma ai mahaifi ba abin wasa bane..

Oh mahaifi ba abin wasa bane? Mijine abin wasa ko? Shiyasa naga kun taru dake da iyayen naki kuke zagina?

A'ah ba haka ba ne JayD, JayD ba wanda ya zage ka and besides I went there because I thought I'm gonna lose him forever..

Oh you now know his worth? He yelled at me, shiyasa kika bada kofar da ake ta zagina, idan tallauci na ya dame su miya basu bani arziki ba tudan su ke badawa?

How do you mean JayD? Ya kake irin wannan maganar akan iyayena huh?

Oh you now know there worth ko? Idan kinsa iyayen ki ne then why did you choose me over them...?

JayD you're scaring me now and I don't know why you are bringing this up?

Tambaya na ma kike yi? Bacin kin raina ni? wacce mata ce zata saka kafa ba tare da izini mijin ta fita?sannan harta tsaya a gun da ake zagin mijinta wai nikam Aisha anya kina so na kuwa? Dan mai sonka baze zauna inda ake zagin ka ba?

Dan Allah kayi hakuri hakan baze sake faruwa ba. Nayi maganar cikin lalashi hade da yin kuka, kuma walhy ba wanda ya zage ka..

He sighed deeply and gave me a side long glance full of hostility. Wato Innaro karya tayi kenan?

I am sorry kaji JayD, Innaro rikicin tsufa ne, amma ba wanda yayi maganar ka..

Kinsa Allah idan ba kiyi warning yayarki ba, sai na cin mata mutunci ko da yake ba laifin ta bane laifin ki ne, tunda ke kika bata kofa..

Gannin fa ba saurara na zeyi ba, na dinga bashi hakuri ina kuka..can yace

It okay ya wuce, yayi maganar a kausashe, next week zamu koma Abuja, tunda week za kuyi resuming..

Allah ya kaimu JayD, gobe ina je asibiti sai nayi masu salama tafiya gabadaya..

Shiru yayi baice dani kome ba..

Washe Gari Da safe

Bayan nayi abinda da zanyi na gama, na shiriya tsaf hade da kiran Mimi ta zo ta rakani..

Bayan munyi ma Ummah salama zamu fita kenan, JayD ya shigo ciki gidan, daman tun da ya fita sallah asuba bai shigo ba...

Ina zaku yayi maganar a kausashe..

JayD ka manta da batun zuwa asibiti...?

Dake da wa kukayi maganar asibiti? Yayi maganar a hassale

I told you ai, kuma your response was... Ban karasa magana ba ya dakka min tsawa yace just shut up and get inside..

Cike da mamaki nace JayD ka manta yau za a salamai Abba?

Aisha idan kika sa kafa kika fita gidan nan, to ki dauki hakan a matsayin Saki..... !

*Ma abotan karatun A DAREN AURENA SABON SALO, shin kuna tunanin Aisha za ta asibiti ko-ko zata bi umarni mijinta?🤔*

*Shin Innaro na da fans? Ko acire ta acikin book din? 😄*
*Littafin na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya kafin ya karanta domin hakkina ne. Biya ta wannan account din: FATIMA DAHIRU  UBA 2291620442 sai ku nuna shaidar biya ta number 09074267236. Dan Allah banda vtu.*

Continue Reading

You'll Also Like

36.8K 7.6K 35
OPEN! Join a community of passionate readers, where the love of literature meets a welcoming and professional atmosphere.
191K 20.4K 56
"කේතු දන්නවද මම කේතුට කොච්චරක් ආදරෙයි කියල ?" "හැමතිස්සෙම වචනෙන් නොකිව්වත් සර්ගෙ ඇස් මගේ ඇස් එක්ක පැටලෙනකොට ඒ දිලිසෙන ඇස්වලින් මට පේනවා සර් මට කොච්...
8.7K 292 56
WOC SERIES SAMPINGAN XAVIER ADREAN X DAHLIA ARYANA Dahlia Aryana. Dipaksa bekerja di kelab malam oleh ibu kandungnya sendiri. Berhari-hari dipaksa me...
14.9K 424 13
"𝑪𝒂𝒖𝒈𝒉𝒕 𝒎𝒚 𝒆𝒚𝒆, 𝑰 𝒂𝒊𝒏'𝒕 𝒆𝒗𝒆𝒏 𝒂𝒕 𝒕𝒉𝒆 𝒔𝒑𝒐𝒕 𝒄𝒖𝒛 𝑰 𝒃𝒆 𝒐𝒏𝒕𝒐 𝒚𝒐𝒖"