Sarkakiya

By Bintabusaddiq

6.5K 525 2

Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruw... More

Hadari 🌧🌧🌧🌧
Wacece ita
Ina zan ganta😪
Tsefe
Akasi
Alkawari
Jigo
Abaya
Sakaci
Sarah
Sarah (ii)
Matambayi
Kwarjini
Cherry🍒
Hutu
Rarrashi
Monday
Boyayyen mosoyi
Reply
Malami
Malam Jabir
Birthday
Vacancy
Alhaji Audu 1
Alhaji Audu 2
Alhaji Audu 3
Rikici master
Muhawara
Interview
Interview 2
Interview 3
Tsohon ciwo
Selection
Office
Se yaushe ne
Takeaway
Aura
Gyara
Tsawa
Bacci
Yaudara
Dizgi
Kuka
Why
Tuhuma
Barazana
Al'ada
Al'ada 2
Dariya
Tour
Kira
Sabon Al'amari
Dinner
Dinner 2
Dinner 3
Sorry
Aniversary
Aniversary 2
Aniversary 3
Night call
Laifi
Asbiti
Wa take so
Lallashi
Makoci
Tafiya
Confession
DSS
Amana
Soft spot
I love you
Kano
Kano 2
Dan uwa
Tun farko
Dame ya zo
Zumudi
Shakku
Tambaya
Rejection
Asbiti
Alfarma
Tashin Hankali
Aure
Mari
Depression
Rashin lafiya
Rashin lafiya 2
Fire🔥🔥
Punishment
Tafiya
Dalili
Maamah
Hakki
Sweet night
Babymorry
Habo
😢😭
😢😭 2
Allahu Akar
Wasiyya
Motherhood
Paris
Kayan barka
Iv
Station
Ango
Chanjin yanayi
Alkawari ya cika
Karshe

Dokoki

53 5 0
By Bintabusaddiq

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Khairi ta kwankwasa kofar office din a tsorace dan yau bata san me zata tarar a office din manya ba. Ta dade tana kwankwasawa amma baayi magana ba kamar da wasa ta gwada budewa taji kofar ta bude. A hankali ta tura kofar kamar barauniya

Tana daga ido sukayi ido biyu da umar. A zaune ta ganshi a kujera, duk da sun hada ido hakan be sa ya dauke idon sa daga kanta ba ya ci gaba da kallon ta.
Ta shiga cikin office din kamar me sanda

"Good morning sir"

Babu answer, ta kara gaishe shi nan ba babu answer. A sulale ta zauna a kan kujerar sofa dake office din, saboda ta kula idan bata zauna din ba baze taba ce mata ta zauna ba.

Se da sukayi kasan hour daya babu wanda yayi magana a office din, khairi ta gaji da zaman rashin aikin yi sannan tayi magana
"Akwai abunda zanyi maka....."

"Me yasa baki dawo jiya ba"
Be bari ta kai karshen maganar da takeyi ba yayi mata tambayar.

Jiya da ta fito daga office din Alh ibrahim gida ta wuce, yanayin yadda taga Alh ibrahim yasa jikin ta yayi sanyi matuka, bata san yadda zata fuskanci abun da yake tunkarar ta ba. Kwakwalwarta gaba daya a toshe take shiyasa ta wuce gida don ta huta

" naga lokacin tashi a aiki yayi ne shiyasa na tafi"
Khairi ta bashi answer

"Interesting"
Umar ya fada tare da nade kafar sa yana kada ta a hankali sannan ya cigaba da magana
"Daga yanzu se har na bar office sannan zaki tafi"

Khairi ta dago kai da sauri sannan tace
"Ko da lokacin tashi ya wuce?"

Be bata answer ba ya ci gaba da kada kafa yana mata wani kallon tisiye, da taga ba ansa ze bata ba se ta saukar da kanta kasa ta fara wasa da yatsun hannun ta. Office din ya koma shiru kamar makanarta

Bayan lokaci kadan wayarta tayi kara alaman message ya shigo. Ta sa hannu a jaka ta fito da wayar, Message din da ta gani ne ya sa ta murmushi

"I miss your beautiful smile, i miss been close to you"
Ta dade tana kallon message din sannan tayi reply

"Please who are you"

An dauki mintuna kadan sannan taga reply dinsa

"Your secret admirer, secret lover❤️"

"Shi secret admirer bashi da suna ne"

"Ya na da shi mana, sunan me dadi kuma"

"To meyasa ake boye sunan"

Ummu!!!!!
umar ya daka mata tsawa, se da ta wayarta ta fadi daga hannun ta
A razane ta kalli umar

"Me ya faru?"
Tayi tunanin wani abu ne ya faru ma

File din da ke hanun sa ya wullo mata, file din ya fadi kusa da kafar ta.  Wani irin bakin ciki taji a ya tokare a makogwaran ta. Dan meyasa baze ce tazo ta karba ba ze wullo mata kamar ba mutum ba.

"Dauko file dinnan"

Ya fada tare da hade rai, khairi ta tsaya shiru tana tunanin abunda zatayi mishi. Cin mutuncin nasa kuma ya fara yawa, ga tsawar da ya daka mata sannan ya wullo mata file. Ko baiwar gidan su ce ay se haka.

Kallon file din tayi a wulakance sannan tace
"Me yasa baza ka ce na zo na karba ba"

"Ganin dama"
Ya amsa da gadara

Magan ganun Alh ibrahim ne ya dawo mata, yadda ya bata hakurin duk abunda umar ze yi mata na cin mutunci ta shanye ta kyale shi..
ka ci darajar mahaifin ka ta fada a ranta

A hankali ta durkusa ta dauki file din sannan ta tako inda yake itama ta dan buga file din da karfi akan table dinsa ta hade gira

Umar ya dago ya kalle ta da fuska kamar matattce, itama kallon shi tayi da tsana kuru kuru a fuskar ta

"Bude"
Ya fada tare da dauke idon sa a kanta,

Khairi ta dauki file din ta bankada page din kamar file dinne yayi mata lefin

"Karanta"
Ya kara fada da murya a dake.

Khairi ta fara karanta abunda ke cikin file din.
Dokoki da ka'idoji ne ya rubuta. Dokokin sun kunshi

[Se har ya bar office kafin ta bar office din,

kada ta sake ta shiga harkar da baa sata ba,

babu yi masa bincike,

baba ita babu alaka da kowa a company,

be yarda wani ya shigo inda take ba, kuma itama be yarda ta je wani gurin ba.

Babu bacci a office

Kullum idan tazo se ta shigo ta gaishe shi har se yace ta tafi sannan zata tafi, bata isa ta bar office dinsa ba se ya bata izini ]

Dokoki barkatai de wasu ma abun dariya.
Khairi ta gama karantawa sannan ta ajye file din a kan table dinsa.
"Na karanta, zan iya tafiya office dina?

"ki tafi da file din bana so naji wani excuse, don bana afuwa kuma baba yafiya idan aka saba min"

"No need"
Khairi ta fada fuska a daure sannan ta juya ta bar office din. Ya karata da masifar sa

Tana fita umar ya saki wani murmushin mugunta
Ya tuno yadda sukayi da Abdulkareem bayan fitar su khairi jiya, office din ya kasance daga umar se Abdulkareem

Umar yayi ma Ak kallon sama da kasa sannan yace
"Me ya kawo ka office dina"

Ak yayi hade rai sannan yace"
" me kake tunanin ze kawo ni"

Umar ya ja doguwar "hmmmmmm" yana zagaye Ak dake tsaye yana huci, ya sheke da dariya sannan yace
"Ummulkhair ???, saboda secretary dita ce yasa kazo?

Abdulkareem ya nuna girjin sa da hannu yana fadin
"Ummulkhair is mine, you will not harm her in any way, eles......."
Idonsa yayi ja, wani irin zafi yake ji a ransa, be taba tunanin umar ze shiga tsakaninshi da farin cikin sa ba.

"Elses what??? Me zakayi"

Abdulkarem ya furzar da iska a hankali sannan ya juya ya fita daga office din, yasan umar ogan sa ne amma kwata kwata bashi da girma ko mutunci a idanun sa, yanzun ma hakuri ya bawa kanshi saboda kar yayi abun da zezo yana da na sani

Yana fita umar ya sake bushewa da dariya, ya kara samun dalilin rike khairi a wajen sa, ummulkhair ta zama makamin da ze yaki Abdulkareem, harda baban sa ma. Wani dadi yaji a ransa da ya dade be ji irinsa ba, ya dade wani abu be sa yaji dadi a zuciyar sa kamar wannan ba.

Duk abunda ze taimake shi wagen ruguza company yake nema kuma khairi tana daya daga ciki.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

Continue Reading

You'll Also Like

45.7K 2.2K 51
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin k...
28.5K 1.7K 22
Tayaya ummi da salman zasuyi rayuwar aure wanda da abaya basu son junan su an hada su AUREN HAĎI ku biyoni muji yadda zata kaya
7.3K 254 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin lit...
39.4K 2K 19
Labarin sanyayyar tacacciyar soyayyar ruhi biyu.. Wanda akai wa auren dole da juna, Amman basu san da hakan ba. Shin ya zaman nasu zai kaya idan suka...