Kai leg din shi yayi tare da kai mata duka a cikinta, ya cigaba da dukarta, sai da ta farka, sannan ya rufe fuskar shi, kana ya saka glass akan idanun shi, cikin wani irin tsoro da mugun ciwo ta fara ja da baya, sai a lokacin ta fahimci Abinda Badar yake gaya mata.
_Duk yadda kike tsammani abun ba haka bane! Sir Mahir bai san kome ba! Bai san abinda yake faruwa ba! Karki yarda da kowa dan zasu cuce ki, yadda muke kallon abu ba haka bane Sir Mahir bai san kome._

   Wannan shine abinda ya gaya mata, dake akwai wutar tsanar Mahir bata fahimci haka ba, tana son magana amma ta kasa, zunzurutun shock da tayi dasu.

    Wai da taga fuskar Nazzir mutuwa zata yi, dan haka yana cikin waya ta shiga ƙoƙarin danna mishi ihu, da sauri suka kuma rufeta da duka.
"Kin gama mana aikin mu, me zamu yi dake? Dan haka zamu yi maneji da ke, zamu amshi abinda muke bukata daga gare ki."

         Dan haka suka kamota tare da rufeta da duka, kuma bawai da hannu ba da katako, sai da suka ga bata motsi sannan Manager ya shiga ƙoƙarin yaga rigarta tare da kokarin sai ya tab'a wandon ta kuwa shure shi, dan haka ta kuma cigaba da dukarta, karshe da suka gama kai ta wani dakin beraye suka yi sannan suka yi tafiyar su.

        ••• hankalin Mahir Hamoud Boualem, idan yayi dubu ta tashi, duk inda yake saka ran shi zai same ta, dan haka aka shiga nimanta tare da Nazzir da abokan aikin shi. A sanadin b'atar Noorh aka dakatar da shi tafiyar da zai yi, amma ya koma Lagos, dan dole ya hana idanun shi barci, sakamakon niman ta ko magana ma ya daina, sannan kullum da ita yake yawo.yaje har gidan su, abin bakin ciki suka ce ba yarsu nace tsintar ta suka yi dan sun san koda ta dawo zai yi wuya su yarda ta zauna a gurin su.

         Zuba musu ido yayi sannan yace musu.
"Kuna nufin marainiya ce?"
Tab'e bakin Baban Tasleem yayi sannan yace Mishi.
" Gaskiya labarin yarinyar yana da nisa, sannan muma tsintarta muka yi dan haka idan ka ganta kayi mata abinda tayi maka karka damu, mu ma idan tazo koranta zamu yi dan ba yar mu bace"

      Wannan furicin da suka yi, basu yi tunanin zai zame musu damuwa nan gaba ba, da wannan Mahir ya bar gidan, gashi bai da number ta, komawa yayi suka bashi number ta da kyar, sannan ya shiga nimanta.

         Tare da niman wani tsohon abokin shi da suka yi aiki a Afghanistan ya tura Mishi ya taimaka mishi da binciken inda take, maganar gaskiya Mahir ya damu, domin zargin shi da ake shi ya sace ta, kuma ya kasa cewa kome fatar shi ya ganta ya ci qaniyarta yadda sai ta gane bata da hankali.

        •• Lauyoyyin Ummin ta dauka Mishi aka kuma turo shi domin ana niman a b'ata Mishi suna sosai, sannan aka shiga niman ta tare da jiran ko mutanen zasu bukaci wani abu Kafin su saketa.

A gefe guda ana tracking number ta, wanda aka tabbatar tana cikin garin a wani gurin can. Sanan kuma Mahir da kanshi ya bada sana'arwa duk wanda ya same ta, ya bada ladar miliyan uku. Idan kuma mutanen da suka yi garkuwa da ita zasu ji, haka ce ta faru, domin kuwa suna jin labarin haka suka turo gidan tv Gaskiya ta Fi Kwabo, akan matuƙar yana son su sake ta, sai ya rufe Kamfanin shi.

        Sun bashi nan da awa ashirin da hudu. Shiru yayi sannan yacewa Nazzir.
"Ni kuma a cikin awa ashirin da hudu, zan fito da ita, amma ba zan rufe kamfanina ba!" Dan haka ya fita ya bar Office din shi, Nazzir yabi shi da hararar mugunta. Yana faɗin.
"Zaka mutu kuwa."

                Lokacin da ya kira Annur, ya gaya mishi layinta yana gab da tsinkewa, dan haka yayi maza ta tafi inda take kafin kome ya tsaya mata. Haka ya koma gida tare da sauya kayan shi bai dauki wali ba ya fita tare da niman wata motar haya, ya biya me motar kudi masu yawa, sannan ya amshi motar yace zai dawo Mishi da ita idan ya gama abinda yake son zai dawo Mishi da Motar.
    •• yau kwana biyar kenan, dakyar ta tashi da tsamin jiki, dan Allah ya taimaka sun bar kofar d'akin a buɗe, duba wayarta tayi da yake cikin aljuhun wandon ta, shafa ciwon da yake jikinta tai, sakamakon sake mata kare da akayi juya ya cije ta, bayan ya gama yagalgala mata kayan jikinta.

             Dakyar bra ɗinta yake rike da Beautiful Boons ɗinta wanda ya gama shan matsar Manager yana yi yana marinta, tare da gaya mata ta wuce limit, shi yasa suke mata wannan uƙubar, sannan ba Mahir yace zai zo neminta ba, kafin nan sai sun yagalgala namarta.

            Wani irin kuka ta saka, tare da kaicon rayuwarta, domin a yanzun da take jin Manager yana fadar sune suka turo mata kome tare da kashe Badar da saka hannun manyan shi, yasata tausayin Mahir, ga baki daya taji tsanar kanta da kanta, tana me niman ina zata ganshi ta roke shi ya yafe mata. Kallon kofar tayi taji alamar suna barci, mik'ewa tayi tana kokarin duba wayarta gashi network ɗinta babu kyau, jijjiga wayar tayi tare da mikewa tana dingishi tana niman network sai ya fito sai ya ɗauke.

     Da sauri ta kalli kofar tare da lek'awa, taga duk sun kwanta, sakamakon shan giya da suka yi.  A hankali ta fito tana bin bango, dan bayan kafarta zuwa agarar ta a kumbure suke, a hankali take sand'a har ta bar cikin falon, a gurin bude kofar ne kuma ake yinta, domin taga key din a kan Center table, takawa tayi ta isa gurin. Tana kai hannunta aka rike tare da magagin maye yace mata.
"Idan ka buɗe ka rufe!"
Gyada kai tayi sannan ta dauka tana juyawa dayan su na mik'ewa, ya kura mata ido. Sannan ya koma ya kwanta,  tana tsalleke wani, ya kama kafarta.
"Karki tafi, masoyi ta." Ya fisgo ta, kasa rintsa idanunta tayi sannan ta samu ta kwace kanta.

    Tana buɗe kofar ta rufe su ta cikin gidan, hango wasu guda biyu tayi suma sun sha sosai, dan haka taga rigar dayan su a shanya, ta dauka ta saka, tare da wani katon wando, tana sakawa ta fito nan ta ga wani karen da yafi na ciki girma, juyawa tayi ta koma da baya, Bayan gidan ta koma ta sami wani drum, ta haura da taimakon lada,ta haye hango nisar kasa da saman tayi tasan matukar ta diro ta kare mata, wani irin kuka ne ya kwace mata..yayinda zuciyarta ya kasu biyu, ta koma cikin gidan ne ta zauna su yi mata abinda zasu yi ko kuma ta dira koda ba zata rayu ba.( Toh ga inda ake yinta har naga yadda zasu cinye ta🤨) please Voting karku sani jin kasalar rubutun mana, jiya tsabar naga babu Voting ne naki typing fa 😂🤣 Alqur'an idan aka Cigaba da tafiya haka zan ware abuna.
#Mahir
#Noorh
#Nazzir
#Taslem....

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now