Wani dauke kai tayi tare da Cigaba da tafiyar ta, sai da tazo zata wuce, kawai ya saka mata, kafa. Garin tsallake shi ta zube dake skirt ɗinta irin me pencil din nan ne bakin shi.

Haka kayan suka watse baki daya, murmushi tayi sannan tace mishi.
"Wow thanks Baby!" Sannan ta mike abinta, yana mamakin yarinyar nan, tana saka kai zata fita, wata yarinyar ta watsar da yorgot a kasar, gashi shoe ɗinta irin flat din nan ne, zuciyarta na dukar tara tara, kawai ta kai kafarta kai, ji kake zuuuuiiiiiii farrrr, tana zamewa skirt ɗinta yana yagewa ta baya, komawa tayi ta zauna, sakamakon buguwar da tayi a k'ugunta. Amma taurin kai ya hanata ta nuna fushin ta, asalima murmushi ne akan fuskarta, dariya suka saka mata, abu daya ya hanata mik'ewa skirt ɗinta, gashi hijab ɗinta Dan Karami ne, ba kamar da, da take saka yadi uku da rabi har kwanjinta, yanzun kuwa yafi biyu ne, iya kacin shi k'ugunta yake rufawa, yagewar skirt ɗinta kuwa har samamta take jin shi, kuma ba karamin faduwa tayi ba.
"Yar jarida! Tashi mana, ko ba zaki iya daukar kanun labarai da yagaggen skirt bane?"

Cikin wani irin kuka ta d'ago kanta tana kallon yarinyar da take mata wannan maganar, hawaye ne suka shiga zuba mata sharrr.

"Sir Mahir Hamoud Boualem! Shi kenan naci kudina ku tayani murna, kace kana son ka ga faduwar ta, na fadar da ita har da sakata kuka, Sir Nagode sosai. Allah ya jikan Abbanka, Guys bye." Yarinyar ta mike tare da Kawayenta. D'aga mata hannu yayi hannun shi dauke da jarida.

Ya cigaba da abinda yake a hankali, yana kallon ta da wutsiyar ido, yana son yaga zata iya mik'ewa ko ba zata iya ba, so yake yaga tana da kunya ko bata da kunya. Tana zaune a gurin Allah ya kawo karshen rikicin sai ga wata mata da yaranta, sun zo sayan snacks, tana shigowa taga Noorh tana kuka sosai, ga mutane na shiga da fita, a ka'idar Mahir idan zai sayi abu kowa fita yake amma yau dake ya hada mata mugun abu, yace kowa ya zauna kuma abar kowa ya shiga.

Kallon Noorh matar tayi, dake babba ce.
"A'isha Omar Jimeta!" Subhanallahi, tashi mana!"
Cikin kuka tace mata.
"Ba zan iya ba, skirt dina ya yage."
Kallon Mahir tayi sannan tace mishi.
"Na zata Major an haife shi domin ya kara kasar shi da mata da yara ne! Ashe shi kare kimar shi yaƙe, na zata bankad'o abinda yake faruwa zai saka Major ya farka daga barcin shi ashe shi lokacin yake niman me hanyar daukar fansa, amma ba zan maka shishigi ba, Aydah jeki cikin mota ki dauko min zanin nan!"

Da sauri yarinyar ta fita, cikin zafin rai ya fice daga gurin, yana ganin tayi mishi laifi amma kuma once ana bashi laifin ta, kawo zanin yarinyar tayi matar ta mikawa Noorh ta daura a hankali sannan tace mata.
"Nagode Ummi"
Murmushi tayi mata sannan tace mata.
"Idan zaki yi aiki, ki fara da bincike. Haka zai sanya ki fahimci abinda kike bukata."
Gyada mata kai tayi amma bawai tana jin zata kyale Mahir bane, duk da kuwa taji shawarar matar amma tabbas sai ta rama yau Insha Allah.
Godiya tayi mata, sannan ta fita ko ta kan kayanta bata nufa ba, ta bar gurin, abin hawa ta koma ya kaita gida, sai dai ta manta bata amshi Number matar ba. Tana isa cikin dakin su, dan taga gidan babu kowa, dauko kayan ta tayi ya shiga isar da abubuwan da yayi mata, tana gamawa tare da wasu bayanai dangane da mutuwar Badar.

Tana gamawa ta mike ta manta da abubuwan a gurin, ta shiga ban daki, Tasleem ba Shigowa taga, abubuwan da tayi, ba tare da shakku ba, ta tattara kome, ta tura wayar ta sannan ta juya ta ficcewarta, bata tsaya a ko ina ba, sai falon anan ta gayawa Iyayenta, abun da yake faru. Sannan ta nuna musu zata bawa Mr Mahir, sun ji dadin haka.
Tare da shirya yadda idan Mahir ya saka aka kama Noorh zasu ci dukiyar ta a ruwan sanyi.

Har Noorh ta gama abubuwan ta, tazo ta dauki abincinta ta barsu zaune..
Kwashe kayanta tayi ta rufe su a cikin lokar gadonta. Sannan ta kwanta bayan ta idar da sallah isha.
••
The early morning.
Ta shirya zuwa gurin aikinta, inda aka bata labarun safe, abinda ta fara, shine tabbatar da labarin mutane sab'anin da Mahir ya sallama ba tare da biyan su hakkin su ba, har aka yi hira dasu, sannan ta kuma sake videon cin zarafin ta da yayi a gurin cin abincin. Sannan ta kuma kira ga hukumar kare hakkin dan Adam, da su shigo cikin al'amarin matar, sannan ta kira Sunan Mr Nazzir, a matsayin wanda yana sane Mahir yaƙe aikata wannan abun bai dakatar dashi ba, da ace mata ne toh babu makawa sai inda karfin shi ya ƙare.
Tana gamawa ta fito, tare da mikawa Manager sauran takardun da ta gama karantarwa, cikin b'acin rai yace mata.
"Ke wacce irin sakarya ne? Waya aike ki,.kiran abokin cinikin mu, Mr Nazzir Abu Aswad, kisan gudummawa da ya bamu kuwa? Toh Kiyi a hankali da rayuwar ki, domin duk abinda kike ana kallonki ana bibiyar motsin ki. A matsayin ki na ya mace baki san kome ba sai rashin kunya da mutunci, sam baki da kamun kai, kin zama kamar wata karya ke kullum kina haushi da namiji a tsakiyar hanya."

Ya gaya mata magana sosai, wanda ba kome yaja mata haka ba, sai dan niman ta da yake yi, taki amincewa. Kuma dama itace bata san kudirin su ba. Aiki suke da ita, kuma bata sani ba. Cikin sanyin jiki ta bashi hakuri, sannan ta wuce tare da barin d'akin labaran.

A hankali maganar Badar yake dawo mata, amma dake bata mai da hankali akan shi ba, ta share abin.
--
Acan kamfanin kuwa, Tasleem tana kallon lokacin da Mahir ya wuce, dan haka bayan wani lokaci ta juya tabi bayan shi, yana tsaye tare da juya bayan shi, ta shiga da sallama kamar mumminan gaske, cikin wani yaudararren murya tace mishi.
"Sir!"
"Get out" ya daka mata tsawa,
"Don Allah ka tsaya na sami me b'ata maka suna da na kamfanin ka."

A zafaffe ya juya tare da zuba mata jajjayen Idanun shi, mika mishi wayar tayi, tare da fita daga Office din shi, a hankali yake duba hujjojin da ta haɗa, tun daga ranar da ya ganta, a nan shima sai da ta Rubuta, sannan ta kuma hada wasu bayanai na musamman, can ya kira wayar sakatariyar shi yace a kira mishi Tasleem ya ji daga bakin ta wacece take mishi wannan aikin.

Bayan ya kwashe kome, sannan ya tura a laptop din shi, sauran kuwa ya bar mata, domin yadda yake ganinta zata yi rawan kai. Zata iya bawa wani labarin, dan haka tana shigowa ya shiga tambayarta cikin hikima tare da bata guri ta zauna a gaban shi, aikuwa ta shiga mishi iyayi da rawan kai, tare da bashi labarin abinda ya faru, tare da tabbatar mishi da Noorh ce take mishi wannan zagon kasa.

Murmushi yayi mata tare da cewa.
"Nagode sosai, amma baki bawa wani ba ko?"
"Sir ai ba zan iya bawa wani ba, sai kai domin nafi yarda da kai akan kowa, shi yasa banyi iri ne abinda wasu jahilai suke ba, na bawa wasu sirrin ka."

Murmushi yayi sannan ya kauda kanshi yadda take abin takaici yake bashi tana abu sai kace ma maciji, sam bata da fasali mace sai kace One.
"Ok zaki iya tafiya thanks"
Wani fari tayi da idanunta sannan ta mike tare da barin Office din,tana fita ya kira Nazzir, ya ce yazo maza.

Can kuwa sai gashi yazo a cike ranshi na b'aci, juya mishi da laptop din yana wasa da wani abu a kan table ɗin.
"A'isha Omar Jimeta! Itace ta haɗa wannan bayanan, kuma dole na mata rashin mutunci."

"Me yasa ka dauki zafi da yawa, tiger?" Ya tambaye shi a sanyayye,
Cikin fusata ya mike domin ya kasa rike fushinsa, yana kallon Mahir da hankalin shi kwance.
"Meye nawa da zata min Sharri? Yanzun na gani a labarai wai dani a cikin masu sanya ka aikata duk abinda kake yi."

Dariya ya kunshi, sannan yace mishi.
"Shine kake jin haushinta ko?"
"Ya ba zanji haushi ba? Kai dalla matsa min."
Ya juya zai fita waje.
"Kar ka mata kome! Masu sakata aikin zasu ji da ita, sannnan me yasa mutanen da nake sallama baka basu hakkin su na aiki?"

Cikin wani irin faduwar gaba, ya juya yana kallon Mahir.
"Duk na basu hakkin su, sharri kawai yarinyar take min, kuma."
Mikewa yayi tare da bude frig ya sauko goran drink na wanda aka kona inda ake yin shi, ya mika mishi, buge hannun shi yayi tare da cewa.
"Me zanyi da giya?"
"Kana nufi giya kuke sarrafawa a ma'aikata na?"
"No rai na ne a b'ace, ya amsa tare da fita waje!"
Kallon shi Mahir yayi sannan ya maida daya goran, shima ya bishi.
"Karka mata kome zanji da ita,!"
"Ya wuce ba zan mata kome ba"
--
Tana gama labarun yamma, ta nufi hanyar gida, tana isa ana kawo mata katin gayyata na bude wani babban mall, taga daga cikin masu gabatarwa har da Mr Mahir.

... Tana shiga gidan ta isa d'akin su, tare da ciro kayanta, ta samu an goge mata kome na kan wayar, na laptop din ne da akwai password ɗin, kawai shan jinin jikinta tayi tasan babu me mata haka sai Tasleem, sai ta share batun ta.

••
Washi gari.
Bayan ta taso aikinta ta tsaya, suka gabatar da taron anan ma sai da sukayi fada da Mr Mahir, kamar yadda suka saba, dan har rike su ake, wannan abun ya sani kowa, domin tsakani da Allah, Mahir yake shirin dukarta, itama kuma bakinta bai mutu ba, yace mata.
"Sai na b'atar dake! Sai na shafe tarihinki"
"Ka fadi haka! A gaban yan jarida, ka daure kanka da kanka, zaka sha mamaki sai ka rasa inda zaka saka rayuwarka ba dai Nice zaka b'atar ba? Ni zaka salwantar. Hahhhh ka shirya bawa yan jarida amsar da ta dace."

Sam bai fadi haka saboda ya aikata abinda zai a fada ba, kawai dai ya fadi haka ne dan ya gaya mata zai iya aikatawa, abinka da wanda Hausa bata albarkacin bakin shi ba, dan haka manyan mutane da suke gurin suka yi ta mishi magana akan abinda ya faɗa bai dace, ba a matsayin shugaban kamfanin Hamoud Boualem, shi babba ne, kuma Hasken matasa ne shi...
Sorry Guys....🤨🙄

MAH~NOOR🌹Onde histórias criam vida. Descubra agora