"Kinyi kyan kai!"
Mikewa yayi tare da gyara zaman kayan shi, sannan ya juya tare da tab'a wani abu, kofa ya buɗe hango daki tayi kamar yadda cikin office din ya kasance, fari sosai kome na ciki fari ke, hatta Furniture din ciki, shiga yayi kofar ya rufe kanshi.. kamar zata yi kuka tace.
"Yanzun don Allah ya zanyi da wannan haukar da ya tara min?."

A hankali ta fara, tattara takardun ta fara rubutawa, kamar wasa ta cika shafi biyu. Murmushi tayi tana yi har kusan karfe biyu na rana, mik'ewa tayi tare da fita sallah, tana zuwa ta samu yana zaune, kallon agogon hannun shi yayi, bai ce mata kome ba. Har la'asar sannan ya kuma shigewa dakin, karfe biyar ana tashi ya fito, zai bar Office din yana fita itama ta mike tare da tattara kayan ta barsu a gurin, bai ce mata uffan ba. Kawai abinda ya sani zata ji a jikinta ne, ba dai shi zatawa taurin kai ba.

Haka ya fita, da sauri Escort din shi suka amshi kayan hannun shi, tare da isa gurin motar shi, suka zuba mishi kayan a cikin motar bayan sun bude mishi. Zama yayi tare da kallon inda take tsaya yaga yadda take yarfe hannun ta, alamar hannun yayi tsami.

A ranshi yake cewa, baki yi kome ba, yanzun kika fara, domin sabo zaki fara.
Koda Tasleem ta iso, bata iya magana ba, motar Badar suka shiga, tunda ta zauna take ajiyar zuciya,a saninta tayi ya kai page goma idan bai fi ba, da suka iso gida. Tana shiga wanka ta shiga gasar wuyarta, saboda zaman rubutun da tayi, haka hannunta, sallah al'adar tayi kawai, ta kwanta akan abin sallar. Ciwo kawai hannun yake mata, kamar zata yi kuka, haka take juyawa, Tasleem ana can ana shirya karya.
•• Da dare suna zaune, amma hankalinta bakan hirar Tasleem da Nazzir, wanda sakusan fada ne da rashin kirki, juya baya tayi tare da mik'ewa tayi sallah isha, ko hirar da suke yau basu yi ba, kawai ta Cigaba da kwanciyarta, abinta sai da tayi barci kai ɗaya, sannan ta tashi tayi alola tare da gabatar da nafilla, addu'o'in. Sannan kusan rabin addu'o'in da tayi duk na niman tsari ne daga sharrin Mahir, Allah yayi mata katangar karfe dashi, kar ya bashi sa'ar cutar da ita. Allah ya kare ta daga sharrin sa.

Haka ta jima har ta idar da Addu'ar ta koma gado ta kwanta, washi gari suka tashi da wuri, sannan suka shirya, duk da taga yadda Tasleem take wani cin magani, kamar wacce aka mata wani abu. Har suka fito,sai lokacin suka ga motar Tasleem a can gefe an gyara, amsar key din motar aka yi tare da shiga suka bar gidan.

Lokacin da suka, isa sun same shi zaune da masu tsaron ma'aikatar, kamar ba wani ba. Dauke kai Noorh tayi bata kaunar ta kalli inda yake ma, yana zaune ya harde kafa daya kan daya, da alamun akwai tsiyar da ya shuka.
Domin taga Nazzir yadda yake bashi hakuri, tare da magana kasa kasa, da alamun yana bashi baki ne, dan taga wasu mutane biyar a tsaye hankalin su a tashe, sai hakuri suke bashi. Cikin masifa ya daka musu tsawa.
"Kuyi min shiru! Kai Nazzir kasan yadda kome yake taya zan zuba jari ana salwantar min da dukiyata, kona min kayan aiki. Masu kyau idan ina bukatar su sai nayi odar su daga China, suje na sallame su, kudin su zai shigo musu cikin satin nan."

"Mtsew! Aikin banza aikin wofi." Ta faɗa kasa kasa.
"Ke!" Duk suka tsaya dama Tasleem ta gama tsorata, dan tayi Allah ya isa yakai kwando dubu a zuciyarta, yanzun ta gama tsorata juyawa tayi kamar wacce aka shaketa, tace mishi.
"Sir Noorh ce tayi magana wallahi bani bace,"

Bakin ciki ne ya turnuke shi, bai san lokacin da yayi wata irin, kwallo da kayan ruwan zafi da yake gaban shi ba, dan mutum ne me son coffee, ya tako gabanta.
"Dube ni! Ni sa'an kine? Ki biyo Ni kamfani na, kina min rashin mutunci."
Lek'awa tayi tana duba gefenta kafin ya kalli inda Nazzir yake tace mishi.
"Don Allah da waye wannan yake? Ko dai yana da shafar junnu ne? A Toh idan bai da lafiya gwara a fara duba shi dan mutum shi daya yana magana abin hankalin ba zai dauka ba."
Dariya suka kwashe mishi har Nazzir, haka yake so yaga an sami wanda zai tanka mishi, a wulakanta kimar shi a gaban mutanen da suke ganin shi da kima.

.yaji kunya da shakkar mutane, sabida an sami me tanka mishi, isa da ji da kai ya zube ya zama shine me wannan abun.

Saka takalmin shi yayi ya take mata kafarta, sai da ta saka kara, ya kuma take mata, yana huci yace.
"Yau zaki ga hauka iya ganin idanunki."
Ya faɗa tare da wuccewa Office din shi. Yana shiga ya shiga dukar table din shi, tare da lacce shi da kafar shi, yana huci.
....
"Noorh kinyi abu me kyau, ki Cigaba da abinda kike mishi yadda kowa sai ya tsane shi. Ki gayawa duniya abinda yake miki,"
Cikin azabar zafi tace.
"Jiya yayi kokarin raping dina, yau kuma ban san abinda zai iya min ba"
"What??"
Ya tambaye ta, tare da zaro idanu.
"Wallahi kuwa, domin sai da na amince zanyi Rubutun ya fasa,"
Cikin jimamin karya yace mata.
"Kinga abinda baki sani ba ko? Ana tace miki ni mutumin banza ne, toh bari kiji yan mata irin ki, haka yayi ta raping din su a Office din shi, sannan yana koran su, wasu ma bazan iya gaya miki ba"
"Amma me yasa baku dauki mata ki akan shi ba?" Ta tambaya a dame,
"Sabida babu hujja ke kuma kina da hujjar yakar shi, tare da ganin bayan shi."
Shiru tayi kafin ta mike ba tare da tace mishi kome ba, ya bar gurin shi, murmushin gefen baki yayi sannan yace.
"Duk inda shiga sai na shiga, sai na rusa maka farin cikin ka, sai na maida maka rayuwa majiginar bakin ciki. Sai na hanaka walwala da sukuni."

Sannan ya mike tare da rantsuwa, akan abinda zai aikata.
--- a dararre na shiga ofishin sa, bai d'ago ba bai kuma fasa abinda yake ba, asalima sai ganin A4 da nayi har guda biyar, wai nayi rubutu. Ya watsar da na juya wani ya kuma cirowa.
"Kai wani irin Azzalumin mutum ne? Anya da zuciya a kirjinka? Taya zan yi wannan aikin?"
"Wallahi ko kwana zaki yi sai kinyi,.kuma a tsaye idan ba haka ba zaki sha mamaki."
Juyawa nayi zan naje na bude kofar ya rufe rub.
"Ai kofar da remote control take amfani!"
A hankali na dauki takardan Ni game zuciya, na fara rubuce-rubucen,.kamar ba da gaske na fara, ban san ya akayi ba ko awa biyu banyi ba, bayana ya fara rikewa, hannuna da kafana suka fara rawa, karku manta Mr Mahir Major ne na sojojin ƙasa.

Duk wani muguntar duniya, babu na biyun sojojin ƙasa, tun ina yi zufa kadan kadan, har na shiga diga sosai, kwalla ya jika min nikkab, jikina sai rawa yake, karshe haka ya fita tare da nufar meeting, yana fita ina sake kuka. Har da shasheka, minti arba'in da biyar ya dawo, yana shigowa ina hadi kukar, dake yaji ajiyar zuciyar da nake. Tsayawa yayi a gaba na tare da cewa.
"Ba dai kuka kika yi ba? Toh ance miki rashin kunya abin dad'i ne, mara kunya karamar mara mutunci, mu zuba Ni dake shege ka fasa,"
"Yanzun muka fara" na gaya mishi.
"I like your confidence!"
"Mugu!"
"Cigaba da tsayuwa!"
"Azzalumin kawai"
"Anan zaki tabbata!"
"Allah ya isar min!"
"Dama Ai shi din ishashe sarkin sarakuna ne! Dan haka tun ba a haife ki ba yake da isar shi."

"Allah kaga abinda yayi min, Ubangiji ka bani damar daukar Fansa"
"Duk ranar da kika dauki fansar ki, nayi miki alkawarin kyautar da babu wanda aka tab'a bawa shi a duniya!"
Kukan da take had'iyawa ne ya kwace mata.
"Simple kice min Boss am sorry,"
"Da na kiraka Boss gwara nayi hatsari hakoran da harshe na, narasu har abada."
"Cigaba da rubutu."
Bakin ciki ya sata had'iye Kukan, gashi zaka ji yana muryan kuka, amma zunzurutun taurin kai irin na jinsi biyu da suka yi gamayyar halitta a jininta ya sanya taki accepting din laifinta, Cigaba tayi da aikin
....🤣 Wadannan mutane 🙄🤔 🤦🏽‍♀️ sai kace kaji.....

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now