Hamoud Boualem Family

Start from the beginning
                                    

     Dan kimanin shekaru saba'in idan ka ganshi ba zaka ce ya kai haka ba, tare da matar shi Sahiba, yaran su uku.

          Nazzir shine babba, sai Nurul Sahar, sai kuma  Zoolfa. Suna da mugun ji da kansu, basu cika son mutane suna zuwa gurin Hajiya Maryam ba, toh ya zata yi ita na mutane ce, Hamoud Boualem asalin su yan kasar algeria ne. Wasu damuwa irinta zumunci yasanya Hamoud Boualem ya bar kasar shi ta Haihuwa,

   Ya dawo Naija da zama, lokacin da  yazo ne ya nemi inda zai fara kasuwanci sai ya zabi zaman yola, a can ya hadu da Hajiya Maryam, har suka yi aure.  Ana suka haifi mahir, sannan ya kafa kamfanin shi na soft drink, Sabida yana da asalin babban branch din shi a Kasar shi ta Haihuwa. Wato Algeria.

.... Bayan haihuwa Mahir suka tafi Algeria anan suka samu family house din su ya kuma tarwatsewa, sakamakon matsalar  cikin gidan su, a cikin mutanen da suka bar gidan har da dan uwantar su. Shima ya bar garin biskira. Haka ya dame shi sosai,. Da zai koma ne ya tafi garin bechar inda mahaifiyar shi take aure, ya daukota da kanin shi Barraq Abu Aswad. Mahaifiyar su mai suna.

   Hadiya, tazo ta zauna dasu lokacin Hajiya Maryam tana karatun ta akan lawyer. Haka suka ci-gaba da zama a Yola har matar Barraq ta haihu lokacin Mahir na da shekara biyu har yanzun suna tare da Hajiya Maryam.

       .... A hankali kome na family yake tafiya cikin tsarin Ubangiji, sabida Mr Hamoud Boualem yana bawa kowa damar yayi abinda yake so. Har Mahir da Nazzir suka girma, aka kai su makaranta mafi tsada da kyau wato king Abdul azeez Saudiya. Acan suka fara karatun su har suka kai matakin digiri.

         Anan ne kuma suka raba jaha, domin shi Mahir yana son aikin tsaro, yayinda Nazzir ya zabi kasuwanci. Mahir ya tafi College of militry USA. Inda ya samu degree din shi a fannin binciken sirri, sannan ya kuma sake samun degree na biyu, akan yaki da ta'addanci. Dan haka ya dawowa gida Najeriya hukumar sojojin ƙasar suka dauke shi a shashin sirri.
        
     Amma daga baya ya ajiye aikin bayan wani irin tashin hankali da akayi a ƙasar naija, wanda aka samu fada tsakanin bangarori biyu na ƙasar, yanzun haka ya ajiye aikin baya damuwa da kowa, sai kasuwancin shi da kamfanonin mahaifin shi musamman wadanda suke dakon mai dasu.

      Mahir yana da matukar kirki amma bai da mutunci kasancewar yayi aikin soja, abu kadan yake fusata shi, bai cika hayaniya ba, har yau Mahir yana da mafarkin akan wata mace da suka haɗu. Amma ya manta inda suka haɗu.

      Mutum ne da ya kasance miskili,. Bai da magana amma yasan kan mugunta, domin idan yana gari. Yana da Office a cikin gidan shi, akwai wani a cikin gidan mahaifiyar shi.

       Idan aka mishi abinda bai masa ba, zai iya hana kowani mai aiki  barci a ranar, ya saki kuyi ta aikin da babu. Idan yana barci ba a hayaniya a cikin gidan su ko gidan shi. Atleast dai bai son kwaraniya, shi yasa ya ajiye aikin militry, yace aikin militry bana mutane irin shi bane.

           ......
Sauran Mansion din kuwa, sun hada nashi dana Nazzir. Duk cikin gidajen gidan Mahir yafi na kowa haduwa da haska Mansion din sabida gidan sama ne da fuskar gidan yake kallon taku, sannan Bayan anyi building gidan, amadadin katanga wasu irin Glass me mugun kauri aka saka a jikin gidan Amadadin bango.

           Anyi tsarin gidan farin paint ne, yadda haka falon gidan guda hudu ne, kamar yadda dakunan gidan suka kasance huda uku.
        Falon shi na farko wanda yake sama kayan cikin kujerun falon ba wasu dayawa bane amma gray colour ne, sai dan gurin shakatawa, wanda daga falon kana hangowa, kuma kana hango tekun Lagos. Sannan shima falon yan me dauke da dinning table kujeru guda ukku

      Sai na biyu, shima multicolour ne, amma a kasa yake, sannan akwai littafai, tare da frame na wall, da dinning table, sai yan wasu drower masu shegen kyau na jikin bango wanda aka yi shi daga wood. Akwai yan step da zai haura dakai falon sama. Zuwa bedroom din shi.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now