★★★
2019....

Kar'ar Alarm ce ta tashe mu daga nannauyar barcin da muke, na danna kan Alarm din, cikin jin mugun gajiya na kalli Tasleem, mik'ewa nayi.. tare da ɗaukar towel ɗina, na kalli agogon da yayi kukan sannan nufi ban dakin mu.

     Yau zamu fara aiki da ina aka tura mu service, kasancewar Daddy ya hana a turamu ko ina bautar ƙasa, wai muyi a Yola, hankalin shi zai fi kwanciya idan yana ganin tagwayen shi a tare da shi.
     Kallon ta nayi tana murmushi, kamar yadda ta saba, d'aka mata duka nayi sai da ta tashi zaune tare da zuba min ido, kafin ta tura baƙi.
    Baka ce mai kyau da ita, sai dai doguwa ce Irin mutanen nan da ake kira Muciya da zani, murmushi nayi sannan nace mata."asuba tayi har na dibo ruwan wanka na, saura ke. Mun gama training daga yau sai inda zamu yi Attachment kina nan kina mafarkin kanzon kurege da kika saba.

      Wani irin blush ta bada, tare da lumshe idanunta, dafe goshina nayi tare da wuce ta, tana mafarkin da ta saba.

     Idan da sabo yaci ace na saba da halin Tasleem, na wuce na dauki brush tare da nufar ban daki naje na sille wanka, sannan na fito, ganinta har zuwa lokacin tana zaune. Tana mafarkin da ta saba.
  
Cikin nutsuwa na fita, na shiga shafa mai, ban cika son makeup ba, dan ina da kyau dai-dai gwargwado, Ni fara ce sol kasancewar Mahaifiyata da yar kasan Algeria ce. Mahaifina dan Akko na garin gombe,

  Sannan idan ka kalle ni ina da kiba dai dai misali, sannan ban da Tasleem bana magana da kowa, sabida ban cika son hayaniyar mutane ba, haka Yasaka ake min kallon ina da girman kai.
        Ina da matukar hakuri, bana daukar reni ko wulakancin.

            "Tasleem, bamu da lokaci yau zamu fara aiki da, inda aka tura mu. Kuma kina zaune."
    Tashi tayi a kafitar sannan tace min.
"Noor! Ina son duniyata! Ta zama babba, ina son auren babba mutum me daraja, wanda duk inda na shiga ana ce min Matar wane"
         "Idan kinyi hakuri! KOME DA LOKACIN SA, zaki yi nasara. Kuma ki nemi zab'in Allah, dan ni nafi sha'awan nayi rayuwa ta low class, ban son daukakan duniya, bayi da amfani."

     Murmushi tayi sannan ta shiga wanka. Tasleem da Parent din tq, suna da mugun son kai. Duk abinda zan samu na rayuwa na Tasleem ne. Sannan duk abinda zata samu na tane.  Zai yi wuya ta nasan ta samu domin b'oyewa ake kar na sani, tun tasowar mu suke nuna mana ita ya kamata ta ta sami nasara ba ni ba. Shi yasa sai na koma a rayuwata bana son nasara ko dan na kasance marainiya ce bani da uwa bani da uba.
     My First choice na karatu, Medicine ne. Itama shi ta cika, abin mamaki koda mukayi jamb ta fadi sai ni na samu,  ita kuma bata samu ba, dole aka canza mata course, har dani. Ita aka bata accaunter ni kuma aka bani Mass communication. Ban damu ba, dan na fahimci su kar nayi gaba na barta a baya ne, sai na amshi sakamakon nayi godiya.
      Ni da ita mun taso kome namu iri daya ne, amma a ta bangaren Cigaba na rayuwa nata daban ne, Mommy da Daddy sun koya mata buri, kuma haka ya faru ne sabida kasancewar ni nafita kyau, na fita halittar jiki me kyau, dayawa suna zab'ena a barta, dukda itama ba laifi tana da nata kyan but ta taso da kazamin buri da kishina.

        A gaban mutane zata wofantar da ni, dan kar na samu yabo a gurin mutane, shi yasa ban damu da kwalliya ba, domin idan zamu fita, tare ita zata gama b'ata lokaci. Ni kuma za a azazalamin na fito. Idan na fito suka ga nafita kyau su tsiro min da damuwa har sai nayi zuciya nace ta tafi kawai.

       Na hakura, abin yana mugun min ciwo, sannan sun basu kyautatta min ba, su kuma basu barni na koma gurin dangin Mahaifiyata ba.

               Koda muka shiga makaranta ma, haka take wulakantani, amma idan tana son koyan wani abu na karatu, haka zata saka ni a gaba da magiya, haka zan koya mata tana tashi zata nuna min itace ta iya ni ce me koyan. Dan haka na daina koya mata. Ina da mugun zuciya shi yasa suke d'aga min kafa.

            Dan kokari nafita mai da hankali na akan karatu, ita kuma tayi kwalliya ta sha gaye, kowa ya san itace wata. Shi yasa ban damu da ita ba, har yau ita ke bina. Koda muka shiga aji na biyu a jami'a, sai Mommy ta hanani yawo da gyale, suka sani ina yawo da hijab, sabida wai kar ana gani na, aki kula yar su. Ni ina kyan da yake dakushe na yar su, na hakuri idan ta sami miji sai na cigaba da yawo ba hijab da niffab. Haka ya sani hakura da saka gyale, duk kwalliyar da zanyi da hijab ne. Amma a haka ban tsira ba, idan nayi saurayi sunyi ta kunshe shi kenan, har sai na rabu dashi. Ita kuma ta fara soyayya dashi.

    Wani lokacin kuma ita ke kore min su, nayi samaruka  dayawa amma ana kore min su, sabida ita bata samu ba, ni da na samu kuma an kore su. Bawai farin jini na fita ba, kawai ita tana duba Wanda ya kasan best Man in earth, ko nace world wanda yake da good career, rich man wanda ya maida hawa Bugatti kamar hawa mashin. Wanda zai yi mata kyautar Mansion a cikin Unguwar maitama na Abuja ko a lekki. Ko banana island ko a  Tobago island U.S. Mutumin da ya shirya wa rayuwar shi Luxury life, yadda zasu shiga su fita. Yana da gidaje a kasashen Turai da wasu yanki na Afrika, wannan shine mafarkin Tasleem Elhussain Jimeta....
Hey guys Am back da wani story! Don Allah idan ba zaka karanta ba, karka damu kanka Please And Please idan baki yi karki zage ni, don Allah bana son tashin hankali, kamar yadda wasu suka min A KOME DA LOKACIN SA. Sannan zaku yi hakuri zan rinka posting din duk bayan Four days insha Allah.
Idan kuma kika yi voting da comments insha Allah zan mai dashi After few two days...
#Vote
#Comments
#Share🤩😍😘

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now