1

285 19 3
                                    

Tana kwance a kan gadonta da novel a hannunta 'Little Women' tayi zurfi wajan karantawa se taji ana kwankwasa mata kofa dan haka setaja tsaki ta mike daga kwanciyan da tayi ta jawo hijab dinta ta kama hanyan kofan tana sakawa.
"Waye?" Ta tambaya tana tsayawa a bakin kofan "Nine, bread din na kawo maki" Mallam Musa gateman dinsu ya amsa ta daya gefan dan haka seta bude kofan "Harka dawo?" ta tambaya tana amsa "Nagode" Seya miko mata chanjin "A'a ka rike kawai kasha pure water nagode"
"Nagode, Allah saka da alkairi, Allah kuma yayi albarka!" ya fara gero mata addu'oi "Amiiin Mallam Musa seda safe". "Allah tashemu lafiya!" seta ja kofan ta kulle sannan ta ajiye bread din akan study table dinta na kusa da kofan sannan ta cire hijab din ta kuma kan gadon ta kwanta tana jawo littafin ta cigaba da karatu se wayanta ya fara ringing dan haka seta sake ja tsaki ta zaroshi a karkashin pillow ta se taga Zahrah ce sister ta dan haka ba tareda bata lokaci ba ta dauka tana sakawa a kunne.
"Hello girl? Whats up?" Mait ta tamabaya tana kwantawa sosai tana kallon ceiling din dakin "Nothing much, are you still coming?" "Insha Allah yau nayi niyan tahuwa amma yanzin se gobe da safe insha Allah zan shiga school nayi submitting assignment yace se 12am dole zani dan wulakanci maimakon kawai na kai mashi by 8am sena kamu hanya daga nan".
"Ae haka duk suke da bakin muguntansu, naga picture da kika min sending ta whatsApp jiya Khaleel da waye?" Yamutse fuska tayi "I have no idea, it seems they are very close these days her whole dressing was F9, wallah as in kwata-kwata yarinyan batayi ba to cut the story short she is old fashioned!" Mait ta gama magana ranta a bace. "And what is it you are worried about? You can't possibly compare yourself with her, she is a slut for crying out loud! Ki dena damuwa da ita, ki nuna masu ma bakisan sunsan juna ba idan ya gaji da kanshi ze gayan maki wacece ita a wajanshi amma yanzin idan kika nuna kin damu har kina wani abu wai shi nan kishi tou wallah he will take advantage of that am telling you" Zahrah tayi magana magana, yadda take magana bazama a taba cewa itace kanwar ba

Murmushi Mait tayi ta daya gefan "What am i gonna do without you? Bansan yadda rayuwana ze kuma ba idan baki kusa dani Zahrah....." Kallon wayan tayi seta maida kunnenta "Ina zuwa Mama tana kirana maybe taji labarin zan dawo ne!'
"Tab tou Allah yasa kar tace kiyi zamanki dan naji harta fara complaning yawonki a titi ya fara yawa!"
"Na shiga uku, bazan ma dauka wayan ba gabadaya" Dariya Zahrah tayi "Babu ruwana fa kartaci kaniya na tace na kawo maki gulma amma tace gara kije gidan Mammi tunda Mid-Semester break ne idan yaso in kika gama exams seki dawo gida, haka naji suna shawara ita da Baba jiya da nake gayan mata an baku Mid-Semester break"
"Ya Allah, amma Mama tasan banason zuwa gidan nan wallah kwata-kwata.....wallah na tsana Tahir din nan itama ta sani! Akan naje gidan gwara nayi zamana a dakina har'a gama Mid-Semester ya fiye min kwanciyan hankali wallah!" Tana magana kaman zata fashe da kuka dan takaici. "Kema kinsan Mama bazata taba yarda ba, taya ma ta yarda kika kuma off campuss? Dakyar fa, gara kawai ki saka ma kanki ruwan sanyi ki hakura kije gidan tunda kwana biyar ne kawai nan da nan zaki kuma school din! Besides sunason kije gidan ne dan fadan da kuke da Tahir din wai maybe kafin ki koma zaku dena... Zaku zama besties by then" Ta gama magana trying to mock her.
Bude dakin Zahrah akayi aka shigo seta juya taga wanda ya shigo sega Mama da waya a hannunta "Hala da Mait kike waya?" ta gama magana tana isowa gabanta se Zahrah ta mike zaune tana kallonta ita kuma Mait ta daya gefan tana jin muryan Mama se tayi saurin cewa "Kice mata bani bace!" amma se Zahrah ta kasa magana tana kallon fuskan mahaifiyarsu kawai dan haka Mama ta saka hannu ta amsa wayan daga kunneta ta kalla screen din seta galla ma Zahrah harara sannan ta saka wayan a kunne.
"Dan ban isa ba shine dan kina waya da Zahrah na kiraki har sau biyu bankai kiyi cutting wayan ki dauka nawa ba koh Mait?" Mikewa Mait tayi daga kwanciyan seta fara in'ina ta kasa magana "Don't dare lie to me, i called to tell you this.. karki kuskura ki kamo hanya gobe kiyi zamanki a garin, bakuda nisa da Yaya dan haka ki shiga taxi ya kaiki har gidan...."
"Amma Mama....". "Am not asking you this is a commad Mait and that's final idan na isa dake kenan idan kuma bakiji ba shikenan zaki iya abunda kikeso!" DING! Ta kashe call din, tsayawa tayi tana kallon wayan se kuma tayi wulli dashi kan gado amma sedaya kai kasa seta dukar da kanta ta fashe da kuka, dan idan akwai wanda ta tsana a duniyan nan tou ya biyo bayan Tahir tun suna yara da kaman abun arziki suna son junansu amma daga baya komai ya baci har yau ba'asan dalilin da suka tsana junansu ba, they practically hate each others presence!

Aure Ko Ajali?जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें