TARKON MAQIYA

24 1 0
                                    

Ranar wata Sunday muna zaune ni da qawata zulaihat muna rabuta wani Assignment, din chemistry,jinayi anzunguri qafata da sauri na dago kaina,zulaihat kenan akwai son gulma;nima hankalina yakarkata kan abinda take son nunamin.Tafiya take kamar me tausayin qasa,se famar lallauyewa take tana tafe tana famar tauna jikake qas qas......na dan mintsini zulaihat,nace; "ke malama;sa idon ya isa haka, en kuma kika bari ta qaraso tafahimci kallon muna furci kike mata kekika sani".Da murmushinta taqaraso inda muke, tare da fadin cewa; "qanwata assignment kukene?" nace; "wallahi kuwa aunty rabi; gashinan muna fama". ta danjima muna hira sananan ta tashi tanufi dakinsu, tana juya baya zulaihat ta tabe baki tace; tabdijan "gaskiya Aisha yayan nan naki yana da jan aiki a gabansa, da sauri na kalleta cikin rashin fahimta,ta tintsire da dariya tace;irin wannan lallauyewa haka,mace ba kuzari". Nace; "ke banfa fahimtaba; wani yayannawa?".Tace; " ya mustafa mana;ke duk bidirinnan da ake baki saniba?". Nace mata "yanzu dai zanfara ji abakinki". Tace; " dan Allah da gaske Aisha bakisan abinda ke tsakanin ya mustafa da aunty rabi ba?".Nace; "seriously wallahi bansani". Tace;"tabdijan aikuwa dak 'yan group dinsu sun san cewa shi zata aura, tasake tintsirwa da dariya, nai tsaki "mits ke wallahi nonsense ce; baki da aiki se shirme na dan bangajeta da kafadata,tamike atsaye;tadora dan yatsanta a kan kirjinta, tayi juyi tace; "kamarni yarinya me aji kikalleni kicemin nonsense",nace " to karya nayi ina fada ina dari, zulaihat kenan inasan zama da zulaihat kasancewarta mutum me barkwanci, kuma me himma awajan karatu,shiyasama tin farkon zuwana school din jininmu yahadu,bani dawata qawa kuma aminiya sama da zulaihat a duk fadin school din nan.

Zulaihat tace; "to ai shikenan tinda haka kikace,bake bajin wani bayani". Na janyota nace; " yi hakuri zuuly".ta zauna tace; "Aisha wallahi ba zancan wasa; akan abinda zan fada miki aikinsan husna ko 'yar class dimmu?" Nace "nasanta". Tace; " yayarta habiba ba group dinsu daya da aunty rabiba, to aunty habiban ce take tambayata wai da gaske ne yayan Aisha aunty rabi zata aura?". Nikuwa nacemata;ban saniba.Aisha tace; "tabdijan yaushe ya mustafan ya ganta haryace yana sonta tana cikin garin kazaure yana kano, en banda a cikin makarantar nan en yazo take zuwa ta gashsheshi,lallai iska na wahalar da me kayan kara, en de ya mustafane zata wahala shi baya kula 'yammata,karatune a gabansa". Zulaihat tace; "yanzu dai abinda za ayi tinda shi yayan namu be saniba, ke yakama ki nemamata fada a cikin zuciyarsa,kodan mutuncin da take miki". Nace; "kema ai zaki iya nema mata". Tace; "au haka kikace; "aikuwa zaki sha mamaki,tana fada tana murmushin gulma, nace; "me ya mustafa ze da ita?" Tace; "au dan tace tanasan yayannamu,meye lefinta?gata fara doguwa bata da wata makusa a jikinta,tana tafe tana rausaya". Wata junior dimmu muka hango tanufo inda muke da alama aunty rabi ce ta aikota,zulaihat Tace; "Aisha ga matar yayafa taturo a kawomana abin dadi, gaskiyafa munacin batin ma tarnan, tatintsire da dariya;dai dai lokacin yarinyar takaraso, " Wai gashi inji aunty rabi".zulaihat ce ta karba tare da fadin kicemata angode.Nakalli zulaihat nace; "zulaihat dasa idon jaraba kike kinsawa aunty rabi ido da yawa, ya akayi kikasan mu za akawowa?" Tace; "saboda matar yaya nace shiyasa nasa mata ido".

To hakadai rayuwarmu tacigaba da tafiya acikin makaranta,har lokacin jarabawa yazo,munzana jarabawarmu ta zangon karshe a s.s one,daga itakuma en mundawo zamushiga s.s two.

Ayau asabar ake rufe duk wasu makarantun kwana,bayan kammala, jarabawa,karfe 10:00 am ya mustafa ya karaso cikin makarantarmu, da gudu na qarasa ina cewa; "oyoyo oyoyo,ya mustafa". Yana tsaye abakin motarsa ya harde hannayensa biyu akan kirjinsa,fuskarsa dauke da murmushi. Motar mu nashirin tashi sega yaya rabi ta qaraso cikin sauri ta dan leqo da kanta, "qanwata se tafiya kenan?" Nace; "wallahi kuwa aunty rabi" fuskata dauke da murna da dokin zuwa gida, tace; da ya mustafa barka da safiya". yace mata; "barkadai" batare da ya kalli inda takeba.Ina kallonta ta wutsiyar ido ta kurawa ya mustafa ido,se alokacin na sake tabbatar da abinda zulaihat ta fadamin, se yanzu na fahimci cewar Ashe zuwan da take duk san da ya mustafa yazo ta gshsheshi,Ashe dawata manufa aranta gashi ku shi bama kula yake da itaba,zulaihat ce kadai wacce ya mustafa yasanta,nace tab; amma aunty rabi nada aiki a gabanta wannan miskilin yayan nawane ze saurareta, dariyace takusa kwacemin nai sauri na maidata ciki.Mun dauhanya,munatafe ahanya muna hirarmu ta tsakanin 'yan,uwa,haryake gayamin cewa saura sati biyu bikin yaya sani, cikin zumudi da doki nace; "da ummi din za,ayi ko ya canja wata?".Yace; Ita dince dai". Nace; "ya kyauta kuwa". Yace "dakuma ba ita bace be kyauta ba kenan?" Nace; "bawai haka nake nufiba,kasan ummi taso yaya sani duk da irin abinda yake mata,gata da nutsuwa ga hakuri ni wallahi halayentane suke burgeni,shiyasa nakesan yaya sani ya aureta". Ya mustafa yace; " hakane kema haka kike harma kinfita".Nayi wani dam murmushi; me dauke da jindadin yabon da akaimin, tare da fadin cewa;A,a yaya mustafa banda san kai dan kaga ni yar,u warkace". Yace; to bahakambane?". Cikin nutsuwa ya mustafa yake tuqi; komai nasa anitse yake yi,sannu sannu; muna tafe munahira wani lokaci
n muyi shiru,har muka qaraso kano,ba mu dau wani lokaci da shigowa cikin garin kano ba, muka isa gida.

Muna zaune a palo da umma;takalleni tace dani; "Aisha amma wannan zuwan kinrame,kokinyi rashin lafiyane?" Nace; "A,a umma karatune;na de danyi zazzabi na kwana biyu kuma shima farkon komawatane".Umma tace; "to ai gwara ki dage; dan kinsan babu abinda Alhaji yake so irin yaga kimmai da hankalinki wajan karatu.Amma kirika yiwa qawarnan taki nasiha rashin san karatun nata yayi yawa,wannan hutum bata koma makarantaba, yayanki yace;yana yawan ganinta ita da wannan yaron amota".
Nace; " umma shima dai yaya da saka ido yake,yasani ko dan uwantane".Umma tace; "ba dan,uwantabane;ya fadamin ko dan inane,kuma ai dolane yasa mata ido yau ko bawata abota a tsakanin ke da ita indai ana zaman mutunci da iyayenta ai dole ka taya mutum kula da tarbiyar dansa,yarin yarnan tin tana j.s one mahaifiyarta tayi sakaci da tarbiyarta, nawa hafsa take sunbarta tana kula samari, har anazuwa daukarta a mota Allah dai yashirya.


TARKON MAQIYAWhere stories live. Discover now