TARKON MAQIYA

67 4 0
                                    

"Ni sunana Aisha;mahaifana su nansa Alhaji garba;mahaifiyata sunanta Hajiya fatima;amma muna kiranta da umma ma haifinmu kuma muna kiransa da Alhaji kamar yadda mukaji ma haifiyarmu na kiransa da shi mu biyu ne agurin mahaifammu dani da yayana ibrahim.

Mahaifimmu Alhaji garba mutumne dan asalin jihar kano suna zaune acikin unguwar nan da ake mata laqabi da unguwar alasawa wato qoqi,gidansu babban gidane gidan malamai;sunan mahaifinsa malam haruna;mahaifina shine qarami a dakinsu sai qannansa wanda suke 'yan;uba mazabiyu mata uku.

Mahaifiyata kuma 'yar;asalin unguwar jakara ce;sunan mahaifinta malam musa,mahaifinta ya dauketa yabawa babana; saboda amintakar dake tsakaninsu da kakana baban babana.mahaifina beyi wani zurfin ilimiba lokacin daya auri mahaifiyata,yana gama secondary school akamai aure,lokacin itakuma mahaifiyata tagama primary.

Sana ar gidansu babana awannan lokacin itace se da tasoshi da kumbuna,mahaifina yacigaba dazuwa kasuwa bayan ya kammala makaranta,lokacin da result dinsa yafito yaje yasami mahaifina akan zancen zai koma karatu,mahaifina yanuna qin amincewarsa yace; "wannan karatunma dakayi ya isa ka hakura haka,a cewar mahaifinsa;in dai yafara karatu ba zai zauna a kasuwaba shikuma yafiso 'ya 'yansa sunemi nakansu basu dogara da aikin gwamnatiba, dole mahaifina yahaqura.

Dashekara ta zagayo yasake zuwa wajan mahaifinsa akan zancan komawa makaranta,abinda ya fadamai abaya shi yasake mai mai tamai,se da mahaifina yayi ta lallabashi yace mai hakan ba zai hanashi zuwa kasuwaba,kuma ya nunamai cewar karatun zai taimakamai wajan harkar kasuwancinsa,sannan ya yadda.

Mahaifina ya samu admission a;(b.u.k),lokacin yayana ibrahim yanada shekara biyu aduniya,nikuma mahaifiyarmu tana dauke da tsohon cikina,sati daya da samun admission din mahaifina mahaifiyata ta haifo san taleliyar budurwarta kar kaso kaga farinciki da murna awajan mahaifan Aisha.

Shekarata daya aduniya;shikuma lokacin yayana ibrahim yana da shekaru uku aduniya,aka sakashi a makaranta lokacin mahaifimmu yana level two.haka dai rayuwarmu tacigaba da tafiya da mahaifammu cikin farinciki da kwanciyar hankali,inada shekaru uku aduniya aka kaini makaranta shikuma mahaifina suna gab da kammala makaranta yayana ibrahim yana primary one;nikuma ina nursery one,tindaga kaina mahaifana basu qara samun haihuwaba,gata kam muna ganin gata;kasancewar mu biyu mahaifammu suka mallaka aduniya,amma duk dahaka baisa sun batamuba tarbiya kam sum bamu tarbiya,mahaifimmu mutumne mesan 'ya'yansa suyi zurfin ilmi,saboda haka be damuba ko nawa ze kashe wajan ilmummu,yadoramu akan turba me kyau;tarbiyarmu tare da bamu ingantaccen ilmin islama da na zamani,rufin asiri dai dai gwar gwado Allah yayimana shi

Mahaifimmu ya kammal karatu;bayan shekaru biyu da kammalawar sane;ya shiga fafutukar Neman ai ki;be sha wahalaba ya samu aiki a ma aikatar buga jaridu.

Ina primary six mahaifimmu ya gina gida a goron dutse, gidan me dauke da babban Palo daya wanda yake dauke da bedroom guda uku ko wanne da toilet acikinsa.Mundawo gidammu na goron dutse;inda muka shiga wata sabuwar islamiya;Allah ya hadani da wata qawa wacce jininmu ya hadu da it;dayake ita gidansu akusa da makarantar yake duk sanda zantafi sai nabiyamata,idan kuwa har na makara ban biyamataba ita zaka ganta tazo,har 'yammakarantar suna cemana hassana da Usainada dayake dukkammu sirarane kusan yanayin qirarmu daya,se dai ita hafsa tafini dan tsayi kadan,kuma ita tana da tsiwa;nikuwa ina da haquri,gidan da take ba gidan babantabane mijin Babar tane,mahaifinta ya mutu tun tana qarama,se dai ya dauketa kamar shi ya haifeta,yana kuma qoqari wajan yimata tarbiya,se dai mahaifiyata ta shagwabata bata san laifinta duk da tana da qanne amma kamar ita ka dai ce 'ya agidan shiyasa hafsa take shagwabarta yadda ta gadama; saudayawa inai mata magana akan wasu halaye da takeyi se tace; "to in banyiba wa zaiyi;karfa kimanta nice 'yarfari agidammu". Nikuwa se nace da ita " to ai koni danake auta bani da qanne bana haka" se tace; "to ai ke ba asanki agidanku". Hmmmm!quruciya idan tafadi haka se raina ya sosu; nariqa ganin kamar ma ganarta gaskiyace. Haka qawancanmu yacigaba da tafiya da hafsa muna qara shaquwa.






TARKON MAQIYAWhere stories live. Discover now