_WASHEGARI_

  
        K'arfe shida na sassafiyar ranar maman amir na kwance saman gadonta,tun bayan data idar da sallar asuba bata koma ba,idanunta biyu sai azkar da takeyi wanda idan tagama saita sake dauko wani.

       Daga bakin uwar dakin nata taji sallamar ahmad,kamar yadda ta koyar musu shigo mata daki sai sun tsaya sunyi sallama tabasu izini,kai ta daga ta amsa masa sallamar sannan yashigo,ya gidata duk da qananun shekarunsa ta amsa
"Umma,mama batayi mana wankan ba,kuma lokacin makaranta yana qurewa" shuru tadanyi,al'adarsu shine duk wadda keda girki ita zatawa qananun wanka sannan tashirya musu abinci naci dana tafiya makaranta,tunda taga haka tasancewa lallai jiyan anyi bacin raine ita da baban amir
"Shikenan,bari na taso nayi muku,duba min kettle din idan da akwai ruwa kazo ka gayamin".

      Dai dai lokacin da yake duba kettle din abban nasu yashigo
"me kake anan?ina shirin makarantar taku?"
"Umma ce tace na duba ko akwai ruwa a ciki
" ba'ayi ma wankan ba kenan?"kai kawai yaron ya daga,sosai yaji ranshi yabaci,wato shi zata nunama iyakarshi kenan?,a fusace ya qarasa qofar dakin nata ya yaye labulen yashiga.

      Tana zaune gefan gadonta tana baiwa ummi nono,idanun nan a kumbure hakama fuskarta,gaba daya jin duniyar take ta juya mata baya,batajin dadin komai,kamar tafita tabar mishi gidan haka takeji,jiya kwana tayi kuka,har sanda mmn amir tafito ta daura alwalarta ta ka'ida takoma daki duk tana jinta.

      "Wadan nan yaran?,wa kika barwasu?,waye zai musu wanka?"wani kallo ta dago ta watsa masa
" oho,kaje ka kira wancan tantiriyar da zaka auro tayi musu,tunda mu bamu isar maka ba,kaga gwara mu zame hannuwanmu ita tazo tayi abinda mu muka kasa ko bamu dashi"yana sane yasaki murmushi
"Me kike ci na baka na zuba?,tana nan zuwa kuma zatayin,amma a yanzun dole ki tashi kiyi kafin nata lokacin" sosai maganar tashi tasake bata mata rai ta kuma dugunzumata,wato babu abinda zai fasa kenan gameda abinda ya niyyata,har yana ma mayar mata da magana,nan fa sa'insa ta kaure tsakaninsu,kowanne ranshi yabaci yasoma maidawa dan uwanshi da magana.

        Dai dai lokacin da mmn amir tafito tsakar gidan don hada kan yaran tayi musu wanka taji tashin muryoyinsu,gefe daya amir na tsaye fuskarsa cikin damuwa shida ahmad,kada yaran tayi dakinta sannan ta fada dakin mmn ummin
"Haba haba baban amir,bai kamata bafa,kuna abu kaman yara?,duk kunsa hankalin yara yayi kanku?,kiyi shuru mmn ummi mana haba"
"Kinga ba abinda yashafeki,ki qyaleni dashi wallahi,duk wani take takensa na gama ganeshi,tunda ke baki iya qwatarwa kanki 'yanci ki barni nina qwaci 'yancina"
"Don Allah kiyi shuru mmn ummi,haba mana"
"Qyaleta halima,barta tayi,dani take zancan na rantse da girman Allah,tunda aka tada zancan nan kin hana kowa hutawa?,saikace ke daya ce macw cikin gidan nan?,to kiyi duk haukar da zakiyi ki gama,aurene dai babu fashi sai nayishi"
"Ka fada duk abinda kakeso mana jibril,ai namiji kake,batulu,namiji ai dama hankaka ne,gabanka fari bayanka baqi,ka manta lokacin daka dinga daukarmin qawuran bayanni babu wata?,kamanta sanda kake neman aurena ido rufe kanason nashigo gidanka na haska maka shi na zamemaka fitila saboda gidan ya maka duhu acewarka a sannan?,shine zakayimin butulci a yanzu?"duk ya tuna,ya tuna komai,nauyi da kunyar mmn amir suka dabaibayeshi,gashi da alama mmn ummin tonon silili takeson masa,da sake tada husuma,tanasone ya rasa kwanciyar hankali da biyayyar da yake samu wajen haliman kenan?
"kinga maryam,tunda ke baki da mutunci,bakisan darajar mijinki ba to xama babu dole,ki tattara ya naki ya naki ki tafi,don bazan zauna kina haddasamin bala'i da masifa ba tun yanzu"
"Ashasha,haba baban amir haba?,wannan ma aiba zance bane" inji mmn amir duk ranta a jagule,baiko sauraretaba yafice abinsa,don tabarmar kunya yakeso ya nade dama da hauka kada ya baro wani zance daya shafi tsakaninsa da mmn amir din.

        Kuka sosai mmn ummin take,ta nemi gefan kujera taxauna tana ci gaba da kukanta,amir ta qwalawa kira tace yayiwa 'yan uwan nasa wanka,ya saka musu unifoarm tan nan fitowa,sannan ta sake maida hankalinta ga mmn ummi
"Kinga irinta ko?,kinga irin abinda nake gaya miki,akan wata can a waje da batama kai ga shigowa ba har yanzu zaki girgide aurenki,ki fita kibar yaranki wanda baki da yaqini ko tabbacin yadda rayuwarsu zata kasance,yanzu wa gari ya waya?" Itadai batace komai ba sai kuka da take faman sheqa,mamaki duk ya cikata tana tuna soyayyar da suka zuba ita da baban amir,ko a mafarki bata taba tsammatar irin haka zata faru ba,shuru ya ratsa dakin kafin mmn amir tamiqe tana cewa
"Ba inda zaki,ina zuwa" ta juya tafice daga dakin da niyyar baiwa baban amir baki,saidai koda taje dakin nashi bainan,ahmad ya gaya mata yafita,saboda haka ta sauya akalar tata zuwa dakin girki ta dorawa yaran ruwan tea,tanayi tana tunani cikin ranta.

       ******************

"Haba don Allah dear,nifa banason ka dinga bata ranka a banza a wofi,yanzu kamar kai ace kana teburin me shayi wannan ai zubarmin da mutunci kawai kayi" jim tayi ma wasu mintina sannan tace
"Aini wallahi banga wani abu da xakayimin da har zai kaimu ga haka bama,nidai don Allah ka koma gida koka qaraso nan gidam anty luba na hada maka break,tunda su duka basu damu dakai ba nina damu dakai" sake shuru tayi kafin daga bisani tace
"Toh shikenan,i love you" daga haka ta aje wayar tana murmushi
"Uhmmm,rufaida kenan,ke naga ko a jikinki ma,da aketa jiye miki shiga tsakiyar mata biyu" dariya tasaki kafin ta tabe baki
"Mata biyu ko muna mata,nifa wallahi anty ko a jikina,wadan nan niban daukesu a bakin komai ba,kada madai uwar gidan nan tashi taji labari,wadda ko isasheshen ilim boko bata da,yadda kikasan matar ladar noma,gwara gwara ma ta biyun itace kawai nakega tafi fada a wajensa fiye data farkon,haba anty,me zanji,kamata?,nida nake da karatu har matakin degree dame zasu tsoratani?,wancan mai kwalin diploma din ko dayar da banda kwalin secondry bata da komai?,wucenan wallahi"
"K'nnnn,to ai shikenan,yanzu yaushe zaki shiga kasuwar?" Dan shuru tayi sannan tace
"Ina tunanin anjima kadan,don akwai wasu magunguna da zan siyo wanda yakamata ace nashasu tun last week amma ban samesu ba,to tayimin waya ta kawo nazo na amsa" baki anty luba ta kama tana dariya
"Lallai rufaida,kurman tanadi kawai akewa auren nan" fari tayi da idanu cikin jin dadi
"Kedai bari kawai anty,burina kawai nazama tafisu,duk da yanzun ma nasan tafisu dince" dariya tayi ta juya tafice tana cewa
"Idan kin tashi tafiyar kimin magana inada saqo"
"Tohm" ta amsa mata tana maida kanta tasake gyara kwanciyarta,tanajin dadin yadda take juya jibril son ranta,kamar sitiyari a hannun driver ba tare da wata matsala ba,hakanan ba tare data nemi komai ta rasa ba.

HANGEN DALA ba shiga birni baWhere stories live. Discover now