BABI NA BIYU

3.5K 358 6
                                    

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA* 👁️‍🗨️👁️‍🗨️
    _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*BABI NA BIYU*

       Bakwai da rabi na dare bayan sun gama sallar isha'i,tana tsakiyar yaran suna aikin gida da aka basu a islamiyya,yaranta ne guda hudu,amir,ahmad,hanifa da rabi'a,sai yaran mmn ummi guda biyu mubarak da usman,wanda da can baya sai da aka kai ruwa rana kan donme mmn ummin zata dinga yiwa yaran aikin makaranta?,ko cewa akayi itadin bata iyaba ko bata da karatun,saida suka kai ruwa rana ita da baban amir kafin ta sauko ta haqura.

      Tana daga gefe tana kallonsu,hannunta daya saman cikinta wanda yafara nauyi,kadan kadan tunaninta na tafiya kan zuwan hafsat shekaran jiya gidan,wanda hakan yasake sawa mmn ummin takumsa sauyawa,har ita kanta tasake sauya mata,dan hadin kan da rabarta da take tasake janyewa,wanda ita ko kadan bai mata dadi ba,tasani cewa dole sai sun wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu sannan koma wacece xata shigo daga baya itama tayi koyi dasu.

       Sallamar baban amir ita ta katse mata tunaninta,suka hada idanu sanda yaran ke rige rigen isa gareshi su rungumeshi gami dayi masa sannu da zuwa,ya qaraso dakin yanaji da sannu da zuwan yaran,tayi qoqarin qaqaro murmushi saman fuskarta tana masa sannu da zuwa,amsa mata yayi yana nazartarta,yanajin tausayi tausayinta yana kamashi,haliman taci sunanta qwarai shi kansa yasan da hakan,komai Allah shike tsarawa dan adam shi,auren maryam na cikin qaddararsa,haka rufaida da yakejin sonta cikin jikinsa,hakanan yana jin cewa tayi dai dai dashi ta kuma dace da ra'ayinsa,banda hakan babu abinda halima mmn amir tarasa,wanda daa a baya baisan da hakan ba,kafin ya auri maryam ganin gazawar haliman yake,gani yake kaman nata iya komai ba,akwai abubuwa da yawa da bata iya masashi wanda yake hasashen samunsa gurin wata macen,ashe Allah ya tsara masa auren maryam ne don ya fidda qima da darajat haliman a idanunsa,sai bayan ya auri maryma ne ya tabbatar haliman ba kayan banza bace,wannan dalili yasa yake matuqar ganin qimarta da qoqarin kyutata mata,gefe guda kuma yanajin kunya da nauyin abubuwan daya ringa aikata mata lokacin da idanunsa suka rufe yana neman auren maryam,wanda yayi imanin cikin kawaici da yakana ta halima haryau wani abun bata gayawa maryam shidin ya mata ba lokacin neman aurenta,sai gashi ayanxu yana samun sassauci da sauqi daga wajen haliman fiye da maryam,wadda ta bazawa idanunta kwalli,takuma shafawa fuskarta toka ta fitittike kamar basu taba wani abu soyayya ba kan auren da zai qara
"Sannu da zuww" haliman ta katse masa tunaninsa,ajiyar zuciya yasaki a boye
"Yauwa halima,kece da sannu,ya nauyin jikin?" Ya qarasa fada yana bude ledar daya shigo da tsarabar da yayiwa yaran nashi yasoma raba musu,murmushi kawai tasaki
"Alhmdlh" ta fada kawai a  taqaice,sai daya gama rabawa yaran duka tana zaune tana kallonsu sannan yacewa amir
"Jeka kiramin antynku,banji motsinta ba" aje kayan hannunsa yaron yayi yafita kiran kamar yadda ya umarceshi.

      Minti biyu amir din yadawo
"Abba,tace ba zata iya tasowa ba batajin dadi"
"Kace magana zanyi dasu,tazo injini" dakatar dasu mmn amir tayi
"A'ah,tunda bazata iya tasowa ba ka taddata can mana,yaukam batajin dadi sosai don tun daxun data gama aikima tana daki kwance" jim bban amir yayi,don yana tantamar hakan,don lokacin dayashigo tsakar gidan yana ganin sanda tashige dakinta abunta,ba tare data kula da sallamar da yakeyi ba,amma yasan mmn amir din taui hakane saboda akaucewa idanun yaran,saboda haka yace
"Shikenan,in zaki iya tasowa ki sameni a dakin nata" yafada yana miqewa yadauki manyan ledojin yafice.

        Sai data basu wasu mintuna sannan ta yunqura tamiqe tabi bayanshi
"Ai dama ko bakayi hakan ba nasani ba wani sona ko damuwa kayi dani ba,ta yaya ranar girkina zaka wani shige dakinta kuma ka aika wai naxo.....to wallahi bbn amir ni bazan dauki wannan ba,tun yanxu wallahi tallahi donma kasani" duk abinda take fada cikin kunnenta suka fada,amma sai tayi kaman batajiba tayi sallama tashiga,sallamar tata tasa bbn amir din bai maida mata amsa ba,saita samu waje tazauna tana yiwa mmn ummin sannu da jiki,zama yayi yasoma bude ledojin yafito dakayan ciki,yayin da take tsaye har yanzu taqi zama
"Gashinan,kayan fadar kishiyane,kowacce saita dauki leda daya" jiki a sanyaye mmn amir ta sa hannu tadauki leda daya tana cewa
"An gode,Allah ya amfana" tana daga tsaye tanajin kaman zata fashe da kuka,wani mugun kishi yana ratsata,wato dai da gaske yake bazai fasa din ba kenan,kai ta gyada cikin fada da bala'i tace
"Tabdijan,duk wani rashin adalcinka muraran yafito wallahi jibril,ka narkawa amarya kaya akwati akwati kalar wanda takeso,mu kuma shine zaka dubemu da wadan nan 'yan tsirarun kayan da basu wuce kala goma goma ba?" Ta fada tana nunasu cikin rainuwa,kai ya daga ya kalleta
"Ke kin manta kala nawa akayimiki?,shine yanzu yazama laifi don an yiwa wata?"
"Au hakama zakace?,wato bban amir gidan nan bau shegiya banza kamarni,to idan haka ne ita mmn amir daka yi mata kai daya da nawa,nan da wata uku kazo kasake mata na haihuwa taci tudu biyu kenan ni tudu daya?" Bacin ran baban amir yaqi boyuwa,cikin fada da hargagi yace
"Ke malama kin fara isata fa kin soma kaini bango,uwatace ke da dai abinda kika tsaramin zanyi?,don kinga ina daga miki qafa ina qyaleki?,to na rantse da Allah ki shiga hankalinki,banason hauka da iskanci kinji ko?" Da sauri mmn amir ta dakatar dashi
"Don Allah kayi a hankali yara zasu iya jiyowa,indai kaya ne ni saina qara mata a nawan tunda ni xakamin na haihuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya"
"Bata isaba wallahi saidai idan kada ta saka" ya fada yanajin nauyi da kunya da tuna sanda ya hana mmn amir din ko tsinke sanda zai auro maryam din da sunan kayan fadan kishiya,a sannan yace mata bashi da kudi,bayan ba haka bane ita kanta tasani amma ta qyaleshi bata sale daga maganar ba,sai kayan fitar sunan ahmad ta saka
"Lallai samu yafi iyawa" mmn amir din ta fada a ranta itama tana tuna lokaci irin haka da za'a kawo mata maryam din a matsayin kishiya,tunda harya riga daya rabtse gaka ta tattara kayan nata tafito tabar musu dakin,don ta tabbatar yau din Allah ne kadai yasan wainar da za'a toya tsakaninsu,tayi imani cewa da maryam ce uta a wancan lokacin da tuni tajima da barin gidan,cin kashin da yayi mata lokacin aurenta dashi a yanzu ko rabinsa baiyi ba,tayi imani Allah baya barci,kuma duk abinda kayi sai an maka mafiyinsa,gashi tun ba'aje ko ina ba tana dandana irin abinda ta dandana itama,ashe nata salama ne tunda ta iya haquri da mallakar kanta.

HANGEN DALA ba shiga birni baWhere stories live. Discover now