orphanage home 2005

Começar do início
                                    

**** DON

"yaushe zaka zo? Kalmar da ta kasa barin cikin zuciyarsa kenan, ya kamata yaje ya ganta. Shi kansa yana son ganinta sama da yadda take son ganin shi, a kullum da tunanin ta yake barci kuma ya farka dashi, tana cikin duk wani motsin sa, hankalinsa baya barin kanta haka tunaninsa.
  Bashi da babbar damuwa sama da yadda ƙaddara ta raba su, kuma ta zaɓi ta cigaba da raba su saboda tsoron lafiyar ta da ranta gaba daya. Ya rasa inda zai boye ta a duniya da zuciyar shi zata gam su tana lafiya kuma babu wani lahani da zai sa me ta.
   Kai ta gidan marayu shine shawara mafi kyau da tazo masa, a ƙalla kafin ya samo mafita akan al'amarin.
  Cikin fuska mai cike da damuwa ya juya ya kalli na kusa da shi, kana yace
' ina son zuwa kano domin ganin Zeezee nah, na kasa hakuri, shekara biyu kenan ban ganta ba sai dai a hoto.
'Don! Wai mai yasa kullum muke magana akan abu daya ne, ka sani duk ranar da ka ziyarci wannan yarinya to kamar kayi shelar inda ka boye tane don haka a kalma mafi sauki kayi signing contract din kashe ta ko sace ta domin da ita ne kawai za'a iya cimma ka. Inji na kusa dashi
'Ta yaya za su gane inda zan je? Shin ba za su hakura ba su manta da komai, shekaru kusan bakwai kenan? Ba su da aiki ne sai na bibiya ta? Ni a gani na komai ya lafa kuma ya wuce. Yace cikin fishi da gazawa gaba daya.
   Dariya na kusa dashi yayi kana yace
'kwarai kuwa! Aikin da aka dauke su su yi kenan, shi mafarauci baya taɓɓa hakura akan abin farautar sa har sai ranar da ya cimma sa. Don haka har ka manta kana raye ne kawai don kana karkashin kariya ta, idan kana son kare Zainab to ka tabbatar ka gina kan ka, ka zama untouchable. Ka fara tunanin yadda zaka karbo fadar ka da aka kwace maka, ka ginu da son daukar fansar jinin masoyan ka da aka raba ka da su, da masoyiyar ka, ka tauna kasa don aya taji tsoro. Domin a gaskiya na gaji da ajiyar lusarin namiji. Ya karasa cikin dariya. Ita wacce ta rage ka bar ta ta rayu cikin kwanciyar hankali while you embark on your mission, And your unpaid debt domin kasan bana abu kyauta. Ya sake kyalkyalewa da dariya.
  Maganganun sa sun tabba shi ainun, don haka yana ganin lokaci yayi da zai dena lusarancin da gaske, ya zama jarumi ta yadda ko sunan sa makiyan sa suka ji to sai sun fitsare wandon su don ta haka ne kawai zai iya karbar fadar sa da kuma sunan sa na Don.
  Ta haka ne kawai zai iya gina irin fadar da yake son sa zainab aciki.

**** ABBA

Yau kimanin wata daya da ziyarar su gidan marayu, amma jin su yake kamar shekara. Ita kawai yake son sake gani ko daga nesa ne. Amma ya rasa ta ya ya hakan zai faru.
   Gidan marayu gida ne mai tsaro, yawanci sai ka sanar da su kafin zuwa ka. Ta yaya zai sanar da su ga me da  bakuncin sa bayan har yanzu shi yaro ne? Ba wanda zai saurare shi ma, yace da kansa.
   Sai dai a yau ya yanke shawarar sake ganin ta ko ta halin yaya, don haka suka hada baki da direban da ke kai shi makaranta akan zai yi siyayya akai gidan marayun, shi tunda babba ne sai ya ya jagoranci tafiyar.
   Haka akayi kuwa ya je yayi siyayyan kayan ciye-ciye katan-katan.
Wanda ya kunshi carton din chocolate, biscuits, sweet, chew gum wanda adadin su ya kai katan goma gaba daya.
   Ahaka suka zuba su gaba ɗaya a bayan booth suka nufi hanyar gidan.
   Suna isa bakin gate din yaji gaban shi ya fara faɗuwa, zuciyar sa kamar zata fito waje, cikin dan lokaci kadan ya ji yana zufa, har ya bude baki zai ce su fasa kawai domin yayi losing confidence dinsa, amma sai ya ga mai gadin gate din ya nufo motar su.
   Sallama mai gadin yayi musu sannan ya tambaye su bukatar su, bayan sun gama hausawa. Sadi direban sa shi ya shige gaba wajen bayar da amsa akan cewar sun kawowa marayu kayan abinci ne. 
  Bayan an gama duba motar don tabbatar da cewa basa dauke da kayan lahani ko Baraza ga yaran aka barsu suka wuce.
   Bai tabba tunanin za'a bar su cikin sauki haka su wuce ba.
Tsayawa yayi yana duba farfajiyar gidan domin tabbas daga nan bai san mai zai yi ba kuma. Shin zai ganta yau kuwa? Domin babu yaro ko daya a tsakar gidan. Yana tsaka da muhawara yaji sadi yace
   'To yanzu ina muka nufa? Wa zamu bawa wannan kayan?
Dan daure fuska abba yayi domin bai son sadi ya gane halin kiɗimewar da yake ciki kana yace
'ciki zamu shiga da su mu bawa committee din gidan ko? Yace ba tare da shi kansa yana da tabbacin hakan ba.
  'To' haka sadi yace tare da bude mota ya fita ya fara sauko da kayan daga booth. Sai dai har zuwa lokacin Abba bai bar dube-dube ba kamar wani mara gaskiya.
   Sadi ne ya wuce gaba wajen kai kayan zuwa cikin wani office wanda aka rubuta "orphan welfare" anan aka jibge kayan, sannan Abba yazo yasa hannu. Akayi musu godiya da addu'o'i.
  Anan daya daga cikin ma'aikatan yake tambayar sa ko shi ɗan Alh. Muhammad Babagana ne, saboda kamannin su da ya gani.
Cikin murmushi ya amsa da cewa shi ɗan sa ne.
'Tabbas barewa ba tayi gudu ɗan ta yayi rarrafe ba ko shine ya aiko ka? Ya sake tambayar shi
'A'a zuwan kan sa ne, inji sadi
'To marayu sun gode sosai Allah ƙara arziki, Allah yasa ka biyo halin mahaifin ka domin yana tallafawa gidan nan sosai da ma sauraran wurare a yadda na ji. And again don Allah ka gaishe shi ka ce masa inji mal. Mutttaƙa na garko.
'To, kawai yace masa duba da yaji karshen maganar amma ace ya fadi mai yace tiryan-tiryan to ba zai iya ba domin hankalinsa ba shi a wurin, addu'a kawai yake yi ga Allah da ya bashi ikon ganin ta. Ko da daga nesa ne.
   Bai yi aune ba yaji ya cikaro da mutum, dawowar da zai yi cikin hayyacinsa ya ga wacce idon sa mararin gani ta ko wanne hali a kasa, ta zauna dirshan.
   Mai take yi a ƙasa haka? Ba dai da ita suka cikaro ba? Ya tambayi kansa
Da sauri ya karasa wurinta ya mika mata hannu alamun yana son taimaka mata, don ta miƙe amma sai taƙi ta tsaya tana kallon sa.
   Fuskanta har ta fara ja, alamun gaf take da ta fara kuka, manyan idanuwanta sun ciko da kwalla, hancin yayi ja shima, dariya ce ta so ta kwace masa amma sai ya katse ta da murmushi.
   Har ga Allah bai san mai ya jawo masa dariyar ba, shin jin dadin ganinta ne, ko kuma jin dadin ganin ta a kasa ne tare da jar fuskarta oho? Ya tambayi kan sa tare da dariya acikin ransa.
'subhanallahi, Zainab ya aka yi haka, sannu tashi, haka yaji na kusa dashi yace tare da zuwa inda ta fadi ya daga ta.
  'ya jikin naki da sauki ko? Ya cigaba da cewa
  ....naji ance baki da lafiya.
   rashin lafiya? Mai ya same ta? Ciwon me take? Take yaji fara'ar da yake ji duk ta tafi.
  Wata murya mai tsananin dadi ga kunnuwan sa ce ta dawo dashi daga karamin nazari da ɓacin ran da yaso faɗawa.
  'Eh, amma da sauki' Nagode. Ya ji tace tare da karkaɓe jikinta da share fuskar ta.
'ok Allah ƙara sauki, shiga ciki likitan yana office yana jiranki.
  Haka ya tsaya yana kallon ta har ta isa bakin office din, sai dai ba ta shiga kai tsaye ba ma a wannan karon sai da ta juyo suka hada ido.
  Bai san dalilin ta na kallon shi ba  amma shi a wurin sa duk da bai san haƙiƙanin abinda yake ji aransa ba, yasan da cewa 'yar aikensa wato zuciyarsa ta na faɗa masa cewar ba zai sake wani farin ciki mai dadi ba sai da wannan yarinyar.

Você leu todos os capítulos publicados.

⏰ Última atualização: Jul 02, 2022 ⏰

Adicione esta história à sua Biblioteca e seja notificado quando novos capítulos chegarem!

TSINTACCIYAR MACE Onde histórias criam vida. Descubra agora