🔚

1.3K 66 10
                                    

*ᎻᏌᎷᎪᏆᎠᎪᎻ*
(ᴛʜᴇ ᴄʜᴀʀᴍɪɴɢ ʟᴀᴅʏ)

           *ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
                ωαттρα∂ @neeshejay

_Dedιcaтed tσ_

*H͙  u͙ m͙ a͙ i͙ d͙ a͙ h͙*
(υммυ fυ'α∂)

*ⓟⓐⓡⓣ 181_End*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Wata ranar juma'a Humaidah ta tashi da labour gadan gadan dama tunda ta shiga watan haihuwa ya daena fita sae masjid kawae sbd irin haka.

Da sauri ya kwashe ta sae asibiti nan aka shiga da ita labour room sosae Drs suka shaiga Bata taimakon gaggawa abun tun kafin sallahr juma'a gashi har uku amma shiru har karfinta ya kare, hakan yasa ya Kira su Ammi ya sanar dasu kan kace me sun iso harda Najwah Dan Dana tana gdan Ammi.

Gaba dayansu zaman jigim sukayi suna addu'a sae 5pm ta samu ta sunkuto katuwar babay girl Dan har an fara tunanin Mata operation,bayan 27mins da haifar macen wani labour ya Kara taso Mata nan ta haifi baby boy manya dasu masha Allah. Nan fa hankalin Drs ya tashi Dan jini ya ballema Humaidah sosae take bleeding. Hakan yasa suka fara Bata taimakon gaggawa fa kyar suka shawo kan matsalar.

Bayan an shirya babies din aka fito dasu nurba gurin su Ammi ba'a mgn Amma shi gaba daya king hankalin sa na gurin Humaidah, sae da aka kaeta dakin hutu kana ya leka ya ganta a kwance tana baccin wahala karasawa yayi cikin dakin dukan gabansa na karuwa ya rasa meke damunsa tunda ta haihu baya jin dadin ransa.

Zama yayi tareda Kama hannunta ya rike kana ya sumbaci goshinta Yana jin wata kaunarta Mae wuyar rubutawa na shigarsa sosae ta basa tausayi sae kawae tsintar kansa yayi da hawaye ya rasa hayen mene na farinciki ko akasin haka Yana nan zaune har kusan magrib su Ammi suka shigo suka dubata kana suka fita Shima masjid yaje yayi sallah ya dawo zamansa ya cigaba dayi Yana gadinta chan ta farka ta fara bude idonta da suka kumbura suntum kallo daya zata Mata ta baka tausayi matuka da sauri ya mike daga kishingiden da yake ya taimaka mata ta zauna tare da saka Mata pillow a bayanta.

Murmushi ta masa sosae take Kara jin son mijinta Amma gashi gani take zata tafi ta barshi asha bazata rayu dashi ba kamar yanda sukaci buri gashi dae ta Haifa mishi yaran da yake so toh Ashe ba tare zasuyi rainonsu ba Kamar yanda suke mafarki.

Wasu hawaye masu zafi suka zubo Mata da sauri ya girgiza kansa ya goge Mata yace"wnn ba lkcn kuka bane heartbeat"

Smiling tayi tace"Ina abunda na Haifa da sauri ya fita ya karbo Mata su ya kawo ammi dake tambayar ta farkane bae ko kulasu ba.

Kallon yaran tayi tana Jin kaunarsu Mae girma cikin ranta hawaye kawae ke zuba a fuskarta kallon sa tayi tace"Dan Allah Ina neman alfarma a gurinka"

Da sauri yace"ki fada idan batafi karfina ba zan Miki Humaidah"

Cikin jin azabar ciyo tace"inaso a maeda ma yaran nan sunamu Dan Allah wato Taufeeq da Humaidah"

Da sauri yace"indan wannane ba matsa fadi Kuma abunda kike so ba Miki bayan wannan"

Smiling tayi tace"ka rike soyayyata har zuwa mutuwarka Dan ni na kire taka kamar rayuwata idan kaga na daena sonka toh fa numfashi nane ya dauke sannan I fatan ko a lahira mu tashi tare"

Da sauri ya girgiza Mata Mae yace"sau nawa Zan fada Miki bana son irin wnn maganar ne wae"

Tace"kayi hkr na dae na" tareda turo bakin ta

Smiling yayi yace"yauwa good girl"

Dan motsawan da tayi ta gyara zamanta jini ya kwace Mata cikin tashin hankali king mike Yana dubawa aiko da sauri ya mike ya fita office din Dr sae dae koda suka zo is too late Allah ya dauke ran abarsa tana murmushi ta rike hannun baby Taufeeq dake zaune

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 24, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HUMAIDAHWhere stories live. Discover now