Yace"ae kodae ba'a daura ba an kusa"

Tace"toh ae saeka jira har a daura din ko"

Fita yayi Yana mita daga cikin daki Ammi ta daga murya yanda zaeji tace"ai da ka dawo ka fada a gabana Mana"

Juyawa tayi taga ba mama Smiling kawae tayi dan tasan ganinsu da tayi ne yasa ta koma hakan yasa ta fita zuwa dibota.

Humaidah kuwa tana fita daki ta wuce tana smiling ita kadae.

Asiya na ganinta tace"ke kuwa lpyn ki kinata smiling Kamar wacce akama albishir da aljannah"

Tace"toh uwar yan sa ido"

Tace"a ba mgnr da Ido bane Naga kina abune kamar sabon kamu"

Ae da gudu Humaidah ta bita ta fice da gudu sae garden.

Jin ta buge da mutum ne yasa tayi saurin komawa baya tana rike goshi dago idon da zatayi ne taga Neehal cikin shiga ta English wears as usual da sauri tace"Dan Allah kayi hkr wlh ban kula da Kae ba ban San kana gurin ba Allah kuwa plss sorry"

Ganin ta rudene yasa yayi sauri daga Mata hannu yace"ya isa waya biyoki ne haka"

Kanta a kasa tace"Ba kowa"

Zaro Ido yayi yace"ba kowa kodae Aljani ne"

Da sauri ta juya baya taga ba Humaidah aiko tsoro ya kamata ta tsala ihu"

Da sauri yasa hannunsa ya rufe Mata baki yace"ke nutsu Mana"

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya ganin tayi shiru ne yasa ya saketa yaja hannunta sae cikin garden din, kan kujerar dake gurin ya masauki zama tayi tana kallon ikon Allah har kasa ya duka daka gansa kasan damuwa ta masa yawa Dan yanzu bashi da tunanin daya wuce na Asiya akullum tunanin ta wace hayance zaebi ya mallaketa ganin wannan ne kadae opportunity din yasa ya kudurta fada masa abunda ne zuciyarsa.

Cikin sanyin murya yace"I know it will sound somehow to you but believe me duk abunda zan fada daga zuciyata zae fito bawae kawae daga bakina ba" Dan numfasawa yayi ya cigaba "Asiya tun ranar Dana fara ganinki zuciyata ta kasa samun sukuni ban taba haduwa da wata mace da zuciyata ta kamu da sonta ba Kamar dan Allah Asiya karkice aa idan ba haka ban San wane Hali zuciyata zata shiga ban San yanda rayuwata zata kasance ba tunda nake duniya idan inason abu tofa zan so shine Kamar rayuwata Dan Allah karki juge ni na rokeki" ya daga hannu alamun roko

Jikinta gaba daya yayi sanyi itama har cikin ranta take son Neehal amma ta dau alwashin sae ta gasashi taga ya koma mutum kwarae kana zata yarda da bukatarsa da sauri ta mike tace"dakata Dan Allah kana tunanin zan iya aure mutum fasiki mazinaci Wanda bae maeda Zina komae ba a rayuwarsa toh idan kayi tunanin haka ne gwara ma tun wuri ka canza Danni bazan iya zama da wanda basae Allah ba na tabbata sallahr nan guda biyar ma baka cikawa a hakan kake so na aure ka to taya zamu fara bawa yaran da zamu Haifa tarbiyya bayan babansu ma ba isashshiyar tarbiyya yake da ita ba kayi hkr malam Allah ya hada kowa da rabonsa" tana Kae haka ta wuce cikin gda abunta

Neehal kuwa mutuwar tsaye yayi gaba daya ya kasa daga koda yatsansa ne maganganunta sae yawo suke a jikinsa da kwakwalwarsa wani irin kunya nadama da Dana sine suka dirsar masa bae taba jin yatsani kansa ba sae yau zama yayi tareda dafe kansa haka kawae yaji hawaye na zubo masa saw kawae ya fashe da wani irin kukan nadama sae yanzu yake jin haushin kansa ada suk Wanda ya masa mgn baya damuwa Amma da Asiya ta mishi yaji gaba daya tsanar kansa ta kamasa kuka sosae yakeyi.

Jin yayi an dafasa bae dago ba bae kuma dae kukan basae ji yayi yace"idan kana sonta to ka fara shirya kanka kafin ka koma gurinta da kudurinka a matsayina na Dan uwanka wnn kawae itace shawarar da zan baka idan ba hakan ba Kuma ba Asiya ba ko wace yarinyar data San ciwon kanta bazata auri mutum irinka ba"

HUMAIDAHWhere stories live. Discover now