36: Hostages (part 2)

Comenzar desde el principio
                                    

   Fitowa yayi shima daga dakin ya shiga office din Yarima, ganin ba kowa a ciki sai ya fito daga gdan ya nufi  inda ya san yana zuwa clearing head dinshi.  Busassun ganyen da yake takawa ya fiddo Yarima daga tunanin da yakeyi ya kalli gefen shi.
   "I needed to clear my head" yace da Karami bayan sun zauna shiru na ƴan mintuna.
  "Wa ya koro ka daga gdan? Mamaka koh Naya?". Dafe kai Karami yayi yace "Both".
   Yarima ma yayi ajiyar zuciya kafin ya fara magana "Kaji batun Mahnoor?"
   Karami ya kalli Yarima duk da gabanshi yake kallo, da bece komai bane bah Yarima yace "She's pregnant"
   Karami ya ɗan daga gira kafin yace "ya sani?"
   "Yes. Mamanshi ta fadamin dazu da zata kai mahnoor clinic"
   Komawa yayi ya jingina da bench din da suke zaune. Shiru neh ya biyo baya na ɗan lokaci kafin Yarima yace "My hands can't be tied. Dole akwai wani abu da zan iya yi__"Tarin daya  taso mai ya katse zancen da yakeyi. Cikin hanzari Karami ya mike yana ɗan bubbuga mai baya. Da tarin ya dan lafa sai ya nufi gda da sauri ya dauko ruwa ya kawo.
   Kurba biyu yayi ya maida murfin ruwa ya rufe yana ajewa gefe.
   "Daddy mu shiga ciki ka hutu". Hannu Yarima ya kai ya rufe fuskar shi "Muje ka kaini gdan Yusuf, I can't take this silence any longer". Karami yace "Ina ga zefi mu bari sai zuwa gobe tunda yau deadline din ze cika, in muka ji shiru sai mu nemi wani hanyar"
   Yarima ya girgiza kai "Tun farko ni nayi kuskure dana linke hannuwana bayan babu tabbas a plan din farko, in wani abu ya same su I'll forever regret not doing more"
   Mikewa yayi yace bari in dauko key, koh taku biyu beyi bah yaji Yarima yaja dogon numfashi, koda ya juya sai yaga ya  dafe kirjin shi yana kokarin yin numfashi.
  A sukwanne ya kai inda yake ya dafa shi yana kiran daddy. 
   Beh san daga inda ta fito bah sai ji yayi tana kiran azo a taimake su.  Zuwa akayi aka dauki Yarima aka wuce da shi gda.

   *******************************
  
A nan gda Dr Sadiq ƴaƴan Fariha yazo ya duba shi. Jinin shi neh ya hau amma Alhamdulillah beh hau sosai ba tunda komai ya lafa ba tareda zuwa asibiti bah.
 
    Duk wanda mah beh lura da tashin hankalin da mazajen gda ke ciki bah a da, yanxu ya fahimci da akwai matsala. Everyone was quite, babu wani surutu koh shige da fice sosai a gdan. Shi yasa beyi mamaki bah da yaji kiran Momma da aunty Safiya. Da ya shiga living room ya samu Aunty Hannah mah na wurin.
   Kafin ya zauna ya fara yi ma Aunty Safiya godiya na zuwanta a daidai lokacin da tayi, dan tsoro ya kafar dashi wurin daya shi yasa ya kasa kira azo a taimake su.
   Tace "Its alright" cikin British accent dinta.
   Koda ta koma magana da hausa accent din beh bace bah "My dear meh ya faru kafin faduwar Yarima?, Maganar meh kukeyi daya tada mai hankali?".
   Saida ya numfasa yace "ba wani specific magana mukeyi bah. Hasali mah casual talks neh na yau da kullum akan aiki da kuma kula da estate din".
  Beh tsaya kallon fuskar su bah dan yasan basu yadda da abinda ya fada bah, kawai sunkuyar da kanshi yayi ya lakwasa kafa yana jiran suce wani abu.
"Kaima kenan baka san abinda ke damunsa bah".
Da sauri ya amsa da eh
   "Baka lura da yana cikin damuwa bah kuma"
   Yace "Na lura da haka, shi yasa mah na zauna tare dashi koh ya fadamin abinda ke damunsa"
  Kafin a cigaba da interrogating dinshi ehsaas ya shigo falo. Coat din dake sargafe bisa kafada ya aje bisa kujera sannan ya matsa cikin falon suka gaisa da kowa. Nan yake jin accent din Ehsaas baya fitowa sosai kaman na mamansa, yace kila dan shi ya dawo da zama nan neh iyayen shi kuma na England.

     Da suka bar falon tare sukaje ganin Yarima wanda yake barci har ya zuwa lokacin.
   "Any news?"
Ehsaas ya girgixa mai kai.  Inna lilllahi wa inna ilaihi raji'un ya fara fada kafin yace "Ƴan awanni kawai suka rage kafin deadline din da suka bayar ya cika"
   Ehsaas yace "In shaa Allah zamu ji wani abu kafin lokacin".

   Kwana sukayi jiran suji wani abu, basu san exactly ta hanyar da zasu san an dace da rescue mission din bah, amma abinda dai suka fi sa rai akai shine suji phone call ko da text neh meh dauke da kalmomin *MISSION SUCCESSFUL*.
    Break in the ice da suke tsammani ba shi suka samu bah, maimakon phone call a TV suka samu update, kuma ba irin wanda sukayi expecting bah.
   
   Da safe neh anyi shirin zuwa aiki, yara sanye da uniform,mata nata hadadar hada breakfast.momma na sama tare da Yarima a daki, a kasa kuma Aunty Hannah da Safiya neh zaune a falo da tea flask a tsakiyar su suna shan shayi, of course tunda da safe neh da news zasu fara kafin su nemi kallon wasu programs.
    Karar faduwar glass ya kai hankalin sauran dake dining area zuwa ga abinda ke faruwa a falo.
   Headlines din da aka nuna suka karanta kafin akayi playing video din da aka ambata a headlines din.  Shigar irin ta ƴan ta'adda, wannan rawanin, dogon gemun da bakaken kaya. A gefen meh magana cikin harshen larabci mutum neh zaune an rufe mai fuska da bakin kaya. tun a headlines din suka san wanda ake magana akai, amma saida aka bude fuskar suka kara gasgata abin.

Zuciyar TauraroDonde viven las historias. Descúbrelo ahora