Maleeka tace Ayya hard luck Allah y jikanta

Yace ameen A sanyaye, ya jikin maleek

Alhamdullh he is improving Ana samun cigaba yanzu kan, ko Dan yaji zaa tafi neman meenal ne oho

Dariya Taso ba muhassin yace haba sister maleek da bemasan abinda muke cewa ba yaushe yaji wannan,

Tabe baki tayi tace bar wannan lover boy din kawai, Allah zaka sha mamaki kaga yanzu ya kike yaga meenal gaban sa,

Murmushi muhassin yayi yana matsawa kusada gadon maleek.

Tinda asubah around 6 Abba yagama shirinsa da yar jakarsa Karama ya dauki duk CV dinsa, yana zuwa park ba dadewa mota tacika suka kama hanya, tin abba najim dadin tafiyar har yagaji don tafiya ce bata wasaba, suna zuwa kano suka tsaya sukayi salloli Abba yadan samu abu yasaka ma cikinsa wani abu, kafin suka Kara kama hanya basubane suka sauka  Abuja sai around 8pm na dare.

A jabi park suka sauka, waya sukayi da alhaji ganin dare yayi yace gaskiya mota zata maka wayar samu kuma  mun fita driver baya nan Amman bari murad yazo ya dauka, toh alhaji godia nake Allah y saka da alkhairi,
No bakomai just find some were safe and wait.

Yana Zaune a park kamar 1hr haka saiga murad ganin mutum tsaye da jaka shi kadai yasa yagane shine, sauka yayi yaje kusada dashi ya bashi hannu suka gaisa cikeda girmamawa,

Wata mota mai mugun kyau suka nufa shi murad ya zauna maxaunin driver shikuma Abba yashiga dayan Gefen, tafiya me Dan tsawo sukayi Abba yaga sunshigo wata unguwa mai mugun kyau shiru take babu ko babura, saidai fitin streetlight da suka ma gurun ado,

Gani yayi sunyi horn a bakin wani kantamemen gida, nan da nan aka bude masa gate ya kutsa Kai cikin farfajiyar gidan duk da dare, Amma hakan baisa Abba rashin ganin kyaun gidan ba kasacewar fitulu sun Haska ko ina, murad  ya zagayo yabude masa tareda karbar jakarsa, gaba yayi abba nabiye dashi abaya,

Adede bakin kofar gidan Wanda Ginin yakasance gidan bene sukayi knocking, wata ce wadda kana ganinta kasan yar aiki ce tabude musu kofa, kutsa Kai murad yayi cikin falon tareda ma Abba iso, duk abba bawai farin shigarsa gidan masu kudi bane Amman baiyi tunanin gidan alhajin yakai haka,

Wani sassayan kamshine mai Dadi yamasa sallama, shiga yayi ya zauna kan daya daga cikin royal chairs din yana bin haddaden falon da kallo, murad ne ya haura sama tareda sallama ya tura dakin ummyn shi, kan sallaya yaganta

Durkusawa yayi har kasa yana, ummie barka da dare barka de murad kundawone eh ummie yana falo, toh bari naje mugaisa tafada tareda mikewa cikin hijab dinta,

Abba dake zaune yana kallon kantamemiyar tvn dake aiki, yajiyo alamar tafiya a steps yana daga kansa yahango wata kyayyawar mata wadda shekarunta bazasu wuce 45 ba kyakyyawa ce sosai gata fara sol, karasowa tayi fuskarta daukeda murmushi,

Gaisuwa sukashigayi da Abba cikin girmamawa, tace gashi kazo alhaji baya nan yaje meeting karfe goma ze dawo, dining aka kaishi Inda aka shirya abinci kala kala zuba iya Wanda zeci yayi yaci don ma baya jin yunwa don agajiye yake,

Ummie ta kalla murad ciki yaren fulatanci tace kakaishi daki kila yagaji yana son hutawa, daukar jakar abba yayi abba yabisa suka nufi wani matsakaicin part mai kyau key yasaka yabude, part din ko ina a tsabtatace yake yashiga ya aje ma Abba jakarsa, yace Abba Idan akwai abinda kake bukata kamin waya, toh murad nagode Allah shiyi albarka.

Abba binsa yayi da kallo yana shawar yaron don akwai tarbiya da ganin girman manya, mikewa yayi yashiga cikin dakin komai a gyare yake toilet yashiga yayi wanka tareda yin salloli yana gamawa yakira mammy bai wani Dade ba bacci yayi gaba dashi Don dama agajiye yake.

Washegari bayan sallahn asuba sake komawa yayi gurin 8am yaji kamar Ana buguwa fitowa yayi yabude kofar da murmushi ya kalli saurayin sai kuma yaga Bana jiya bane amman de suna kama sai kuma yaga kamar najiya shine babba,

Ina kwana abba y gajiyar tafiya, Alhmdullh cewar Abba yana sake kallonshi, yace ni sunana Ayman kanin ya murad yafada yana murmushi dad yace namaka mgna, ok to inazuwa shiga yayi ya shirya sannan yafito yaga har lokacin yana zaune yana jiransa, tare suka shiga cikin part din dad Wanda yafi najiya tsaruwa,

Karo suka kusa ci da murad ya tsaya yana Abba katashi ya gajiyar jiya tareda mika masa hannu suna musabaha, sai a lokacin abba yakkali nakusa dashinyaga ya Dan dara yayan nasa tsayi shikuma murad yadanfishi haske Amma de suna kama sosai,

Alhamdullh murad, ai da Ayman yashigo nayi tunanin Kaine,

Dariya yayi yace to ai ni gani abba Ina sauri zanje Asibiti yanzu aka kirani ankawo wasu patient,

To Likita Allah y taimaka yabada sa a, Ameen abba nagode yawuce dasuri yana shiga mota.

Zauna suka iske Alhaji shikin shirinsa, nan suka shiga gaisawa da Abba kamar daman sun San juna, Alhaji yajasa dining suka yi lafiyayyan break fast su ukku cikeda nishadi, sai a lokacin Alhaji kecewa Ina murad, Ayman yace dad ai ya fita tin dazaun wai kiransa akayi, ok toh kaifa ba case yau ne, Abba Akawai fa buh sai anjima zanfita,to Allah taimaka,Ameen dad.

Shide abba yana ta kallonsu cikeda shaawa don gaskiya yanayin gidan ya burgeshi sosai.

Alhajj da Abba suka fita tare, saida suka gama processing  komai agunda abba zeyi aiki babu dadewa suka kammala komai abinka da kudi,A hanyarsu ta dawowa Abba yana ta kallon garin don garin yamasa kyau sosai, Alhaji ne yace masa Amman kanada gurin zama koh don gaskiya aiki nan nanda sati daya zuwa biya akeson kafara zuwa gaskiya,

Abba yace babu Amman inason nasiya, toh kashirya siye kokuwa muje sai ka dawo, ah muje kawai gara muyi komai yanzu Dana tashi nasan parking kawai zamuyi,

Awata unguwar suka yafaka itama mai mugun kyau babu ma tazara sosai tsakanin gidan Alhajin suzuwa wannan unguwan gidajene masu kyaun gaske Amman de basukai na alhajiba,

Alhaji ya kallisa yana ce ma Abba kazabi Wanda yamaka acikin su abba yazabi Wanda yamasa mai mugun kyau dan Daidai, Alhaji ba bata lokaci yakira agent dinsa yana suzo zaayi cinikin wani gida, duk batareda bata lokaciba aka kammala komai gida yatashi 5m duk da Abba yasan alhaji yace yabada ne Kawai Amman wannan gidan yatasamma milyan 10 Don gidan is well furnished komai akwai shiga kawai zasuyi.

Mikama abba ta takardun gidan yayi tareda makulli yana cewa Allah congratulations, da murmushi abba yace tanks am greatful.

Murya kam gurin abba har ya rasa Inda zai saka kanshi yakuma rasa da wani bakin zai ma alhaji godia don yagama masa komai a rayuwa, bayan duk sungama duk abinda yadace aranan washe gari abba yace zai wuce Don yaje su shirya, Alhaji kirikiri yanasa hawa mota wai akwai nisa kuma ba security,

Nan da da nan aka gama shirin Jirgi, Ayman yatafi kaisa airport ba dadewa jirginsu yatashi zuwa borno..........


Mrs abvdool ce....

"MALEEK"Where stories live. Discover now