8

1K 72 0
                                    

📿📿📿📿📿📿📿📿

   🎀Guguwar So🎀
     7⃣1⃣➡78

By harphsart Rano✍

Ta dan numfasa sannan  ta cigaba..

Haka suka shirya ina jinsu suka fito, a falo na shirya musu a bin kari.. Sai da sukaci sukayi katt.. Shikuwa alhaji ko abincin ya kasa zama yaci..

Sun fito zasu tafi ne sulaimanu yace ai shi bazai bisu ba..

Galla masa harara ja'afaru yayi sannan yace kadda Allah yasa kaje.

Na lura dakai kwata kwata bakason zumunci wlh.. Shidai shiru yayi yana sauraronsa..

Bayan da Alhaji bai yi dashi akan ya bisu ba amma sam yaki..

Haka suka ja suka tafi ko driver basu bari yaa bisu ba..

Haka kawai naji zuciyata ta cinke, kwata kwata hankali na bai kwanta ba..

Na dawo daki na zuba tagumi, chan naji dawowar yara daga makaranta..

Dole na mike na fita kafin su shigo su tarar dani a haka.. Kasancewar su yara masu wayo..

Chan dare sai ga kiran Alhaji, jikina na rawa na daga..

Jin muryarsa yasa nayi ajiyar zuciya.. Nan yake sanar dani sun isa lafiya sai gajiya..

Haka mukayi hirarmu sannan ya nema na bashi yaransa yaji muryoyinsu..

Sun dade suna zuba masa surutu daga karshe yayi mana sallama..

Tou kwanansu biyu a lagos, abinda yaje nema anyi nasaraa..

Da haka ya kirana yana sanar dani, Murna yake sosae nima na shiga tayashi..

Washegari suka shirya don juyowa...

Ina zaune a parlour, Ina jiran isowarsu. A lissafin da nayi dga fitowarsu nasan suna gab da shigowa..

Tun Ina zuba ido ina duba lokaci har tara na dare babu su ba alamarsu..

Waya kuwa na kira sau ba adadi, amsar dae daya ce akashe take.. Nan fa hankali na ya tashi..
Ganin zaman bazae mun ba yasa na dauro alwala..

Ina nan akan sallaya naji shigowar mota, zumbur na mike nayi waje..

Sororo na tsaya ina kallonsu. Dukkaninsu sun sunkuyar dakai kasa.. Wani bakin mutum na gani gefensu yasha riga da wando. Babu alamun fara'a a fuskarsa..

Gabana ne ya yanke ya fadi, Muryata na rawa na shiga tambayarsu, Lafiya yaya na ganku haka?? Ina mijina?? Me ya faru ku sanar dani?? Ba wanda ya tanka min..

Na shiga rusa kuka, ganin zan tara musu jama'a yasa tukur daka min tsawa. Mijinki Allah yayi masa rasuwa..

Kuma maganar gawarsa mun riga mun binne ta achan saboda mun isa

Jiri naji yana dibana bansan sanda na yanke jiki na fadi ba..

Toh bayan sati daya da mutuwar alhaji, sun tsaya sosae wajen karbar gaisuwa...

Ina zaune a daki, tukur ya shigo min ko sallama babu..

Gobe ki shirya zamu je wani guri.. acewar tukur,  Kuma tare da yaran, sannan bana bukatar ki dau wani abu..

Da sanyin safiya muka kama hanya.. Muna ta tafiya, sai gamu a kano.. Wannan gidan da muke ciki shi ya kawo mu ya dire, wannan shine abunda kula mallaka keda yayanki na daga dukiyar dan uwanmu..

Kuma anan nakeso ku cigaba da zama dan nima kwanannan zan dawo garin

Karki tunanin guduwa da yayan dan'uwanmu, duk wani motsinki ido na na kai, yana kaiwa nan yajuya ya tafi..

GUGUWAR SO (Completed✅)Where stories live. Discover now