1

4.8K 175 2
                                    

GUGUWAR SO

HAFSAT RANO
  
Page   1-20

Tafiya take cikin matsanancin tashin hankali wanda sam bae sa ta lura da inda take sa kafarta ba.. Tafiya kawae take hawaye ya wanke mata fuska.. Tana dana sanin kasance warta cikin wannan duniya.. Why? Why?? Shine abunda take ta nanatawa a zuciarta..
Wani matsanancin gudu yake a dalilin kiran gaggawar da akae masa cewa jikin mominsa ya rikice.. Bai lura da ita ba sam.. Sae dayazo daf da ita.. Wani wawan birki ya taka hade da danna horn iya karfinsa..
duk yanda yaso ya kauce mata be samu nasara ba sae daya bangaje ta tae wata razananniyar kara.. hakan ya jawo hankalin mutane da suke wucewa jefi jefi

I suka yo kanta dan kawo agaji.. Fitowa yae daga motar a rude "ohh shit damn it. Ya karasa wurin tare da nan russunawa a gabanta tana sheshekar kuka.. ta dan kurje kadan amma bata samu wani mummunan rauni ba..
mutane nata mata sannu suna Allaha kiyaye gaba.. Ta mike jiki ba kwari ta kama hanya tana dan dingisa kafa, hakan yasa yae saurin shan gabanta tare da cewa pls kiyi hakuri dukda kece me laifi kina tafiya wt out checkin d road.. Bata tanka masa ba illa cigaba da tafia da tayi.. yace baiwar Allah ina sauri ne amma ga wannn ki saya magani.. A hankali ta furta ka barshi na gode.. Ta cigaba da tafianta tana dingisa kafa.. Noke kafada yayi alamun i dnt care ya fada motarsa ya bata wuta..
Allah Allah yake ya gansa gaban mominsa. Karfe shida da yan mintuna ya matsa horn a kofar wani hadadden get.. Me gadi ne ya leko ta wata yar kofa ganin me horn din ya sashi bude get din cikin ajama.. kafin ya gama budewa tuni ya shgo tare ta ftowa cikin sauri wanda har yaso ya mnta da rufe motar.. Ya juyo da sauri ya danna securityn motar ya haura balcony..
Momynah! momynah! Shine abunda ya shgo yana fada.. Yae saurin haurwa sama ganin ba kowa falon. Momy ya hango kwance kan sofa gefenta daddy ne,, sae twins en momy islam da iman.. Sae auta khalil wanda suke kira da little khaly , .. Saurin karasawa yayi ya rike hannun momy tare da cewa momyna ya jikin.. Shafa kansa tayi tare da murmushi tace my boy har ka iso.. Jiki alhmdlh.. Ya juya zua ga dady ya gaisheshi.. Ya amsa masa da kulawa.. tare da tambayarsa hanya .. su iman ma suka gaisheshi..
Bayan sunyi sallah sun dawo duk suna zaune a falo daddy yae gyaran murya yace dama inason na ftrda momynku india akan matsalar nan tata shine nake ganin mene shawarka?? Ya jinjina kai yace daddy shine tunanin da nake nima.. Daddy yace ina da bussnss da zae kaini india kuma atleast zanyi wajen 1month.. kaga sae mu tafi tarr.. Anan suka yanke shwaran ftar da momy india nxt week ..
A hankali take tafia hadda karaso kofar wani kurkutacchen gida wanda duk unguwa babu gida mafi muni irinsa.. Tura kyauren gidan tayi hade da sallama..
Umma ta mike da sauri ta riko hannunta gami da cewa "Me faru dake nurr?? Me ya tsayar dake haka kuma naga kin shgo hankalinki a tashe ko wani abun kawun yayi miki?? Bata samu damar amsa mata ba saboda zafin da kafar ta ke mata ga wani zugi da dan yatsanta ke mata.. Umma ta cigaba shisa nace karkije karkije kika nunan ba abunda zae faru gashi nan abunda ya faru ta fada tana share kwalla da gefen zaninta.. Nurr ta fashe da kuka hade da cewa umma kafata zafi hannu na😭..
Mota ce ta bige ni umma.. Umma ta rafka salati mota nurr garin yaya?? Ta wawuro hijabinta tace wuce muje wurin habu me chemist ya dubaki.. Nurr ta riko hannun umma hade da cewa umma ina muke da kudin zua chemist.. Sai a lokacin umma ta tuno basu da ko naira biyar.. Ta rausayar da kanta gefe tace tou ya za miyi muje ko bashi ya bamu inasa ran hajia zata biyani kudina. Tace umma ba komi akwai ragowar rop bari na shafa ta wuce ciki tana dan dingisa kafa amma bata bari umma ta fahimta ba saboda taga yanda umma duk ta rikice ita kuma bata son damuar ummanta..
Cikin sauri ya shgo rike da wata bakar leda yana shgowa ya tarar da ummansa da nurr a zaune a tskar gida nurr ta bawa umma labarin yanda sukae da kawunsu dazu..
Da sassarfa ya karaso ya jao kujera yar tsuguno yace umma sannu da gida, ta amsa da abbana sannu da kokari Allah yai maka albarka.. Amin Yace umma wlh yau aikin ne baya tafiya sosae shisa kukaga nayi yamma. Amma ga abunda na samo gami da mika ma umma ledar. Nurr ta mike ta dauki leda ta shga wata yar rumfa ta dauko wani kwano ta juye Zogale ne da kuli kuli.. Ta zo gaban umma ta ajiye hade da komawa ta debo ruwa a kwano tazo ta ajiye ta koma gefe ta zauna.. kabir ne ya lura da dingishin da kanwarsa take ya juyo cikin kulawa yace kanwata me sameki a kafa?? Umma tace wlh mota ce dazu ta bige ta tana dawowa daga gidan kawunku. Subhanallah mota umma garin yya?? Nan umma ta labarta masa yanda nurr da shaida mata. Yace ai ya kamata aje a duba ko tayi targade ne.. Amma kuci abncin sae na rakata gidan talatu ta duba ko targaden ne.. Umma ta jawo kwanon suka fara cin abinci a hankali shikuma kabir ya kwantar da kansa jikin bangon hade da lumshe idonsa yana tunanin rayuwar✨

GUGUWAR SO (Completed✅)Where stories live. Discover now