38

2.4K 103 80
                                    


    
    ♥ ❤
           
         ♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*Addu'a Yayin Da Ruwan Sama Yake Sauka*

اللّهُمَّ صَيِّـباً نافِـعاً ..

*written *✍
       -by-
         *Deeja one love*

Wattpad 13deeja.

Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *ONE LOVE* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe,  muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.

_*39*_

Yaya Khaleel yace"shikenan Momma na sa.....",cikin tsawa Abba ya dakatar dashi yace"dakata Khaleel mu zaka ciwa mutunci mu ɗauki ƴar mu baka tun tana cikin mutuncin ta sai yanzu da ƙaddara ta gifta mata zaka ce zaka rabu da ita?".

   "kai fa ka matsa sai tayi karatu da natsuwar ta da komai ka matsa muka barta amma yanzu zaka ce ka rabu da ita,to wallahi ka sani kana sakin ta itama uwar ka sai ta bar gidan nan,yanzu ya rage naka kuma ko bayan raina ka saki Mama na ban yafe maka ba".

   Cike da mamaki Momma da Ummi duka suke kallon Abban,Yaya Khaleel kuwa idanun shi kamar zasu faɗo ƙasa.

    Baban gida yace"ya isa haka Abubakar me ya kai ka da wannan furucin",cikin fushi Abba yace"Yaya wallahi na rantse matuƙar ya rabu da ita to itama uwar shi sai ta bar gidan nan kuma yafewa ba zan yi ba idan har ya sake ta ko bayan babu raina".
   
     Ran maza ya ɓace dama haka Abba yake akwai zuciya,duka wajen jikin su yayi sanyi,ni kuwa wata irin ajiyar zuciya na sauke dan bana so Yaya Khaleel ya rabu dani.
   
    Na tsani zaman zaria yanzu fata na kawai na bar cikin ta,Baban gida yace"Khaleel hukunci yana nan dan haka ka tattara matar ka ku bar garin nan".
   
    Baba ya rufe taro da addu'a nan fa hayaniya ta fara tashi,"ai dama na san hakan zata faru kuma wallahi ki sani kin jawa kanki masifa da bala'i sai kin gwammaci baki ratso ta hanya ta ba ".
   
    Yaya Abdus-samad ya cilla mini harara yace"ba dai Borno ba Allah ya kawo ki lafiya banza shashasha kawai",Yaya khaleel kuwa cikin baƙin ciki yace"ki tashi mu tafi indai bina kika zaɓa na miki rantsuwa sai kin tsani zaman ki tare dani,ba zaria kike gudu ba to sai kin so dawowa zaria da kanki".
   
    Momma tace"yauwa ɗan albarka kada ka raga mata ko kaɗan ka tabbatar ka ƙuntata mata",ni dai cikin sanyin jiki na miƙe na fice daga ɗakin ina kuka.
   
  Ɓangaren mu na nufa,a bakin ƙofa na tarar da Ummi tsaye,muna haɗa idanu na saukar da kaina ƙasa,Ummi ta cilla mini harara tace"uban me kika dawo kiyi mini anan?".

   Murya ta bata fita hakan yasa nayi shiru,"kin juya kin bar nan ko sai na nakasa ki",cikin sauri na juya na fice.

   Wajen parking ɗin motoci na nufa anan na rakuɓe kamar almajira,ga jiki na har rawa yake saboda zazzaɓi.

     Ina nan tsugunne har suka gama shiryawar su,zuwa lokacin har ƙafa ta ta gaji da tsugunno dan haka na zauna kawai na miƙar da ƙafafun.

     Suna ƙarasowa wajen nayi saurin miƙewa,duka suka shiga motar sannan nima na buɗe na shiga.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 14, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

K'AREENATEEY Where stories live. Discover now