37

925 23 2
                                    


    
    ♥ ❤
           
         ♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

الدعاء اذا تقلب ليلا

Addaua iza takallaba lailan

                           ADDUAR YAYINDA MUTUN YA FARKA MAANA YAJUYA ACIKIN BARCINSA

لا إله إلا الله الواحد القهار رب السموات والأرض وما بينهما العزيز الغفار

La iha illahul wahidul kahhar rabbussamawati wama baynahuma alazizulgaffar

                              BABU ABUN BAUTAWA DAGASKIYA SE ALLAH MAKADAICI MARINJAYI UBANGIJIN SAMMAI DA QASSAI DA ABINDA KE TSAKANINSU MABUWAYI ME YAWAN GAFARA

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*written *✍
       -by-
         *Deeja one love*

Wattpad 13deeja.

Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *ONE LOVE* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe,  muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.

*_37_*

  Kamar wanda aka tsikara sai kuma Yaya Al'ameen ya nufi wajen Yaya Khaleel,ɗago shi yake ƙoƙarin yi amma ya kasa hakan yasa ya nemi taimako daga Yaya Abdus-samad,shima sai lokacin ya iya nufar ɗan uwan nashi da sauri suka ɗauke shi sai asobiti,dan ma tsakanin su babu nisa sosai.

    Be wani jima ba ya farfaɗo,ai fa nan ya sake haukace musu,Yaya Al'ameen yace"ka kwantar da hankalin ka mana".
   
  Idanu jajur ya kalle shi yace"in kwantar da hankali na fa kace?,mata ta da wani ƙaton",Yaya Al'ameen yace"haba K.A kada ka bari zargi ya shiga tsakanin ku mana".

   Maida idanun shi yayi ya lumshe cikin kunar rai yace"karuwa ce dama!",Yaya Abdus-samad ya buɗe baki a karo na farko yace"haba my man ba dai karuwa ba ni ina ganin da wani abu a ƙasa".

   "babu wani kare ta da zaka yi Abdus-samad domin kuwa kai kanka kasan a ɗan kwanakin nan ta canza da yawa".

   Sosai suka dinga tattaunawa akan matsalar har likitocin suka sallame shi,babu yadda Abdus-samad be yi dashi ba amma yaƙi yarda hakan yasa kawai ya ƙyale shi.

****   ******   ******
Ni kuwa ina can gida ina faman jiran kiran nashi,haka har barci ya ɗauke ni,sosai na dinga mamakin yadda be kira ɗin ba da safe.

  Har na shirya na tafi makaranta yau 12-2 sai 4-6 haka muka fito duka amma ina tunanin meya hana shi kira gashi ban san me yasa yanzu na damu dashi ɗin sosai harma ya zarce shirin mu na farko.

   "Buddy kina jina kuwa",cewar Jabeer kenan a lokacin da zai maida ni gida,"me kace ne?",na tambaya.

   Cikin kulawa nace"kaga Yaya Khaleel ne yace zai kira ni tun jiya har yau kuma shiru",wani yawu me ɗaci ya haɗiya sannan yace"hmmm!may be aiki ne yayi mishi yawa har ya manta".

K'AREENATEEY Where stories live. Discover now