35

778 23 5
                                    


    
    ♥ ❤
           
         ♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*written *✍
       -by-
         *Deeja one love*

Wattpad 13deeja.

Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *ONE LOVE* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe,  muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.

An ƙarbo daga Abu Huraira Allah ya ƙara mishi yarda yace"Kada maƙwabciya ta raina abinda zata bawa maƙwabciyar ta koda kofaton akuya ne.

Wani hadisin manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yace"kalma me daɗi sadaka ce".

*_35_*

Ban ce komai ba,sai yatsun hannun shi da na zubawa idanu,shi kuwa fuska ta kawai yake kallo,be ƙi mu zauna har abada a haka ba.

  Ƙarar waya ta ne ya dawo dashi hayyacin shi,a tare muka kalli screen ɗin wayar, *Abar ƙauna ta*, wayar ya ɗaga.

   "Haba Juwairiyya daga wanka sai kije ki zauna gashi duk an taru ƴan uwa da abokan arziƙi ana ta ɗaukar hotuna wai kina ina ne?".

  "ku cigaba da ɗaukar hotunan ku ita ba yanzu zata zo ba",muryar Yaya Khaleel kenan da ta ratsa dodon kunnuwan mu.

  Dariya Rufaida tayi tace"ah! Yaya shikenan to,ke kuma ai sai kice mini jinya kika je",murmushi nayi kawai.

  Katse wayar yayi sannan ya kalle ni,nima shi naka kallo,"dama Yaya baka da lafiya?",gira ya ɗaga mini.

  "ayya ai ban sani ba ya jiki?",kauda kai yayi yace"taya zaki sani bayan baki damu dani ba yanzu,tunda na gama miki amfanin da zan yi miki".

  Abincin na buɗe na hau zuba mishi domin bana so a cigaba da wancan maganar,fuska ta ya riƙo ya juyo dani.

  "wai Yaya fa kana sani babu kyau namiji yana taɓa mace amma kai kana yi har ma fiye da haka",murmushi kawai yayi bece komai ba.

   "waye ɗazu ya kawo ki gida?",sai da na ɗan kalle shi sannan nace"Aboki na ne Jabeer",ɗaga gira yayi yace"oh! Shi yasa kika ganni kika ɗauke kai".

   "Yaya kai fa kace kada na kuma yi maka magana,idan nayi maka zaka karya ni",yace"da gaske?",shgawaɓe fuska nayi nace"kai Yaya!",ki zuba mini abincin pls.

   Miƙo mishi nayi,kallo na yayi sannan ya kauda kai,murmushi nayi sannan na ɗebo na nufi bakin shi.

  A hankali ya buɗe bakin na zuba mishi,lumshe idanu yayi sannan ya kuma buɗewa,a tare muka yi murnushi.

   Shima ya ɗebo ya nufo baki na dashi,babu musu na buɗe ya zuba mini,lumshe idanu nayi nima.

   Haka muka dinga ciyar da juna har muka ƙoshi,miƙewa nayi domin tattara kwanikan yayi saurin dawo dani ya zaunar dani.

K'AREENATEEY Where stories live. Discover now