Bayan dan Wani lokaci taga an sauke su a wata hotel mai taken ' _Sarova mara GC: narok county kenya,_

Nan ne ta gane ashe ba south african suka iso ba kenya ne,wajen ya hadu iya haduwar da zaka so ka zauna nan har iyakan karshen rayuwar ka.

Bayan fitowar sa daga motar Wani private resort ya nufa da ita mai kofofin glass da walls da decors din hutawa na gani na fada,

shi tun daga gida yayi booking reservations din sa da komai da komai online da shike ma ba zama zasuyi anan ba...

yace ki shiga ina zuwa ya mata nuni da wani waje alaman daki ne...
Daga nan Sai ya fice.

Sama ta haura ita kam"'tana turo kofar wani sanyin dadi ya ratsa ta

dakin nasu an hada masa shiri mai tsafta
kan lallausan tuffed bed din ta zauna tana kalle kallen cikin kafin ta mike izuwa window view don ta hango abubuwan ban sha'awa dake shimfide a oudoor landscape..

Its so amazing...bata tabayin tunani a kasa kamar kenya za'a samu luxury hotel har haka ba.

Bata hankara ba taji yace u like it?...ta danyi murmushin bazata ta juyo..sai jin shi tayi daf da ita,hakan  yasa ta dan kalle sa,

C'mon lets go...'ya fada cikin sauki ya kamo hannayen ta zuwa sitting room inda suka baro.

Wasu yan maza tagani suna shigowa da packaged shoping bags a sanye da kaya kamar na indian police force sai dai shi plain ne
' Yayi mata ido akan ta dauki wanda zata iya ta koma ciki,nan ya sallame su ya biyo bayan ta.

Zata ajiye yace kayan ki ne,u have to check them and c inyayi miki ko kina da wasu wanda zaki sa ne?"a shagwabe tayi masa kallon ai baka barni na dauka ba kafin tace ah a,..
hmm kawai yace ya juya mata baya
Nan ya shiga rage kayan jikin sa,tana tsaye har ya nufi toilet ya sake shower akan sa sannan ta fito da kayayyakin.

Wildrose hip up skirt guda daya da Fellini trousers royal blue sai tops da madaidaitan hair covers dinsu wanda suke matsayin mayafi sai inner wears pants da bra guda biyu da normal sandal shoes..

"komai yayi mata anan.. dan Da wuya ake samun irin wannan brand din kayar sabida mostly illegal shippers ke shigowa da shi daga design industries a india.

Bata gwada ko daya ba dan yawanci size din ta ne Yana fitowa ta shiga tattara kayan zata ajiye a gefe' yana goge kansa da hand towel yace ya baki gwada ba,
Bata son cika kallon sa a wannan yanayi amma sai ta daure tace,na duba zasu yi min"..

Yayi shiru alaman yaji sai tace..nagode' yayah..
a takaice Yayi grin.. tare da umartan ta akan taje itama ta kimtsa tayi sallah.

Agurguje tayi da jikin ta kammala komai da shike ba inda zasu je kuma lokaci ya tafi..

royal blue fellani trousers din ta kwama' irin wandon nan ne fubu masu fadi da tsayi,akai ta daura farar long sleeve shirt tayi tucking kamar yadda ake sawa

She looks serene and simple Tayi kyau sosai duk da ma babu kayan kwalliya sai chappets din data goga akan lips dinta

shigar sosai ya bayyana yarintar ta akan tsari

Just in time yasa aka shigo musu da abinci site din,don sam baya son fiye shiga mutane.

Daga nan Bacci mai nauyi tayi Bata ma samu daman ganawa da kowa ta waya ba.

Washe gari da safe sosai ta huta ma ranta  bayan sun kammala komai awaje aka shirya musu breakfast a wata outdoor open air bungalow su biyun su..

'Fresh fruit juice da cooked egg and veggies'hade da sarova mara special akayi serving.

Wasu ma bata iya ci ba suka tashi suka koma daki don tun bayan sallahr asubahi yake ce mata zasu fita wani waje

AJALIN SOWhere stories live. Discover now