Rayuwa

1.3K 52 3
                                    

Rayuwar aure a musulunci musamman ma a ƙasar hausa,abu ne mai muhimmanci wanda kuma yake cike da ƙalubale. Babban abinda yasa muke fuskantar matsaloli ya samo asali ne daga tsallakewa tsarin da musulunci yayi wa aure.

Wasu matsalolin masu gyaruwa ne, wasu kuma fawwalawa Allah komai Shine kawai zai magance su.

Zaman tare aka ce zo mu zauna zo mu saɓa, to amman idan aka saɓa ɗin sai ai sulhu a tsakani a shirya. Domin kuwa, ƴar uwa ko kin kai ƙara gidanku haƙurin dai shi za a baki.

The moment aka ce an ɗaura miki aure to ɗau ɗamarar fuskantar jarrabawar rayuwa. Ta yiwu tunda kika taso a gidanku baki taɓa neman wani abu kin rasa ba. Duk wani gata an miki,sai gashi yau da kanki kin kawo wanda kike so aka aura miki shi. To fa shi ba lallai yaci gaba da faranta miki son ranki ba.

Kamar yadda normal rayuwa take cike da abubuwan mamaki, to haka rayuwar aure itama take. Mu yawaita duba rayuwar na ƙasa damu, misali, wani shi bai ma san iyayensa, wani ba tare dasu yake rayuwa ba, wani da ɗaya daga cikinsu Allah Ya ƙaddara masa rayuwa to amman duk da haka ya rayu cikin ƙoshin lafiya kuma Allah Ya ɗaukake shi.

Matuƙar kayi imani da Allah,to faɗin Allah ne sai Ya jarrabe ka don Ya gwada imaninka. Kowa da ka gani yana yawo a doron ƙasa akwai jarrabawar rayuwa da ta zame masa ƙarfen ƙafa, haƙurin mutum da dogaronsa ga Allah shi yake sa masa nutsuwa a cikin zuciya.

Ko masu kuɗi, idan suna baka labarin irin gwagwarmayar da suka sha kafin sukai wannan matsayin sai ka iya zubar musu da ƙwalla. Sannan kuma duk yawan dukiyar mutum sai kaga wata tawaya a tare dashi wadda kudi bazai warware masa ita ba, misali, rashin lafiya, ko mutuwar wani nasa wanda zaiso ace yana raye suji daɗin dukiyar tare.

Aure bautar UbangijiWhere stories live. Discover now