page 19-20

118 6 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

☘☘ ☘☘ ☘☘

*AMATULLAH*
_baiwar Allah..._

☘☘ ☘☘ ☘☘☘

©®
*REAL SHAXEE🍒*

*GMAIL*
shaxeezeenatdeen@gmail.com

zeenatdeens@gmail.com

*wattpad*
*@zeenatdeenshaxee*

*facebook*
*zeenat deen shaxee*




*PAGE 19-20*
______________
kai tsaye gun dasukace zasu hadu sukaje suna zuwa sukuma 'yansanda,sunfama bincikesu sunbar gun zama sukayi kawai,suna ta kallonkowa sun rasa,wazasu,tambaya kawai,ganin wani ma'aikacin gun sukayi,yazo yakawo musu shayi sannan ya kamo hannun Sadiq kamar gaisawa zasuyi ya danka masa takaddu guda biyu sannan yace." Ina fatan kana lafiya abokina inkaje gida,kakirani da sabuwar nomber ka kai kullun asake nomber uwa mace." murmushi kawai sukayi Abdullah yayi huff yace." Kaidai rabu dashi nima inata yimasa fadan haka yanzuma sauri muku muje gun wata sabuwar,budurwar dayayi nace sai munbiyo mun kora shayi." " Ahh hakan yayi bara inje insallami mutane." sudai suna cike da mamaki suka dan sha shayi sannan suka biya kudin sukabar gun kai tsaye gida suka nufa suka gayawa anty su komai da komai sannan suka nuna mata takaddar.

Takaddar guda biyuce daya babbab dayar kuma karama tana dauke da nomber waya guda biyu ansa inkagama karanta ta kaddar ka kirani dan kaji karin maganar babbar suka war ware inda Abdullayi yafara karanta abunda aka rubuta afili.

_Salamu alaikun narubuta wannan wasikarne domun nasan cewa ba lallai bane abarni muhadu daku domun gudin gaskiya ta bayyana dan haka zanbawa mai gun shayinnan yabaku ita to dafarko dai zancan ku daukaka kara zuwa kotu bazai taba yuhuba domun kuna kokarin yin hakan zai sa adauketa daga nan gidan yarin zuwa inda bazaku taba ganintaba koku ji labarinta domun wani lauya yasoyin haka amma yasa aka koreshi aka soke masa ta kadda yadda bazai iya kuma yin wani aikinba ya kashe masa iyaye da yan uwa dan haka ga adres dinsanan ku tuntubeshi domun yakara muku haske awannan lamari sannan ku gaggauta barin garinnan agobe kuma anty ku ta ajiye aikinta amma kafunnan ku fara zuwa gun wannan lauyan ayau dinnan bissalam..._

Dukansu ba karamun tashin hankali suka shigaba." Waini Abdullah mai yake shirin faruwane wai mai yarinyar nan ta aikata ne ni nafara shiga rudu gaskiya." dafa kansa anty tayi." Dama ni nasan abunnan zai faru domun al amarinta babba ne sosai yanzu kutashi mutafi hadda ni dan inaso inji komai." futowa sukayi suka hau mota suna duba adres din har Allah yakawosu gidan wani gidane madai dai ci fakin sukayi sannan suka kwankwasa gidan zuwa can aka bude wani matashine wanda,bazai huce 38yr ba kana ganinsa kasan yana cikin wahalar rayuwa dakuma babu kallinsu ya tsaya yanayi sannan yace kushugo daga ciki.

Shiga,sukayi har falon wanda kana gani kasan bata samun isheshshen gyara zama sukayi suka fuskanceshi suka gaisa.

Anty Mariya ce tayi masa bayani tundaga farko harzuwa yanzu fashewa yayi da kuka Sadiq ya rungumeshi yana rarrashinsa har suka samu yayi shiru ahankali yafara cewa.

" _Dafarko dai a AMEENAT HOSPITAL nafara ganin Amatulla naje duba abokina naganta tana kuka tana rokon likita akan yaduba iyayenta batada kudi amma tace zata biyashi daga baya nikuma nahucesu ina tausaya mata naje nayi dubiyata na futo kuma bangantaba nashige abuna bayan sati biyu kuma naji wai ance Alhaji Hashimu shine mahaifinta wai takashe maza uku a hotel abun ya girgizani amma dana sameta saitaki gayamun komai danhaka ban yaddaba naje Hotel din nayi bunkice inda nagano wasu hujjoji masu karfi dan haka na daukaka kara saura kwana hudu mushiga kotu Alhj Hashimu yazo dashi dawasu yaransa da daddare suka kashemun kanwa kanina ummata dama babanmu yadade da mutuwa sanban yajamun honin akan Amatulla indai nakuma shiga lamarinta zaikasheni yasa aka batamun takaddu yanzu haka da kyar nake samun abunda zanci kunji abunda yafaru dani..._"

Dukansu shiru sukayi kowa yana kallon kowa sai zuwa can Abdullayi yace." To aganinka yanzu yazamuyi."

" Gaskiya zan shiga wannan tafiyar amma da farko saimun fara zuwa gidan yarin munyi hira da ita kaf muntambayi komai yadda baxamu kuma komawaba amma tahanyar yin videos dinta sannan mu dauki hujjojin dana samu na hotel din dan bama bukatar komawa ayanzu saimuyi video din wannan wanda yace kakirashi a takaice dai muhada duk hujjojin mu a video in mungama hadawa saimu fara sakinsu tako wane media yan jariduma muturamusu ta hanyar dabazasu gane muba yadda za arasa wanda yake wannan aiki kullun musaki sabon video ko pic din takaddun hujjojin mu to daganan duniya zataso sanin gaskiyar lamari kunga magana zataje gaba har agurfanan dasu akotu mukuma aranar,saimu dira akotun mubada hujjojin mu tahanyar duna video din bayanin Amatullah kuma itama tayi magana shikenan mungama." tafi suka fara yimasa suna murmushi." Ko sunanka ma baka gaya manaba munata uban surutu kuma ina fatan zaka zama 'kanin kamar su abdullah tunda baka da itaye yanzu." murmushi yayi har da kwallah ya taso,yazo gaban Anty ya tsugunna." Nagode da wannan karramawar,taki kuma nayi farin cikin hakan dama sai garari nake agari banda masu kula dani yau nasamu yayye da uwa danni uwa,zan daukeki sinana Ibrahim."


🤕🤕😭YAU BANDA LAFIYA SOSAI KUTAYANI DA ADDU'A

AMATULLAHIWhere stories live. Discover now